Kuskurewar Da Ake Samu Tsakanin Jinin Istihala Da Na Haila
Kuskurewar Da Ake Samu Tsakanin Jinin Istihala Da Na Haila
A yaushe ne za a iya siffanta jinin da ke zo wa mata da haila? Kuma a yaushe ne yin wanka yake wajaba gare mu? Don na ji ana fadin cewa babu bukatar yin wanka idan jinin da ya zuba dan kadan ne sosai. To amma idan kuma ya zama babu makawa dole sai an yi wankan, to shin wannan jinin dan kadan (da ya zuba) za a kalle shi ne a matsayin jinin haila?
Da Sunansa Madaukaki
Hukuncin jinin haila yana tattare da wasu sharudda ne kamar haka:
1- Siffarsa ta janibin nau’in kalarsa da jizawarsa ta karkata zuwa ga baki-baki, ya zama yana fitowa da zafi-zafi da radadi tare da shi.
2- Tsawon lokacin da yake dauka bai yanke ba ba ya wuce kwanaki goma kuma karancinsa ba ya gaza kwanaki uku.
3- Mafi karancin tazara a tsakanin wannan jinin haila da waninsa kwanaki goma ne.
4- Idan mace ma’abociyar kayyadadden lokaci ce duk wata to ko yaushe a haka zai zo mata, amma da zarar an samu canji to zai yiwu ya zama jinin istihala ne; kuma kowanne daya daga cikin biyun nan yana da hukuncinsa wanda aka yi bayani dalla-dalla a cikin littafin hukunce-hukuncen shari’a mai suna (Subulul Salami), wanda kuma za a iya samunsa a sayit (site).