Tarihin Rayuwa

| |times read : 1985
Tarihin Rayuwa
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Shaikh Muhammad Bn Shaikh Musa Bn Shaikh Muhammad Ali Bn Shaikh Yaqub Bn Alhaj Ja’afar.

An haife shi a Najaf mai tsarki da asubahin ranar haihuwar Annabi (s.a.w.a) (wato 17 ga watan Rabiul Auwal) a shekara ta 1380H wacce ta yi daidai da watan September shekara ta 1960M. Ya taso a cikin gidan ilimi da addini, gidan da ya shahara wajen khidaba (wa’azi) da adabi, don kuwa da yawa daga cikin mutanen gidan sun wallafa littafan adabi da fikira da khidaba, kamar babansa shaikh Musa – mai shahararriyar mujallar nan wato Aiman – da kakansa shaikh Muhammad Ali wanda aka yi wa lakabi da (shehin masu huduba), da kakansa na bangaren mahaifiyarsa shaikh Muhammad Mahdi, da kakan babansa shaikh Yaqub wanda ya kwankwada daga makarantar irfani da halayen kwarai ta marigayi shaikh Ja’afar Shustari da marigayi shaikh Husain Koli Hamdani.

Ya yi balaguro zuwa Bagadaza tare da mahaifinsa a shekara ta 1968 AD, kasantuwar mahaifin nasa ma’abocin harkoki ne na addini da siyasa da zamantakewa wanda yake yin wadannan harkokin tare da marigayi shahid sayyid Mahdi Hakim, jikan marigayi babban marji’i sayyid Muhsin Hakim (kuddisa sirruhu) wanda ya kasance shugaba ne na addini da na al’umma a Bagadaza.

Ya yi karatun addini mai zurfi tun da sauran kuruciyarsa, a lokacin da ya kasance yana bin mahaifinsa a ko’ina yana mai halartar majalisosin darassunsa kuma yana da kaifin fahimta tare da natsuwa, sannan daga baya sai ya dinga rubuta darussan filla-filla – bayan dawowarsa – gurin mahaifiyarsa (Allah ya ji kanta da rahama), sannan kuma mahaifinsa (Allah ya ji kansa da rahama) ya kasance yana yin ishara ga kwazonsa da kaifin kwakwalwarsa a gaban malamai da manyan mutane, bai kai dan shekara goma ba ya fara karanta littafai, har ma ya rubuta wani bahasi mai fadi mai taken “Giya ita ce tushen miyagun laifuka”, alhali a lokacin ko balaga bai yi ba, to haka dai ya kasance yana tasawa yana ta kara nutsawa cikin karanta manya-manyan littafai.

A farko-farkon shekarun saba’inoni a lokacin ana cikin hutun bazara ya samu shiga wata makarantar addini ta Hauza Ilmiyya wacce marigayi sayyid Ali Alawi ya assasa a unguwar Ubaidi a nan birnin Bagadaza.

Ya kamala karatunsa na boko (academic) a Bagadaza, inda ya samu shedar digirinsa na injiniyan gine-gine (building engineering) a kwalejin Injiniyoyi/ Jami’ar Bagadaza a shekara ta 1982 AD, a wannan lokacin ya kamata ne ya je ya yi aikin hidimar kasa abin da aka tilastawa dukkan ‘yan kasa su je su koyi aikin soja, sai kuma ya zama a daidai lokacin ana yaki tsakanin Iran da Iraki, kuma shi tarbiyar da ya samu ta addini ba za ta barshi ya sanya kayan soja ya shiga wannan yakin na zalunci ba don gudun cewa daidai da sa’a guda kar ya zama daya daga cikin azzalumai, to sai ya zabi ya zauna gida tare da hadarin da ke tattare da zaman gidan ga rayuwarsa, domin jami’an gwamnati sun watsu a ko’ina musamman ma dai a Bagadaza suna kame kuma kai tsaye a bainar jama’a suke sanya bindiga su harbe dukkan matashin da ya ki yadda ya shiga aikin soja.

