SHAFIN FARKO | | TAMBAYOYI
TAMBAYOYI

Raba labarai

Wajabcin Bin Waliyyul Fakihi

Shin wai bin waliyyul fakihi wajibi ne? A nan fa ina nufin biyayya ta siyasa ce.

 

Da Sunansa Madaukaki

Ku bibiyi dukkan umarnoni da wayarwar kan na maraji’anku a cikin abubuwan da suke faruwa na daga mas’alolin fikihu ko matsaya ta siyasa ko abubuwa masu aukuwa na zamantakewar al’umma kamar yadda Imam Mahdi (as) ya yi wasici a jawabinsa madaukaki; inda yake cewa: “Amma dangane da abubuwa masu aukuwa to ku koma zuwa ga masu ruwaito hadisanmu domin su hujjojina ne a kanku, ni kuma hujjar Allah ne a kansu”.

Raba labarai

Makomar Kananan Yaran Da Suka Mutu

Mece ce makomar yaran da suka mutu a can cikin mahaifiyarsu da wadanda ba su balaga ba kuma ba su aikata zunubi ba? Mene ne zai faru a gare su a ranar kiyama? Shin za a mayar da su mala’iku ne a aljanna bayan sun mutu kamar yadda koda yaushe muke jin ana fada?

 

Da Sunansa Madaukaki

Ruwaya ta nuna cewa za su dinga tashi a sararin saman aljanna kai tsaye amma ba za su shiga ba har sai bayan sun ceci iyayensu masu hakuri da imani da hukuncin Allah da kudurarsa.

Raba labarai

Karanta Qur'ani Da Rana A Watan Ramadan

A cikin fatawar da ta gabata kun ce ina da damar in yi takalidanci da sayyid shahidul Sani amma da sharadin komawa zuwa gare ku a cikin mas’alolin da ake da sabani a cikinsu, to daga cikinsu akwai mas’alar karatun Qur'ani da addu’a ba tare da an kiyaye dukkan ka’idodi ba yayin da ake azumi, to mene ne ra’ayinku a kan wannan mas’alar?

 

Da Sunansa Madaukaki

Ya jajirce iyakar iyawarsa domin ganin ya samu ingantacciyar kira’a, ba a neman fiye da haka daga gare shi; kuma ya sani kowane abu yana da dausayi, kuma dausayin Qur'ani shi ne watan Ramadana, kuma na riga na kawo bayanai a rarrabe game da wannan mas’alar a cikin littafin (Fiqhul Khilaf).

Raba labarai

Likitan Hakori

Wani mutum ya je ganin likitan hakori domin a yi masa aikin ciwon hakorin da yake fama da shi, to sai likitan ya umarce shi da barin cin abinci sai dai abubuwan sha kawai, to sai hakan ya jawo masa raunin jiki da gajiyawa har ba ya iya yin azumi, to shin zai iya ajiye azumin?

 

Da Sunansa Madaukaki

Idan ya ji tsoron cewa zai iya cutuwa saboda azumin; ya halasta ya ajiye shi daga baya sai ya rama.

                                                                                                             

 

Raba labarai

Azumin Ranar Shakku

39- Yaya za mu yi azumin ranar shakku wanda ba mu sani ba shin watan Sha’aban ya cika ne wato ya cika kwanakinsa talatin ne ko kuwa ranar farko ce ga watan Ramadan, musamman idan ya zama ba mu samu tabbacin tsayuwar wata ba?

 Da Sunansa Madaukaki

Yin azumin ranar shakka da niyyar cewa azumin Ramadan ne batacce ne, koda taraddudi a niyya to yana bata azumin, misali wanda ya ce zan dauki azumi idan ya zama watan Sha’aban ne to ina azumin mustahabbi, idan kuma ya zama watan Ramadan ne to na azumci wajibi; wannan ba ya inganta, kawai abin da za ka iya yi shi ne ka azumce shi da niyyar sauke nauyin da yake kanka (ma fil zimma) to wannan zai wadatar ga Ramadan idan ya bayyana cewa watan ne.

