Raba labarai
Sallah Tare Da Sauran Mazhabobi
Muna zaune a gidan wani dan uwanmu dan ahlul Sunnah, sai lokacin sallah ya yi, to kasantuwar shi babu turba a wajensa shin yaya za mu yi sallar, shin zai yiwu mu wadatu da yin sujjada a kan darduma kawai?
Da Sunansa Madaukaki
Idan dai babu wani abu da zai hana samun abin da ya inganta a yi sujjada a kansa, to a nemo shi, tunda ai yin sujjada bai takaita ga turba kawai ba, za a iya yinta a kan ganyen bishiya, ko tabarmar kaba ko takardar da aka sana’anta ta daga wani yanki na amfanin gona da makamancinsu.
Raba labarai
Gurbata Mahalli
Shin gurbata mahalli haramun ne, irin wanda yake jawo lahani mai yawa kamar yadda aka sani, kamar hauhawar dumamar yanayi a cikin sararin samaniya da narkar da daskararrun dusar ƙanƙara wadanda suke haifar da mamayar garuruwa masu yawa?
Da Sunansa Madaukaki
Haramun ne a aiwatar da duk wani aiki wanda a cikinsa akwai cutarwa kai tsaye ga maslaha ta gama gari, wato dai abin nufi maslahohin mutane.
Raba labarai
Namijin Da Yake Tunanin Matar Da Ba Muharammarsa Ba
Mene ne hukuncin namijin da yake tunanin matar da ba muharammarsa ba?
Da Sunansa Madaukaki
Allah Ta’ala ba zai tuhumce shi a kan tunani kawai ba, domin kai-kawo a tsakanin tunani da surantawa ba yana a karkashin ikon mutum ba ne, amma kuma dole ne ya kiyaye zurfafawa da nutsawa cikin dogon tunanin ta yanda ba zai kai hadddin da zai aikata abubuwan da aka haramta ba, kuma dole ne ya yanke jerin ci gaban tunanin, wannan kuma lamari ne mai yiwuwa.
Raba labarai
Matasa Da Sha’awa
Ni matashi ne wanda shekaruna sun ja; amma ban samu damar yin aure ba saboda rashin kudi wadanda zan iya daukar nauyin hidindimun matar, a lokaci guda kuma ina fama da matsananciyar sha’awa. To wace nasiha za ku bayar – da fatan Allah ya saka maku da alheri – ganin cewa kusan a ko’ina abubuwan tayar da sha’awar ga su nan birjik?
Da Sunansa Madaukaki
Kada ka tayar da sha’awarka domin hakan zai jefa ka ka fada cikin aikata haramun, kuma ka nisanci gabatar da duk wani abu wanda zai kai ka ga aikata hakan, kuma ka tsare kanka ta hanyar yin aure Allah ne mataimakinsa kuma mai agaza maka. Sannan idan muka yi la’akari da wannan hadisin madaukaki mai cewa “Lallai arziki yana tare da aure da iyalai” a saboda haka lallai ni ina mai yi maka nasiha a kan cewa ka fara shirye-shiryen aure, ka tattauna da ’yan’uwanka da masu fatan alheri ga al’amarin ba za su yi kasa a gwiwa ba wajan taimakonka, da ikon Allah Madaukakin Sarki, kamar yadda muke ba da izinin sarrafa hakkokin shari’a domin aurar da matasa muminai.
Raba labarai
Matar Aure Da Hijabi
Nan ba da jimawa ba zan yi aure, shin ko yana halasta gare ni in ba matata damar zama babu hijabi a cikin gida tare da cewa ina zaune ne tare da dangina kuma a cikinsu akwai ‘yan uwana maza to amma kuma zaman nata da hijabi koda yaushe a cikin gidan akwai takura?
Da Sunansa Madaukaki
Bayar da dama ko rashin bayarwa ba a hannunka suke ba, domin hukuncin shari’a dole ne a dabbaka shi, don haka hijabi wajibi ne a kan mace, hatta ga ‘yan uwan mijinta wadanda suke zaune tare da su a cikin gida guda, kawai hakuri za ta ci gaba da yi, kai kuma sai ka yi bakin kokarinka wajen ganin ka samar maku da gidan zama na kashin kanku wanda ya dace da ita.
Raba labarai
Fita Yawon Shakatawa A Wuraren Shakatawa Na Gama Gari Da Gefen Teku
Mu muna daga cikin masu yin takalidanci da ku; muna da tambaya, shin mene ne hukuncin fita yawon shakatawa a wajen gari da kuma bakin teku domin sararawa da faranta rai?
Da Sunansa Madaukaki
Babu laifi ga wannan idan dai yana daga cikin abubuwan da a hankalce babu wata matsala game da su misali domin nishadantarwa da faranta rayuka, kuma wurin ya kasance babu wani abu na haramun a cikinsa.
Raba labarai
Auratayya Tsakanin Shi’a Da Sunnah
Mene ne ra’ayin shari’a game da al’amarin auren mutum dan Sunnah a gidan ‘yan shi’a? Shin wannan abin mai yiwuwa ne? Idan amsar eh ce, to mene ne sharuddan da za a gindaya a kan haka? Ni dai na taba jin an ce irin wannan auren haramun ne.
Da Sunansa Madaukaki
Wannan auren halastacce ne, domin musulunci shi ne sharadin ingancin aure, kuma yana hakkakuwa ga duk wanda ya furta kalmar shahada.
Raba labarai
Shan Taba Sigari Da Rana Tsaka A Watan Ramadan
Wasu daga cikin dalibai suna shan taba sigari sai suke riya cewa ai akwai fatawa daga samahatul shahidul Sani Sadar (qs) wacce take nuna cewa shanta ba ya karya azumi.
Da Sunansa Madaukaki
Mu muna hana shanta, sannan kuma ci gaba da yin takalidanci da sayyidul Shahid (qs) tafe yake da sharadin sai an dawo gare ni a mas’alolin da ake da sabani a cikinsu.
Raba labarai
Kyautar Da Wata Gaba Ta Jiki
Shin yana halasta ga mutum rayayye ya kyautar da wata gaba daga cikin gabobin jikinsa?
Da Sunansa Madaukaki
Ba ya halasta a bayar da kyautar wata gaba daga cikin gabobin jiki domin ita ba mallakin mutum ba ce, eh sai idan ya zama ta hanyar bayar da kyautar gabar za a ceto ran wani mutum ne, kuma hakan ba zai cutar da shi mai ba da kyautar cutarwa mai tsanani ba, to babu laifi.
Raba labarai
Al-a’alamiyya (Fifiko A Ilimi) Sharadi Ne Na Yin Takalidanci
Shin ko fifiko a ilimi (a’alamiyya) sharadi ne ga marji’in da ake yi wa takalidanci, da ma’anar cewa shin ko sharadi ne ga wanda muke son ya zama jagora a gare mu wato mai nuna mana hanyar shiriya a bisa wannan tafarki (bayan Ma’asumai “as”) dole sai ya zama mafi zurfin ilimi a kan waninsa a cikin tsamo hukunce-hukuncen shari’a, ko kuwa ba sharadi ne ba? To kuma mene ne dalili a duk ra’ayoyi guda biyu din nan?
Da Sunansa Madaukaki
Mu a wurinmu muna shardanta a’alamiyya ne ga marji’in takalidi a cikin mas’alolin da ake samun sabani a cikinsu – wadanda kuma a kan same su – to kuma idan gano hakan ya gagara a nan ya wadatar a koma ga wanda ake kyautata zaton shi ne mafi zurfin ilimin.