Ya mayar da hankalinsa kaco-kaf wajen ci gaba da karanta littafai da koyarwa da shiga cikin zurfin tunani, sannan kuma sai ya fara rubuce-rubuce da wallafe-wallafe – kamar akwai littafinsa mai suna: Rawar da Imamai (as) suka taka a rayuwar Musulunci – ba tare da ya samu wanda zai dauki nauyinsa ba a cikin wannan yanayi na danniya, har Allah cikin ludufinsa ya takaita lamarin ta hanyar samar da wata dama ta sirri da wasu hanyoyi wadanda ana iya tuntutuba da tattaunawa a tsakaninsa da sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu), hakan ya faru a shekara ta 1985 AD ne, kuma har wannan din ya kai ga ya haifar da an samu damar buga wasu littafai da wasiku da suke magana a kan fikirar Musulunci, halayen kwarai a Musulunci da bahasi a kan tarbiyyar ruhi, kuma duk bahasosin an hade su ne a cikin littafai guda biyu wato: (Al-shahidul Sadrul Thani Kama A’arifuhu, da daya littafin mai suna “Qanadilul Arifin”, kamar yadda sayyid shahid Sadr II, albarkacin sakonnin da ke cikin wadancan fikirorin ya rubuta mausu’a (rumbun tattara bayanai) dinsa mai girma (Ma Wara’al Fikhi) da littafin (Nazratun Fi Falsafatil Ahdath) a duniyar yau – .

To bayan yakin Iran- Iraki ya zo karshe a shekara ta 1988 AD, sai ya koma Najaf mai tsarki, ya yi aure ya auri ‘yar marigayi shahidin Intifadar Sha’abaniyya Allama sayyid Muhsin Musawi Guraifi.

A shekara ta 1991 AD ya yi tarayya cikin Intifadar Sha’abaniyya, har ma ya fita tare da mujahidai ‘yan birnin Najaf mai tsarki domin ba da kariya ga Karbala Mukaddasa bayan jami’an jamhuriyya sun kai mata hari don su rusa ta, to sai dai dakarun juyin-juya hali sun mayar da shi tare da wadanda ba su da makamai zuwa Najaf, a saboda haka bai samu damar yin tarayya da su a yakin ba.

Amma ya rubuta bayanai da kalmomi masu muhimmanci a kan a taimakawa Intifada ya kuma yaba wa matasanta tare da daukaka matsayinsu, wasu sakonnin ma ya yi amfani da lasifiku ne ya daga murya sosai don sakon ya isar kunnuwan kowa a dandamalin Haidari mai tsarki.

To bayan dakarun juyin-juya hali sun yi mubaya’a ga sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) a matsayin jagoran darakun juyin-juya halin kwana daya kafin a kama shi, ya kafa lajanoni guda biyar domin jagorantarta, sai ya sanya shaikh Yaqubi a matsayin shugaban lajanar siyasa da sanarwa (Lajnatul Siyasiyati Wal- I’ilamiyyati).

Sai dai wadannan lajanonin ba su iya samun damar fara yin ayyukansu ba saboda hujumin da jami’an jamhuriyyar Saddam suka kawo birnin Najaf bayan kwana daya da kafa su.

A farko-farkon shekarar 1992 AD daidai da watan (Sha’aban/ 1412 AH) ne ya fara yin shigar malamai a inda babban marji’i marigayi sayyid Khu’i (kuddisa sirruhu) ya daura masa rawani.

Ya kasance na farkon da ya tabbatar da marji’iyyar sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) kuma mutum na farko da ya taimaka masa a farkon bayyanar da marji’iyyar tasa a cikin wannan shekara din, kuma wannan shi kansa sayyid shahid Sadr din ya bayyana hakan a wata ganawar da aka dauka (recording), har ya yi bayanin da ya gamsar da mutane masu yawa a cikin Hauza ta ilimi da wajenta cewa shi fa yana tare da shi (kuddisa sirruhu), ya kuma yi musu ishara a kan suna iya komawa ga sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu) (dangane da lamurransu na hukunce-hukuncen addini) har dai al’amarin marji’iyyarsa (kuddisa sirruhu) ya yadu a ko’ina, kuma shaikh Yaqubi shi ne ya zama mutumin da yake a mataki na biyu dangane da wannan lamari na marji’iyya bayan sayyid Sadr (kuddisa sirruhu).

Sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) ya nada shi a matsayin shugaban Jami’atul Sadr Al- Diniyya ba da jimawa da assasata ba, ita wannan makarantar wata cibiya ce da aka samar da nufin kawo sauyi, kamala, daidato da fahimtar juna a tsakanin makarantun Hauza da jami’oin zamani (academic), a wannan lokacin sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu) bai samu wani mutum da ya fi samahat shaikh Yaqubi cancanta ya jagoranci wannan cibiyar ya kuma iya cimma hadafofinta kamarsa ba, domin shi gwani ne da ya gwanance daga dukkan rassan guda biyu – kamar yadda shi kansa (kuddisa sirruhu) ya ambata hakan ga shaikh a lokacin da ya dora masa wannan nauyin a cikin watan Safar shekara ta 1419 AH.

