Sauke Nauyi Na Ibadodi (Na Wajibai) Amma Ba Tare Da Kiyaye Hijabi Ba
Sauke Nauyi Na Ibadodi (Na Wajibai) Amma Ba Tare Da Kiyaye Hijabi Ba
Na kasance ina yin sallah da azumi tun ina ‘yar shekara 15, sai dai ba na sanya hijabi a tsawon wadannan shekarun, koda yake tun daga lokacin da aka haifeni (wato tun ina karama) nake kwadayin saka hijabi, saboda yadda nake matukar son a nan gaba in zama kyakkyawar abin koyi ga ‘ya’yana ta hanyar sanya hijabi, mene ne ya kamata na aikata domin karfafar imanina? A yayin da mahaifiyata dimin-da’iman idonta a kaina ba ta son ta ga na saka hijabin.
Da Sunansa Madaukaki
Lallai mujarradin wannan imanin naki cewa sanya hijabi umarni ne daga Allah, ya wadatar da ke ki kiyaye tare da lizimtar saka hijabi, domin ba ya yiwuwa a dinga ketare umarnonin Allah da hane-hanensa; Allah Ta’ala ya ce: “Wadancan iyakokin Allah ne, saboda haka kada ku ketare su”, kuma sanya hijabinki ba yana nufin kin tozarta mahaifiyarki ba ne, kuma abin kunyar da ta aikata ba ke ce kika sabbaba shi ba, a’a rashin kiyayewarta ga dokoki da iyakokin Allah Tabaraka wa Ta’ala ne suka jawo mata yin hakan.