(Hikima) Batacciyar Kayan Mumini / 76 Samun hikima abu ne mai matukar muhimmanci ga mai neman isa ga kamala a rayuwa da mai kwadayin samun yardar Allah Azza Wa Jalla, abin da aka samu na nassosi dangane da hikima sun ambace ta a matsayin abu mai falala da sharafi kamar yadda aya ta siffanta ta a matsayin alheri mai yawa, {Kuma wanda aka ba shi hikima to lallai ne an ba shi alheri mai yawa} (Suratul Bakara aya ta 269), a ...
Girman Kan Mai Dukiya / 64 Qur’ani mai girma ya yi ishara ga wanda yake dagawa da ji-ji da kai saboda ganin shi mai dukiya ne a kan cewa to ya sani fa lallai yana cikin bakin ciki da asara ne {A’aha! Lallai ne mutum hakika yana girman kai. Domin ya ga kansa cikin wadata} (Suratul Alak, aya ta 6-7). Saboda shi wannan ciwon na ruhi ya sabawa fidirar da aka halicci mutum a kanta kamar yadda ya sabawa abin da ...
Farin Ciki Na Hakika / 57 Mutum yakan yi farin ciki idan ya samu dukiya, mukami da…. Sai dai dukkan wadannan masu gushewa ne, jin dadinsu ma na dan lokaci ne, ga shi kuma ba su da wata damar faranta ran mutum, amma sa’ada da farin ciki na hakika su ne mutum ya sarrafa wadannan ni’imomin a wajen neman isa ga hadafi na hakika wato neman yardar Allah, ta hanyar jajircewa wajen yin da’a a gare shi, domin wannan ne abin ...
Wajabcin Tsamar Da Iyali / 49 Qur’ani ya yi ishara a kan a ba da kulawa ta musamman ga iyalai a cikin ayoyi masu yawa: {Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kare iyalanku da kawukanku wata wuta wacce makamashinta mutane ne da duwatsu} (Suratul Tahrim, aya ta 6). Ayar tana koyar da darasi kan wani nauyi da ya hau kan mutum na jagoranci a cikin iyalai da al’ummar da ke kewaye da shi, kari a kan haka akwai hadisin da ...
Ubannin wannan al’ummar / 41 Ayoyin Qur’ani mai girma da suke magana a kan wajabcin yin biyayya ga iyaye da haramcin saba masu suna da yawa sosan gaske: {Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ka bauta wa kowa face shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata masu} (Suratul Isra’i, aya ta 23). Daga cikin muhimman misdakan da ayar nan mai girma take nuni a kansu akwai hadisin da aka samo daga Amirul Muminin (as): “Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana fadin ...