Raba labarai

Azumin Watan Ramadan Da Zana Jarabawar Aji Shida Ta Duk Shekara-Shekara

Babban malami marji’in addini shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya ja kwananku)

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu

Mu wasu gungu ne na dalibai maza da mata ‘yan aji shida, sai ma’aikatar ilimi a ranar 6/4/2015 ta fitar da sanarwa cewa ta tsara cewa za a fara gudanar da jarabawa a ranar ashirin da bakwai ga watan Yuni, kamar yadda kuma watan Ramadan zai kama a tsakanin 15 ga watan 6 zuwa 18 ga watan 7, alhalin ita wannan shekarar ita ce ginshikin gina rayuwarmu ta yadda daga nan ne za mu fara gina harsashin rayuwarmu da makomarta, a gafe guda kuma ga azumi wanda yinsa zai iya cutar da wasunmu ya hana su karatu musamman idan an kamala daya daga cikin jarabawoyin ta yadda zai zama lokaci ne na a dan huta saboda an gaji, sannan kuma sai a yunkura a koma fagen fama a kama wani karatun domin shiryawa jarabawar gaba, ga shi kuma watan azumin yana fadowa a lokacin bazara cikin tsananin zafin rana, haka nan kuma jarabawar ana yin ta ne a cikin jami’oi. To shin zai halasta a gare mu mu sha azumi na wannan shekarar a rakakun da muke cikin matsi wato ranakun jarabawar? To idan kuma yin hakan ba ya halasta, amma sai muka sha azumin bisa ganganci to mene ne ya wajaba a kanmu, shin biya za mu yi ko ramuwa?

Muna fatan ayatullah (shaikh Yakubi) zai yi la'akari da halin da muke ciki, alhalin bangaren ma’aikata ilimi ya shiga hakkinmu, ya matsar da lokacin aiki zuwa wata guda gaba, kuma ya goge jarabawar da ake yi ta tsakiyar shekara wacce ta kasance mai muhimmanci ga karatun da muka yi na fasalin farko, ga kuma halin rashin tsaro da ake fama da shi a cikin kasa.

 

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu

Wanda ya kasance yana da iko a kan yin azumi tare da tsara wa kansa yadda zai gudanar da karatunsa a kan wannan asasi ta yadda babu abin da zai cutar da karatun nasa da kuma rayuwarsa a nan gaba, wato zai iya ya kashe dare yana mudala’a da wani bangare na yini, to wajibi ne a gare shi ya yi hakan, kuma wannan wata dama ce mai kunshe da nasara da yawa sun jarabata.

Wanda kuma yake son ya sha azumin domin ya fi samun damar shiryawa sosai ya yi karatunsa cikin nishadi, to akwai hanya ta shari’a domin warware wannan matsalar, idan dai yana da iko to kullum da safe sai ya fita a mota ya yi tafiyar da za ta kai tsawon kilomita 22, to sai ya ci wani abin ci ko abin sha bayan ya kai haddin tarakkhus, sannan sai ya dawo gida cikin danginsa alhali yana a matsayin wanda ba ya azumi, kuma zai yiwu a samu jama’a da yawa su dauki hayar mota domin yin hakan koda kuwa a ranar da ake zana jarabawar ne ko kuma a ranakun aiki ta yadda suke daukar hayar mota ta kai su ta dawo da su.

Amma shan azumi bisa ganganci ba tare da wani uzuri ba, to kwata-kwata ba ya halasta, amma idan ya yi zaton yana da kudurar da zai iya yin azumin, sai ya dauka, amma daga baya sai jikinsa ya gaza har ta kai ga dole sai ya karya azumin ko kuma ya fada cikin tsanani wanda ba a yi tsammanin faruwarsa ba kuma bai samu damar yin tafiya ba, to yana halasta gare shi ya karya azumin ya ci ko ya sha ko ya sha magani daidai gwargwadon bukata domin kawar da lalurar da ta same shi, amma ba shi da ikon yalwatawa fiye da haka, daga baya kuma sai ya rama abin da ya kubuce masa; Allah shi ne mai taimako.

