Raba labarai
Kuskurewar Da Ake Samu Tsakanin Jinin Istihala Da Na Haila
A yaushe ne za a iya siffanta jinin da ke zo wa mata da haila? Kuma a yaushe ne yin wanka yake wajaba gare mu? Don na ji ana fadin cewa babu bukatar yin wanka idan jinin da ya zuba dan kadan ne sosai. To amma idan kuma ya zama babu makawa dole sai an yi wankan, to shin wannan jinin dan kadan (da ya zuba) za a kalle shi ne a matsayin jinin haila?
Da Sunansa Madaukaki
Hukuncin jinin haila yana tattare da wasu sharudda ne kamar haka:
1- Siffarsa ta janibin nau’in kalarsa da jizawarsa ta karkata zuwa ga baki-baki, ya zama yana fitowa da zafi-zafi da radadi tare da shi.
2- Tsawon lokacin da yake dauka bai yanke ba ba ya wuce kwanaki goma kuma karancinsa ba ya gaza kwanaki uku.
3- Mafi karancin tazara a tsakanin wannan jinin haila da waninsa kwanaki goma ne.
4- Idan mace ma’abociyar kayyadadden lokaci ce duk wata to ko yaushe a haka zai zo mata, amma da zarar an samu canji to zai yiwu ya zama jinin istihala ne; kuma kowanne daya daga cikin biyun nan yana da hukuncinsa wanda aka yi bayani dalla-dalla a cikin littafin hukunce-hukuncen shari’a mai suna (Subulul Salami), wanda kuma za a iya samunsa a sayit (site).
Raba labarai
Bismillahir Rahmanir Rahim
Marji’in Addini Ayatullahil Uzma Shaikh Muhammad Yaqubi (Allah Ya Yalwata Albarkarsa)
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah wa Barakatuhu
Mene ne asasi da ka’idodin shari’a na yin tiyata domin yin ado da kawa? Kuma da mai da mene ne ma’aunai na shari’a a kan hakan?
Bismihi Ta’ala:
Yin tiyata domin yin ado da kawa wadanda aka sani a wannan zamanin suna da nau’uka daban-daban, to kuma gwargwadon hakan ne hukuncin shari’a zai kasance, idan domin kawo gyara ga wata tawaya a fuska ko jiki wanda kuma yake wajabta wahalhalu na zamantakewa da kuma cin fuska daga jahilai ne, to a nan (sai mu ce): (Daga cikinsu akwai) abin da ya fi zama daidai shi ne yin aiki domin kawar da wannan ciwon ko kaskantar da wulakantar.
Raba labarai
IHTIYADI NA WAJIBI
Shin marji’in addini samahatul shaikh Yaqubi yana ganin yiwuwar yin ruju’i (komawa) a ihtiyadi na wajibi ga waninsa ko a’a?
Bismihi Ta’ala
Ihtiyadi na wajibi yana da tushe guda biyu:
1- Taraddudi a cikin fatawa saboda rashin fitowar dalili balo-balo da kuma dunkulewarsa ko kuma saboda karo da aka samu cikin dalilai (na nassi) da makamantansu.
2- A samu mas’alar da a irinta ake gudanar da asalatul ihtiyad (wani bahasi ne na usulul amali).
To idan ya zama tushen ihtiyadi kashi na farko ne, to muna bayar da damar a koma ga wani marji’in daban wanda ya cika sharudda ba na biyun ba.
To kuma kasantuwar mukallafi ba ya iya tantance wuraren guda biyu, to wajibi ne a gare shi ya yi aiki da tsagwaron ihtiyadodi na wajibai gabaki dayansu, ko kuma ya koma ga shi marji’in a kan kansa domin ya tambaye shi yiwuwar komawa ga waninsa a wannan gurin ko kuma a’a (wato ba zai yiwu a koma din ba).
Raba labarai
IJTIHADI DA A’ALAMIYYA
Ta wadanne hanyoyin shari’a ne ake iya sanin ijtihadi da a’alamiyya (mafi kololuwar sani)?
Bismihi Ta’ala
Ijtihadi da a’alamiyya suna tabbata ne ga shi mutum a kan kansa ta hanyar wijdani, amma ga sauran mutane suna tabbata ne ta hanyar shaidawar ahlul khibra da kebantattu, wadannan kuwa su ne manyan masu falala da malaman hauzar ilimi mai tsarki, ba ma kamar mujtahidan cikinta, amma wasunsu basu da wani ra’ayi a cikin wannan maudhu’in kuma zancensu ba abin la’akari ba ne komai yawansu kuwa, eh, wadannan sauran sun samu su nakalto shaidar da ahlul khibra suka bayar ga makusantansu da abokansu, wannan kuma shi ne abin da sirar ukala (siratul ukala’i) ta doru a kai a cikin sauran ilimomi da fannoni, fikihu kuma yana daga cikinsu. Kamar dai yadda iyalai suke biyayya ga mai gida ba domin shi yana daga cikin ahlul khibra ba a’a sai dai don kasancewarsa amintacce a wajensu, to gwargwadon haka zancensa yakan kasance dalili da hujja a wajensu ba wani abu fiye da haka ba, irin haka ne zancen wani malami masani na wani birni yake yaduwa ga mutanen wannan birnin da makamantansu.
