Marji’in Addini Ayatullahi Yakubi a Yayin Ganawarsa da Kungiyar Nida’ul Aqsa Ya Ce: Babu Wani Canji Ga Zabin Musulunci a Wajen Fuskantar Makiya ta Kowace Fuska.
DA SUNANSA MADAUKAKI:
Marji’in Addini Ayatullahi Yakubi a Yayin Ganawarsa da Kungiyar Nida’ul Aqsa Ya Ce: Babu Wani Canji Ga Zabin Musulunci a Wajen Fuskantar Makiya ta Kowace Fuska.
Samahatul shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya ja kwanansa) ya gana da kungiyar Nida’ul Aqsa a ofishinsa da ke Najaf mai tsarki[1], wanda suka hada da gungun malaman addini mujahidai daga Falasdinu da Siriya da Labanon daga mazhabobin nan biyu (sunnah da shi’a), wadanda suka kudiri aniyar kafa maukibi domin hidimtawa masu tattaki zuwa Karbala domin ziyartar Imam Husaini (as), a hankoronsu na kwadaitar da muminai su ci gaba da tunawa da Kudus da kuma kiyaye wannan jigo na jahadi har sai an dawo da yankunan da aka kwace. To bayan mahalarta taron sun bayyana manufofin wannan yunƙurin kuma sun yi bayanin wahala da tsayin dakan al'ummar Falasɗinu, sai samahatul shaikh ya fara bayaninsa yana mai yi masu marhabin lale, sannan yana mai bayyana masu ni’imar da Allah ya yi wa gurin da khususiyyar da yake kunshe da ita wanda wuri ne da yake makobtaka da (haramin) Amirul Muminina (as) mutumin da ya kawar da makircin Yahudawa da kaidodinsu a yaƙe-yaƙen Musulunci dauwamamme, sannan kuma ya bayyana khususiyyar wannan lokacin na tunawa da yunkurin Imam Hussain (as) a matsayinsa na alamin jahadi da mukawama da ƙin yarda da zalunci, ga shi abin koyin masu juyi da kira zuwa ga ‘yantar da dan’adam. Bayan nan sai shaikh ya juya yana mai cewa:
Lallai Al- Aqsa a matsayinta na farkon alkibla kuma ta ukun mahallai biyu masu tsarki tana da wata kima ta musamman a zukatan Musulmai tun a farkon Musulunci, kuma lallai maraji’ai a Najaf mai tsarki tun a farkon lamarin sun muhimmantar da lamarin Falasdinu da birnin Kudus muhimmantarwa mai girma. Kuma lallai marji’in addini muslihi marigayi shaikh Muhammad Husain Al Kashiful Gida’i (qs) da kansa ya halarci taron addinin Musulunci da aka gudanar a Kudus a shekara ta (1350 AH: 1931 Miladiyya) tun a farko-farkon hijirar Yahudawa zuwa ƙasar Falasdinu bayan alkawarin Balfur a shekarar 1917 AD.
A inda samahatul shaikh ya yi ishara a kan alakar da ke tsakanin marja’iyya a Najaf mai tsarki[2] da goyon bayan da suke bayarwa ga jahadi domin fuskantar Yahudawan sahayina tun a shekara ta 1969 lokacin da aka kaddamar da aikin sadaukarwa bayan waki’ar kona masallacin Al- Aqsa, inda har babban marji’in addini na wannan lokacin sayyid Muhsin Hakim (qs) ya albarkaci wannan yunkuri, har ma ya ba da izinin a sarrafa dukiyar shari’a (khumusi) wanda mabiya suke fitarwa su ba maraji’ai domin a yi wancan aikin da su.
Kuma marji’ancin addini ya kasance koda yaushe yana kira ga a yi riko da zabin da Musulunci ya bayar don fuskantar makiya domin shi makiyi yana yin yaki ne bisa imani da yake da shi da sadaukarwa, don haka dole ne a fuskance shi ta wannan hanya ta akida, sai dai gwamnatoci masu gudanar da mulki bisa la’akari da tsare-tsaren da suka yi imani da su da kuma yanayin kai-komonsu, sun tayar da wani taken kishin kasa na Larabawa wanda kwata-kwata ba zai wadatar ko ya zama isasshen dalili na sadaukarwa ba, domin karancin kusancinsa da akidar Musulunci, a saboda haka ne suka sami damar kautar da dukkan al'ummar Musulmi daga wannan yunkurin ta hanyar yaudarar su cewa lamarin Falasdinawa bai shafe ku ba domin lamari ne na Larabawa zalla.
Kuma samahatul shaikh ya yi nuni da cewa lallai an sami sauyi da canji a shekarar 1987 miladiyya lokacin da mujahidai suka riki zabin Musulunci sannan suka kaddamar da gwagwarmayar mukawamar Musulunci, sai karfin ya karu zuwa ga wani karfi na musamman, kuma wannan ne abin da Allah ya ambata da fadinsa: “Idan mutum ashirin masu hakuri sun kasance daga gare ku za su rinjayi dari biyu, kuma idan dari suka kasance daga gare ku za su rinjayi dubu daga wadanda suka kafirta” (Anfal: aya 65), sai kuma Allah Ta'ala ya fadi dalilin hakan a karshen ayar da cewa: “Domin su mutane ne da ba su fahimta”.
Kamar yadda samahatul shaikh ya yi nuni da canjin da aka samu na juyawar karfin cikin yardar Allah Ta'ala ya zama yanzu mujahidai ne suke da shi, domin cewa a baya sun kasance suna jifar makiyansu Yahudawan sahayina da duwatsu a daidai lokacin da suke tunkarar ruwan harsasai da kirjinsu a bude, yanzu kuwa sun ci gaba ta yadda suke harba wa Yahudawan sahayina dubban makamai masu linzami a karshe-karshen nan a wata amaliyyar Saiful Kudus har sai da ta kai ga biranen Yahudawan sahayina sun jigata (sun rasa inda za su saka kawukansu).
Daga karshe, wadannan baki sun nuna matukar farin cikinsu na ganawa da samahatul shaikh, inda suka bayyana cewa lallai marji’anci a Najaf ya kasance wanda ya farfado da fatansu kuma har yau bai gushe ba yana a matsayin ginshiki na al'amarin Falasdinu kuma mai goyon bayansa da jagorantarsa.
[1] An yi wannan ganawar ce a ranar Litinin 12 ga Safar 1443 daidai da 20 / 9 / 2021.
[2] Marji’in addini samahatul shaikh yana da matsayai dangane da lamarin Falasdinawa ga wasu daga ciki:
A- Littafinsa mai suna: Nazaratun Fi Falsafatil Ahdas. Wannan wasu sakonni ne tsakanin shaikh Yakubi da malaminsa shahid Sadr (qs) a tsakiyar tamaninoni a karnin da ya gabata.
B- Mika ta’aziyyarsa ta shahadar Ahmad Yasin.
C- Zantukansa game da munasabobin ranar Kudus ta duniya.
Wadannan dukkansu an tattare su a cikin littafi mai suna: Falasdin Wal Kudus Fi Dhamiril Najaf al-Ashraf.