Matasa Da Sha’awa
Matasa Da Sha’awa
Ni matashi ne wanda shekaruna sun ja; amma ban samu damar yin aure ba saboda rashin kudi wadanda zan iya daukar nauyin hidindimun matar, a lokaci guda kuma ina fama da matsananciyar sha’awa. To wace nasiha za ku bayar – da fatan Allah ya saka maku da alheri – ganin cewa kusan a ko’ina abubuwan tayar da sha’awar ga su nan birjik?
Da Sunansa Madaukaki
Kada ka tayar da sha’awarka domin hakan zai jefa ka ka fada cikin aikata haramun, kuma ka nisanci gabatar da duk wani abu wanda zai kai ka ga aikata hakan, kuma ka tsare kanka ta hanyar yin aure Allah ne mataimakinsa kuma mai agaza maka. Sannan idan muka yi la’akari da wannan hadisin madaukaki mai cewa “Lallai arziki yana tare da aure da iyalai” a saboda haka lallai ni ina mai yi maka nasiha a kan cewa ka fara shirye-shiryen aure, ka tattauna da ’yan’uwanka da masu fatan alheri ga al’amarin ba za su yi kasa a gwiwa ba wajan taimakonka, da ikon Allah Madaukakin Sarki, kamar yadda muke ba da izinin sarrafa hakkokin shari’a domin aurar da matasa muminai.