Kuma sayyid (kuddisa sirruhu) ya kasance yana yabonsa yana kuma nuna shi, an ma buga wani yanki na zantukansa a cikin mukaddimar littafi mai suna: (Al-Mushtaqqu Indal Usuliyin) da kuma: (Qanadilul Arifin), sannan wata biyar kafin shahadarsa a ranar 5/ Jimada Thani/ 1419 AH, wanda ya yi daidai da 27/9/2019 AD, ya zabi shaikh Yaqubi a matsayin wanda zai kalifance shi, za a samu wannan a zancensa da aka dauka (recording) wanda ya yi wa dalibai a ganawarsa da su a Jami’ar Sadr Al- Diniyya: (…..A yanzu zan iya cewa lallai zabi daya tilo a Hauzarmu shi ne samahat shaikh Muhammad Yaqubi zuwa lokacin da Allah ya tsawaita min rayuwa na shaidi ijtihadinsa… don haka shi ne dai wanda ya dace ya riki lamarin Hauza a bayana, ina gaba da wanda ya yi gaba da shi).

Haka dai shaikh (Yakubi) ya dinga bi sannu a hankali kafin ya bayyanar da ijtihadinsa domin kiyaye ladubban Hauzar Ilimi, amma dai ya dinga yada bahasosin istidlalinsa wadanda ya rubuta tun a shekara ta 1420 AH, sai samahat Ayatullah shaikh Muhammad Ali Kurami “dama zilluhul sharif” ya shaidi cewa lallai ya kai matsayin ijtihadi albarkacin bahasosinsa da suka yadu a tsakanin malamai da dalibai a shekarar 1424 AH/ 2004 AD, (kuma ya samu shaidar ijtihadi daga wurin samahat Ayatullah shaikh Muntazari (kuddisa sirruhu) da samahat Ayatullah shaikh Muhammad Safi Tehrani (kuddisa sirruhu) da shaidar ijtihadi daga sayyid Khu’i (kuddisa sirruhu) a shekarar 1386 Shamsiyya da sauransu), muna fatan Allah ya ji kan wadanda suka gabata ya kiyaye wadanda suka yi saura. 

Ya lizimci sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu) har zuwa lokacin da ya yi shahada a watan Zulki’ida 1419 AH wanda ya yi daidai da 1990 AD, kuma shi ne ma wanda ya yi masa sallar janaza tare da ‘ya’yansa biyu da wasu ‘yan kadan da ba su fi cikin-tafin-hannu ba na masoya a cikin yanayi mai tsanani kewaye da dakarun hukuma masu dauke da manyan makamai.

Samahat shaikh Yaqubi ya daukarwa kansa nauyin ci gaba da gudanar tare da bunkasa wannan tafiya ta Harkar Musulunci wacce sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) ya samar da ita a Iraki haka nan yana kiyaye tsare-tsarenta da ka’idodinta wadanda mafi yawanci mabiyansa ne (kuddisa sirruhu) suka kafa su, kuma ya samar da wasu sababbin tsare-tsare bayan hukuma ta kawo cikas cikin tsare-tsaren da sayyid shahid ya dora su a kai, daga cikin irin tsare-tsaren da ya kawo akwai gabatar da sallar Juma’a mubarakah.

 

 

Karatuttukansa Na Addini

Bisa la’akari da tarin iliminsa da wayewarsa, za mu iya cewa lallai samahat shaikh Yaqubi ya fara karatunsa daga matsakaicin mataki wato ya fara da karatun (sharhul Lum’ati da usulul Fikhi na shaikh Muzaffar (kuddisa sirruhu)) a jami’ar Najaf ta addini a gurin shugaban makarantar marigayi sayyid Muhammad Kalantar (kuddisa sirruhu), dandanan ya sa himma da kwazo ya tattake matakai masu yawa cikin dan kankanen lokaci, sannan a daidai lokacin da ya fara karatunsa mai zurfi kawai sai ya hade shi tare da karatun da ake kira ‘Bahsul Kharij’ (matakin karatun da ke a gaban wanda yake yi) yana yinsu cikin lokaci guda bisa kwadaitarwar da sayyid shahid Sadr ya yi masa a kan ya yi hakan, don haka sai ya dinga halartar bahasinsa (kuddisa sirruhu) na (Al-Usulul Lafziyya) daga watan Shauwal 1414 AH har zuwa lokacin da ya yi shahada a watan Zulki’ida 1419 AH, haka nan ma ya halarci bahasin (Al-Usulul Amaliyya) a wajen samahat Ayatullah shaikh Muhammad Ishaq Fayyad a shekarun 1417 – 1421 AH, ya kuma dinga halartar karatun fikihu a wajen Ayatullah sayyid Sistani a shekarun 1415 – 1420 AH, ya kuma halarci karatu a wajen marigayi shahid Mirza Ali Garawi (kuddisa sirruhu) a shekarun 1416 – 1418 AH, a gabaki dayan karatuttukan ya dinga rubuta darussan malaman nasa ne da hannunsa.