Kuma an shardanta ga ahlul khibra kari a kan falalarsu ta ilimi tsananin kiyayewa da kulawa da tsantseni da nisantar biyewa son rai da maslaha ta kashin kai wajen bayar da shaidar.
Raba labarai
Cin Naman Kaza A Kasashen Da Ba Na Musulunci Ba
Mene ne hukuncin cin naman kaza a kasashen da ba na musulunci ba, tare da cewa ni ina zuwa cin naman ne wajen balaraben Iraki kuma yakan ce ai kazar daga Turkiya ake kawota kuma ana yi mata yankan musulunci ne a hannun Turkawa, shin zan iya gamsuwa da halascin naman wannan kazar ko a’a?
Bismihi Ta’ala
Idan dai ka samu natsuwa da zancensa to babu wata damuwa a kan haka.
Raba labarai
Bismillahir Rahmanir Rahim
Fatawa Game Da Takalidancin Maraji’an Da Suka Gabata (Allah Ya Tsarkake Rayukansu) Da Yin Aiki Da Ihtiyadi Na Wajibi
Marji’in Addini Ayatullahil Uzma Shaikh Muhammad Yaqubi (Allah Ya Tsawaita Kwanansa)
Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu
Ka yi mana fatawa; da fatan Allah ya cika maka ladarka:
1- Shin ko kuna ganin halascin wanzuwa da ci gaba da yin takalidi ga babban malami sayyid Abul Qasim Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) da wasunsa na maraji’ai magabata (Allah ya tsarkake rayukansu)?
2- Shin ko yana yiwuwa a yi ruju’i (a koma) ga waninku a cikin mas’aloli na ihtiyadi na wajibi a cikin risala amaliyya (littafin fatawa)?
Wani gungu na masu takalidanci da samahatul sayyid Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) a birnin Bagdad.
Bsimihi Ta’ala
Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu
1- Muna bayar da dama ga wanda ya kasance mai takalidanci da wdannan manyan malaman: Sayyid Khu’i, da kuma sayyidodi guda biyu kuma shahidai Sadarain (Allah ya tsarkake rayukansu) cewa ya halasta ya ci gaba da aiki da risalolinsu masu girma (littafansu na fatawoyi), da kuma komowa zuwa gare ni a cikin mas’aloli masu bijirowa (sababbi), da kuma mas’alolin da aka san cewa akwai sassabawar fatawa a cikinsu, kuma wannan damar za ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da za mu fitar da wata sabuwar fatawar da izinin Allah Ta’ala.
2- Mu muna masu lizimtawa mukallafi da yin aiki da hukuncin ihtiyadi na wajibi wanda aka ambata a cikin risala amaliyya.
Amma idan a cikin yin hakan ya hadu da wani tsanani, sai ya bukaci samun hanya mai fadi wacce za ta ba shi damar samun rangwame a cikin lamarin, to ya tuntube mu, domin watakila ya zama lamarin yana daga cikin lamurran da muke bayar da damar komawa ga wani wanda yake cikin mafiya ilimi (a’alam) wadanda suka samar wa mabiyansu hujja da dalili da izinin Allah Ta’ala. Amma ba a kowane lamari na ihtiyadi na wajibi ba ne ake iya komawa ga wani malamin ba.
Allah ya saka maku da mafificin sakayyar da yake wa masu kyautatawa.
Muhammad Yaqubi
6 / 2 / 1433.
Raba labarai
Fatawa Game da Zubar da Ciki Idan Jaririn Yana Dauke da Wata Tawaya
Bismihi Ta’ala
Marji’in addini samahatul shaikh Muhammad Yaqubi (Allah ya tsawaita kwanansa)
Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu
Tambaya: Mene ne hukuncin shari’a dangane da wannan yanayin wanda ya yadu a tsakanin jama’a cewa bincike na zamani yana iya gano mace mai dauke da ciki na jinjiri mai tawaya a halittarsa….to shin ko yana halasta a zubar da irin wannan cikin ganin irin wahalhalu, laulayi da ma wasu nau’ukan rashin lafia da yake haifarwa mai dauke da shi… wanda kuma sakamako ya nuna cewa yaron ko bayan an haife shi mutuwa zai yi… kuma a mafi yawancin lokuta haihuwar takan zo da tsanani ko sai an kai ga yin tiyata don a ciro dan da dai sauran wahalhalu.
Sashen likitoci mata daga cikin
Mabiya masu takalidanci da shaikh Yaqubi.
