Fikihu Da Fakihi A Isdilahin Qur'ani
Fikihu Da Fakihi A Isdilahin Qur'ani
Ba da jimawa ba mun bijiro da ma’anar jahiliyya a isdilahin Qur'ani, siffofi da halayen al'ummar ta jahiliyya da kuma canji na tsarin Allah wanda Qur'ani ya zo da shi, da sauransu a matsayin misali na al'umma.
Yanzu kuma zan gabatar da ma’anar da Qur'ani ya baiwa wannan lafazi na Hauza wato (Al-Fikhu) a matsayin wani misalin daban. Kalmar fikhu wacce ake kai komo a tsakankaninmu da ma’anar cewa tana nufin: Ilimin sanin hukunce-hukunce na shari'a, duk da cewa a isdilahin Qur'ani tana nufin: Sanin Allah Tabaraka wa Ta'ala kuma babu wata mulazama a tsakaninsu, sai dai kawai alakar da ke tsakaninsu ita ce wacce ta hada su ta wata fuska (umum min wajh).
Kamar yadda ya zo a wannan ayar mai girma: “Saboda haka don mene ne wata jama’a daga kowane bangare daga gare su ba za su fita ba zuwa neman ilimi domin su samu fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu sun ji tsoro” Tauba: 122. Mu kuma mun sani cewa tsoro da takawa ba su tsirowa ta hanyar sanin hukunce-hukunce, a’a shi tsoro tushensa daga ruhi, rai da hankali ne. to bayan samuwar takawa da ma’arifa a cikin zuciya to sai wadannan su tunkuda mutum zuwa ga neman ilimi na hukunce-hukuncen shari'a da aiwatar da su, kuma kai da kanka za ka iya jarraba haka karanta littafan fikihu kuma ka yi nutsu cikinsu tun daga na farkonsu har zua na karshensu, shin za ka samu cewa sun kara wa zuciyarka wani abu ko sun kara mata takawa da tsoro? To kuma fakihai nawa muka gani da wannan ma’anar ta isdilahi amma kuma mai tsananin kwadayin duniya ne mai nisa dukkanin nisa ga barin Allah Tabaraka wa Ta'ala.
Qur'ani ma da kansa yana ba mu labarin misalin irin wannan fakihin: “Ka karanta a kansu labarin wanda muka kawo masa ayoyinmu, sai ya salube daga gare su, sai shaidan ya bishi, sai ya zama cikin halakakku. Kuma da mun so, da mun daukaka shi da su to amma shi ya nemi dawwama a cikin kasa, kuma yabi son zuciyarsa, to misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka yi dauki a kansa ya yi lallage, ko kuwa ka barshi sai ya yi lallage, wannan ne misalin mutane da suka karyata game da ayoyinmu, ba su wannan kissar watakila su yi tunani” A’araf: 175-176.
Daga cikin shaidu da suke nuni a kan cewa fikihu na nufin sanin Allah Ta'ala sanya mahallinsa a zuciya wanda ya zo a aya mai tsarki kuma lallai shi ne mahallin hakinanin sanin Allah Ta'ala, yayin da hukunce-hukuncen shari'a mahallinsu hankali ne, Allah Ta'ala ya ce: “Sun yarda da su kasance tare da mata masu zama a (cikin gidaje), kuma aka rufe a kan zukatansu, saboda haka su ba su fahimta (ba su tafakkuhi)” Tauba: 87, a wani wajen kuma Allah ya ce: “Suna da zukata, amma ba su fahimta (tafakkuhi) da su)” A’araf: 179.
Shi ya sa ayar ta sanya wannan fikihun ai ainahin sanin Allah Ta’ala na gasken-gaske, sanin mafara da sanin makoma a matsayin ribanyar karfi gomomin ribanya, Allah Ta'ala ya ce: “Ya kai Annabi! Ka kwadaitar da muminai a kan yaki, idan mutum ashirin masu hakuri sun kasance daga gareku, za su rinjayi dari biyu, kuma idan dari suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dubu daga wadanda suka kafirta domin su mutane ne da ba su fahimta” Anfal: 65.
