Fatawa: Mai Jinin Haila Da Karatun Qur’ani
Da Sunansa Madaukaki
Fatawa: Mai Jinin Haila Da Karatun Qur’ani
Tambaya: Shin ko yana halasta ga macen da take jinin haila ta karanta Qur’ani gaba-gadi ko kuma akwai wasu sharudda da aka aiyana?
Amsa: Da sunansa Madaukaki: Yana halasta ga mace mai jinin haila ta karanta abin da take so na daga Qur’ani mai girma, kuma mustahabbi ne gare ta kamar yadda yake mustahabbi ga waninta ta yi alwala domin yin karatun na Qur’anin, na’am sai dai akwai abin da aka kebance na daga surorin aza’im wadanda a cikinsu akwai sujjada ta wajibi wadannan surorin kuwa su ne: (Al-Sajdah, Fussilat, Najm, Alak) domin karanta su ba ya halasta a gare ta, sai dai idan ta ji wani daban yana tilawarsu, to ya wajaba a gare ta ta yi sujjada kamar yadda ya wajaba ga waninta.
A karkashin wannan, lallai abin da wasu matan suke yi na barin karatun Qur’ani a yayin da suke haila har a cikin watan Ramadana watan kakar Qur’ani to suna haramtawa kansu wannan falala mai girma ce.
Amma wajibi ne mai haila ta lura cewa ba ya halasta taba rubutun Mushafin (Qur’anin) saboda sharadin tsarki da aka gindaya wajen tabawar.