 

Muhammad Yakubi

18 Jimada Sani 1436 AH.

 

 

Raba labarai

Hukuncin Tsarkakar Kifayen Da Ake Shigowa Da Su Daga Kasashen Da Ba Na Musulumi Ba

A kan samu nau’ukan kifaye daskararru (a kankara) a kasuwanni wadada ake shigowa da su daga kasashen kudancin gabacin Asiya kuma an san cewa wadannan kasashe ne na kafirai, to mene ne hukuncin saye da sayarwa da kuma cin irin wadannan kifayen. Da fatan Allah ya datar da ku a cikin yin hidima ga addini…

Da Sunansa Madaukaki

Kasantuwar an shigo da su daga kasashen kafirai ba shi ne muhimmi ba, abu mai muhimmanci shi ne su kasance suna da bawo (karsashin fata), kuma ya zama lokacin da aka fito da su daga ruwa suna rayayyunsu ba matattu ba, shi kuma sharadi na biyu yana tabbata ne a mafi rinjaye don haka sai a tabbatar an samu tabbaci a kan sharadi na farko (wato batun bawon nan a fatar kifin).

Raba labarai

Hukuncin Maziyyi A Yayin Wasanni (Tsakanin Miji Da Mata)

Mene ne hukuncin ruwan nan wanda yake zubo wa namiji a yayin wasannin miji da mata tare da cewa an san abu ne ruwa-ruwa, to idan ya taba tufafi shin yana najasantar da su kuma shin ko alwala tana baci da zubowarsa?

Da Sunansa Madaukaki

Shi wannan ruwa-ruwan (maziyyi) tsarkakakke ne kuma ba ya karya alwala.

Raba labarai

Hukuncin Man Shafawa (Cream) Wanda Ake Shafawa a Fuska Domin Ta Yi Laushi

Bisa la'akari da yanayi na sanyi a lokacin hunturu, mutane da dama suna shafa mai (basilin) na fuska suna dambara shi a koda yaushe. To yanzu idan mutum ya zo yin alwala alhali kuma ya san cewa ya shafa man kafin nan da awa biyu ko fiye da haka ko kasa da haka, shin zai iya yin alwala a haka ko dole sai ya wanke man gabaki dayansa kafin ya yi alwalar?

Da Sunansa Madaukaki

Idan dai abin da ya yi saura kawai wani dan maiko ne wanda ba zai hana ratsawar ruwa cikin fata ba, to babu laifi gare shi, amma idan man ya dankare a kan fatar ne to dole a gusar da shi.   

Raba labarai

Da Sunansa Madaukaki

Mene ne Hukuncin Tattaunawa (Chatting) Ta Internet a Tsakanin Jinsi Biyu

 

Babban malami marji’in addini shaikh Muhammad Yaqubi (Allah ya ja kwanansa)

Mene ne hukuncin wanda yake magana da wata budurwa ta hanyar wayar hannu ko masinja (messenger) da nufin cewa yana son ya shiryar da ita ko ya tattauna wadansu lamurra na yau da kullum masu amfani da ita, tare da ikirarin jin ina da hujja cewa ai ita kamar ‘yar uwarta nake kallonta, a saboda haka ina da hakkin in ji muryarta in kuma yi magana da ita a duk lokacin da na bukata, tare kuma da fakewa a kan dalilin wai ai wannan mu’amalar tamu ba za ta haifar mana da aukuwar wata sha’awa ko fadawa cikin wata fitina ba…..

Ka yi mana fatawa ya shehinmu da fatan Allah ya saka maka da alheri.

 

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu

Irin wannan alakar ba abin yabo ba ce, kuma a mafi yawan lokuta tana kai wa ga fadawa cikin haramun, a sanadin shakuwa ta zuci wacce take aukuwa, kuma yau da gobe ta shaidi irin haka da yawa.

Kuma ba lallai ba ne a cimma hadafi – cewa zai yiwu a shiryatar da ita din nan kamar yadda shi yake tsammani – alhalin a lokaci guda za a iya cimma wannan hadafin ta hanyar jinsinta, misali tunda akwai sashen (site) din Jami’atul Zahra (as) da ire-irensa ta yadda za a iya hada matar da wadannan. Kuma lallai ina kara jan hankali a kan cewa a guji kaidin shaidan domin zai iya faro maku ta hanya mai kyau amma sannu a hankali sai ya fara karkatar da ku har karkacewar ta tsananta; (Allah ya ce): “Kuma kada ku bi hanyoyin shaidan” (suratul Bakara: 168).  

Muhammad Yaqubi

21/2/1433 AH.

1 2 3 4 5
total: 47 | displaying: 1 - 10

OFISHIN MARJI’IN ADDINI

SHAIKH MUHAMMAD YAQUBI (ALLAH YA TSAWAITA KWANANSA) AIKO DA TAMBAYOYINKA

NAJAF MAI TSARKI