IHTIYADI NA WAJIBI
IHTIYADI NA WAJIBI
Shin marji’in addini samahatul shaikh Yaqubi yana ganin yiwuwar yin ruju’i (komawa) a ihtiyadi na wajibi ga waninsa ko a’a?
Bismihi Ta’ala
Ihtiyadi na wajibi yana da tushe guda biyu:
1- Taraddudi a cikin fatawa saboda rashin fitowar dalili balo-balo da kuma dunkulewarsa ko kuma saboda karo da aka samu cikin dalilai (na nassi) da makamantansu.
2- A samu mas’alar da a irinta ake gudanar da asalatul ihtiyad (wani bahasi ne na usulul amali).
To idan ya zama tushen ihtiyadi kashi na farko ne, to muna bayar da damar a koma ga wani marji’in daban wanda ya cika sharudda ba na biyun ba.
To kuma kasantuwar mukallafi ba ya iya tantance wuraren guda biyu, to wajibi ne a gare shi ya yi aiki da tsagwaron ihtiyadodi na wajibai gabaki dayansu, ko kuma ya koma ga shi marji’in a kan kansa domin ya tambaye shi yiwuwar komawa ga waninsa a wannan gurin ko kuma a’a (wato ba zai yiwu a koma din ba).