Kuma hadisi mai girma yana karfafar wannan ma’anar daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Shin in ba ku labari game da fakihi na hakika? Shi ne wanda ba ya katange mutane daga rahamar Ubangiji, ba ya cewa na amintar da ku daga azabar Allah, ba ya sa su fitar da tsammani daga jin kan Allah, ba ya rangwantawa idan ya ga ana sabon Allah, ba ya barin Qur'ani ya karkatar da kwadayinsa ga waninsa. Ku saurara! Babu alheri a cikin ilimin da babu fahimta a cikinsa, babu alheri a cikin karatun da babu tadabburi a cikinsa, babu alheri a cikin ibadar da babu tafakkuhi ko fahimta a cikinta”[1] wannan ya zo a littafin Wasa’ilimi. Amma hadisin yana da karashe wanda ya zo a wani littafin daban[2] kamar haka: “Don haka lallai idan ranar kiyama ta tsaya mai kira zai yi kira: Yak u mutane! Lallai mafi kusancinku mazauni a wurin Allah Ta'ala shi ne wanda ya fi ku tsananin tsoron saba masa, kuma mafi soyuwarku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku kyautata aiki, kuma mafi girmanku a wurin samun rabo a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku kwadayin abin da ke wjn Allah. Sannan sai Allah Azza wa Jalla ya ce: A yau b azan hada maku kasakanci duniya da na lahira ba, sannan sai zo masu da kujeru sannan a umarce su da zama kansu, sannan sai Allah ya fuskance su yana kuma mai yarda da su bayan ya kyautata masu ladarsu”.
Sai ka yi ta ganin siffar fakihi tana daduwa duk lokacin da ya kara kusanci ga Allah Tabaraka wa Ta'ala, ya zo a hadisi daga Amirul Muminina (as) ya ce: “Fakihai da masu hikima sun kasance idan sashensu ya rubuta wa sashe suna rubutu guda uku ne babu na hudu a cikinsu: Wanda ya zama lahira ita ce hankoronsa Allah zai wadatar da shi daga duniya, kuma wanda ya gyara sirrinsa (ya ji tsoron Allah a asirce) Allah zai gyara filinsa (bayyanarsa), kuma wanda ya gyara tsakaninsa da tsakanin Allah Azza wa Jalla Allah zai gyara tsakanisa da mutane”[3].
Kuma a cikin wani hadisin daga baban Hasan (as): “Daga alamomin fikhu akwai hakuri, ilimi da kamewa, domin lallai kamewa kofa ce daga kofofin hikima, kuma kamewa tana jawo kauna kuma dalili ce ta isa ga dukkan alkairai”[4].
Zai yiwu mu amfana da wannan ma’anar ta hanyar hada wadannan hadisan guda biyu, kuma ya zo a Al-Khisal daga Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: “Mutane iri biyu na al'ummata idan suka gyaru to hakika al'ummata ta gyaru, kuma idan suka lalace to hakika al'ummata ta lalace; su ne malamai fakihai da sarakuna”[5], amma a cikin Wasa’ilimi daga Ma’ali a maimakon malamai, makaranta aka kawo, amma idan muka hade su da hadisin da zai zo game da sifar makaranta za mu isa ga ma’ana da aka ambata.
To saboda haka tsakanin ma’anar fakihi a isdilahin Qur'ani da fakihi a ma’anar Hauza alakar da ta hada su ta wata fuska ce (wato umum min wajh) inda za ka iya samun fakihi da ma’anar isdilahin Qur'ani amma bai zama haka ba a ma’anar Hauza, domin kuwa akwai waliyyan Allah, masana kuma arifai da yawa masu karamomi sanannu amma ba su samu wannan daraja ta yin ilimin Hauza ba, kuma zai iya yiwuwa a samu akasin haka ta inda za ka samu wani mutumin ya cika kansa da nazariyoyi da fikirori na ilimin usul da akaliyya da mas’alolin fikihu ta yadda z aka same shi ya cika ya batse hatta a cikin tsefaffun mas’aloli sai dai zuciyarsa ba ta tarbiyyantu da ambaton Allah Ta'ala ba, da za ka tambaye shi dangane da ‘yar karamar mas’alar da ta shafi tsarkake rai da suluki na gari zuwa ga Allah Tabaraka wa Ta'ala da tsarkake badini da zuciya sai ya yi hololo ya zura maka idanu babu amsa, to irin wannan ba fakihi ba ne da isdilahin Qur'ani. Wanda ya samu kamala shi ne wanda ya hada wadannan ma’anonin guda biyu kamar yadda yake ga malamanmu masu tsarki wadanda suka isa wani makami madaukaki a fikihu da usul suka kuma yi nutsu cikin irfani wadanda su ne abin nufi a cikin wannan hadisin madaukaki: “Fakihai su amintattu ne ga Annabawa”[6], kuma da irin wannan ganin na Qur'ani ne ya wajaba a kanmu mu dinga fahimtar hadisai sharifai don gudun kada mu yi asarar sanin madaukakan ma’anoninsu.
[1] Biharul Anwar: 2/49, babin: Siffofin malamai da rarrabe-rarrabensu, hadisi na 8.
[2] Madinatul Balaga: Shafi na 98, daga littafin Ja’afariyyat.
[3] Al-Khisal: shafi na 129, babin uku.
[4] Al-Ikhtisas: 232.
[5] An ambaci masdarinsa a farkon littafin.
[6] Biharul Anwar: 2/36, hadisi 38.