Amsa:
Da Sunansa Madaukaki
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu
Abin da ka’ida take hukuntawa shi ne cewa haramun ne zubar da ciki bayan saukar kwan halitta (cikin mahaifa) kuma har ya kai ga ya zama gudan jini; to sai dai akwai togaciya wacce a irin nan yana halasta a zubar da ciki amma sai bayan an samu tabbaci da sakankancewa a kan ainahin sakamakon bincike wanda ya zama daya daga cikin wadannan:
1- Idan ya zama barin cikin zai jawo rasa rayuwar ita mai cikin.
2- Idan tawayar halittar jinjirin ta yi munin da kusan za a iya cewa wannan ai nau’in halittarsa ba ta mutane ba ce; kamar misali ya zama yanayin halittar kansa ya kai makurar kankanta, amma da tawayar za ta tsaya a kan wasu ‘yan cututtuka to ba za a zubar ba.
3- Amma idan mai dauke da tawayar ya kasance an gano tawayar ta kai matsayin cewa lallai da zarar an haife shi tabbas zai mutu ne kawai, kuma ba a samu daya daga cikin wadancan matsalolin guda biyu da suka gabata ba, to a nan a cikin halascin zubarwar akwai taraddudi, a saboda haka a nan mun bayar da damar ana iya komawa ga daya daga cikin maraji’ai wadanda ake kididdiga su cikin wadanda ake kyautata zaton suna cikin mafiya sani (a’alam), kuma Allah shi ne majibincin lamurra.
Muhammad Yaqubi
21 / Rabi’ul Auwal /
Raba labarai
Da Sunansa Madaukaki
Fatawa: Mai Jinin Haila Da Karatun Qur’ani
Tambaya: Shin ko yana halasta ga macen da take jinin haila ta karanta Qur’ani gaba-gadi ko kuma akwai wasu sharudda da aka aiyana?
Amsa: Da sunansa Madaukaki: Yana halasta ga mace mai jinin haila ta karanta abin da take so na daga Qur’ani mai girma, kuma mustahabbi ne gare ta kamar yadda yake mustahabbi ga waninta ta yi alwala domin yin karatun na Qur’anin, na’am sai dai akwai abin da aka kebance na daga surorin aza’im wadanda a cikinsu akwai sujjada ta wajibi wadannan surorin kuwa su ne: (Al-Sajdah, Fussilat, Najm, Alak) domin karanta su ba ya halasta a gare ta, sai dai idan ta ji wani daban yana tilawarsu, to ya wajaba a gare ta ta yi sujjada kamar yadda ya wajaba ga waninta.
A karkashin wannan, lallai abin da wasu matan suke yi na barin karatun Qur’ani a yayin da suke haila har a cikin watan Ramadana watan kakar Qur’ani to suna haramtawa kansu wannan falala mai girma ce.
Amma wajibi ne mai haila ta lura cewa ba ya halasta taba rubutun Mushafin (Qur’anin) saboda sharadin tsarki da aka gindaya wajen tabawar.
Raba labarai
Sauke Nauyi Na Ibadodi (Na Wajibai) Amma Ba Tare Da Kiyaye Hijabi Ba
Na kasance ina yin sallah da azumi tun ina ‘yar shekara 15, sai dai ba na sanya hijabi a tsawon wadannan shekarun, koda yake tun daga lokacin da aka haifeni (wato tun ina karama) nake kwadayin saka hijabi, saboda yadda nake matukar son a nan gaba in zama kyakkyawar abin koyi ga ‘ya’yana ta hanyar sanya hijabi, mene ne ya kamata na aikata domin karfafar imanina? A yayin da mahaifiyata dimin-da’iman idonta a kaina ba ta son ta ga na saka hijabin.
Da Sunansa Madaukaki
Lallai mujarradin wannan imanin naki cewa sanya hijabi umarni ne daga Allah, ya wadatar da ke ki kiyaye tare da lizimtar saka hijabi, domin ba ya yiwuwa a dinga ketare umarnonin Allah da hane-hanensa; Allah Ta’ala ya ce: “Wadancan iyakokin Allah ne, saboda haka kada ku ketare su”, kuma sanya hijabinki ba yana nufin kin tozarta mahaifiyarki ba ne, kuma abin kunyar da ta aikata ba ke ce kika sabbaba shi ba, a’a rashin kiyayewarta ga dokoki da iyakokin Allah Tabaraka wa Ta’ala ne suka jawo mata yin hakan.
Raba labarai
Daukar Wata Gaba Ta Mamaci Domin Wata Bukata Ta Aikin Likitanci
Shin ko yana halasta a dauki wata gabar wani mamaci (domin wata bukata ta aikin likitanci)?
Da Sunansa Madaukaki
Ba ya halasta yin hakan saboda martabar da dan’adam yake da ita a raye yake ko a mace da kuma haramcin yin gunduwa-gunduwa da mamaci (daddatsa shi gaba-gaba), amma idan akwai lalura ta koyon aikin likitanci ga yin hakan, to sai a yi aiki da gawar wanda ba musulmi ba.