Ubannin wannan al’ummar / 41
09/07/2020 17:51:00 |
17/ZULKI’IDA/1441|times read : 918
Ubannin wannan al’ummar / 41
Ayoyin Qur’ani mai girma da suke magana a kan wajabcin yin biyayya ga iyaye da haramcin saba masu suna da yawa sosan gaske: {Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ka bauta wa kowa face shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata masu} (Suratul Isra’i, aya ta 23). Daga cikin muhimman misdakan da ayar nan mai girma take nuni a kansu akwai hadisin da aka samo daga Amirul Muminin (as): “Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana fadin cewa Ni da Ali dan Abi Dalib mu ne Ubannin (Iyayen) wannan al’umma, kuma hakkinmu a kansu ya fi hakkin mahaifansu a kansu, domin kuwa idan dai har suka yi mana da’a to za mu tsamar da su daga azabar wuta zuwa gida matabbaci, kuma za mu daukaka su daga kangin bauta zuwa ‘yanci na ‘ya’ya”.