Fatawa Game da Zubar da Ciki Idan Jaririn Yana Dauke da Wata Tawaya
Fatawa Game da Zubar da Ciki Idan Jaririn Yana Dauke da Wata Tawaya
Bismihi Ta’ala
Marji’in addini samahatul shaikh Muhammad Yaqubi (Allah ya tsawaita kwanansa)
Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu
Tambaya: Mene ne hukuncin shari’a dangane da wannan yanayin wanda ya yadu a tsakanin jama’a cewa bincike na zamani yana iya gano mace mai dauke da ciki na jinjiri mai tawaya a halittarsa….to shin ko yana halasta a zubar da irin wannan cikin ganin irin wahalhalu, laulayi da ma wasu nau’ukan rashin lafia da yake haifarwa mai dauke da shi… wanda kuma sakamako ya nuna cewa yaron ko bayan an haife shi mutuwa zai yi… kuma a mafi yawancin lokuta haihuwar takan zo da tsanani ko sai an kai ga yin tiyata don a ciro dan da dai sauran wahalhalu.
Sashen likitoci mata daga cikin
Mabiya masu takalidanci da shaikh Yaqubi.
Amsa:
Da Sunansa Madaukaki
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu
Abin da ka’ida take hukuntawa shi ne cewa haramun ne zubar da ciki bayan saukar kwan halitta (cikin mahaifa) kuma har ya kai ga ya zama gudan jini; to sai dai akwai togaciya wacce a irin nan yana halasta a zubar da ciki amma sai bayan an samu tabbaci da sakankancewa a kan ainahin sakamakon bincike wanda ya zama daya daga cikin wadannan:
1- Idan ya zama barin cikin zai jawo rasa rayuwar ita mai cikin.
2- Idan tawayar halittar jinjirin ta yi munin da kusan za a iya cewa wannan ai nau’in halittarsa ba ta mutane ba ce; kamar misali ya zama yanayin halittar kansa ya kai makurar kankanta, amma da tawayar za ta tsaya a kan wasu ‘yan cututtuka to ba za a zubar ba.
3- Amma idan mai dauke da tawayar ya kasance an gano tawayar ta kai matsayin cewa lallai da zarar an haife shi tabbas zai mutu ne kawai, kuma ba a samu daya daga cikin wadancan matsalolin guda biyu da suka gabata ba, to a nan a cikin halascin zubarwar akwai taraddudi, a saboda haka a nan mun bayar da damar ana iya komawa ga daya daga cikin maraji’ai wadanda ake kididdiga su cikin wadanda ake kyautata zaton suna cikin mafiya sani (a’alam), kuma Allah shi ne majibincin lamurra.
Muhammad Yaqubi
21 / Rabi’ul Auwal /