Fatawa Game Da Takalidancin Maraji’an Da Suka Gabata (Allah Ya Tsarkake Rayukansu) Da Yin Aiki Da Ihtiyadi Na Wajibi

| |times read : 287
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Bismillahir Rahmanir Rahim

Fatawa Game Da Takalidancin Maraji’an Da Suka Gabata (Allah Ya Tsarkake Rayukansu) Da Yin Aiki Da Ihtiyadi Na Wajibi

Marji’in Addini Ayatullahil Uzma Shaikh Muhammad Yaqubi (Allah Ya Tsawaita Kwanansa)

Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu

Ka yi mana fatawa; da fatan Allah ya cika maka ladarka:

1- Shin ko kuna ganin halascin wanzuwa da ci gaba da yin takalidi ga babban malami sayyid Abul Qasim Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) da wasunsa na maraji’ai magabata (Allah ya tsarkake rayukansu)?

2- Shin ko yana yiwuwa a yi ruju’i (a koma) ga waninku a cikin mas’aloli na ihtiyadi na wajibi a cikin risala amaliyya (littafin fatawa)?

Wani gungu na masu takalidanci da samahatul sayyid Khu’i (Allah ya tsarkake ruhinsa) a birnin Bagdad.

 

Bsimihi Ta’ala

Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu

1- Muna bayar da dama ga wanda ya kasance mai takalidanci da wdannan manyan malaman: Sayyid Khu’i, da kuma sayyidodi guda biyu kuma shahidai Sadarain (Allah ya tsarkake rayukansu) cewa ya halasta ya ci gaba da aiki da risalolinsu masu girma (littafansu na fatawoyi), da kuma komowa zuwa gare ni a cikin mas’aloli masu bijirowa (sababbi), da kuma mas’alolin da aka san cewa akwai sassabawar fatawa a cikinsu, kuma wannan damar za ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da za mu fitar da wata sabuwar fatawar da izinin Allah Ta’ala.

2- Mu muna masu lizimtawa mukallafi da yin aiki da hukuncin ihtiyadi na wajibi wanda aka ambata a cikin risala amaliyya.

Amma idan a cikin yin hakan ya hadu da wani tsanani, sai ya bukaci samun hanya mai fadi wacce za ta ba shi damar samun rangwame a cikin lamarin, to ya tuntube mu, domin watakila ya zama lamarin yana daga cikin lamurran da muke bayar da damar komawa ga wani wanda yake cikin mafiya ilimi (a’alam) wadanda suka samar wa mabiyansu hujja da dalili da izinin Allah Ta’ala. Amma ba a kowane lamari na ihtiyadi  na wajibi ba ne ake iya komawa ga wani malamin ba.

Allah ya saka maku da mafificin sakayyar da yake wa masu kyautatawa. 

Muhammad Yaqubi

6 / 2 / 1433.