Ya fara koyar da darussan ‘Mukaddimat’ (wato matakin farko wanda ake kiransa da shimfida a Hauza) tun bai shekara da fara karatunsa a jam’iar Najaf ba, sannu a hankali kuma sai yana kara fadada karantarwarsa zuwa matsakaicin mataki (Lum’at da Usulul Fikhi) har zuwa mataki mai zurfi (Makasib da Kifaya), kuma ajinsa da yake koyarwa ya kasance daga cikin mafiya yawan dalibai haka nan ma ya fi sauran ba da tallafin karatu.

Ya fara ba da muhadarorinsa na (Bahasul Kharij) a fikhu a watan Sha’aban 1427 AH, yayin da ya zabi mas’alolin da aka fi samun tankiya a kansu domin su zama maudu’in bahasinsa, ta yadda yakan zabi mas’aloli masu zurfi a bahasi na ilimi, wadanda ake zafafa bincike wajen tattauna su a tsakanin fakihai domin ya zama ya kara daukaka darajar ilimi, adadin masu halartar wannan bahasi nasa sun kai kimanin mutune (200) daga cikinsu akwai malamai masu zurfi a ilimi da wadanda suke koyarwa a Hauzar ilimi. Zuwa yanzu ya tabo wasu nau’oi na mas’aloli muhimmai a ilmance da a aikace. Wadannan bahasosin nasa ana buga su a cikin wani littafi mai suna (Fikhul Khilaf) zuwa yanzu an buga mujalladi tara na wadannan bahasosin wadanda suke dauke da mas’aloli guda hamsin da daya a cikinsu, kuma daga cikin abin da yake kara bambanta bahasinsa da na saura shi ne cewa a bahasinsa yana bijiro da ra’ayoyin manya kuma fitattun malamai magabata da manyan malamai na yanzu inda ya takaita da malaman makarantun Najaf mai tsarki da Qum Al- Mukaddasa.

Yana da risala amaliyya (littafin da ya rubuta fatawoyinsa) mai suna ‘Subulul Salam’, mujalladinsa na farko ya fito ne a shekarar 1430 AH a cikin littafin akwai fatawoyinsa bangaren ibada, kuma an yi ta maimaita buga shi ba sau da dama, kuma yanzu haka ana kan aikin mujalladinsa na biyu wanda ke magana bangaren ‘mu’amalat’, kamar yadda yake da ‘risala amaliyya’ mai magana a kan manasikul Hajji kuma shi ma an yi ta buga shi ba daya ba ba biyu ba.

 

Wallafe-Wallafensa

1- Fikhul Khilaf: Zuwa yanzu an buga mujalladai tara wanda yake bahasosinsa ne da yake gabatarwa na ‘Bahasul Kharij’ a Najaf mai tsarki to sai ake mayar da su littafi.

2- Al-Fikhul Bahir Fi Saumil Musafir: (Fikihu ne wanda a cikinsa ake kawo dalilai na nassosi masu zurfi).

3- Khidabul Marhala: An buga mujalladai tara a cikinsa, a cikin littafin akwai hudubobin malamin, zantukansa, abubuwan da ya gamsu da su a bayanansa da shiryatarwarsa ga al’umma, tun lokacin da ya karbi ragamar jagorancin Harka Musulunci da kula da kiyaye tafiyarta tare da bunkasa ta a Iraki bayan shahadar sayyid Sadr (kuddisa sirruhu) a shekarar 1990 AD, kuma an jera hudubobin nasa bisa la’akari da tarihin yinsu, wanda hakan yana ba da wani tagomashi mai girma ga tarihin Iraki da kuma Harkar Musulunci.

4- Al-Uswatul Hasanati Lil-Qadati Wal-Musallahin: Mujalladi daya ne, bahasin da yake cikin littafin ya tabo sirar Annabi (s.a.w.a) ne tare da yin bayani filla-filla da kuma daukar darussa da ababen koyi daga rayuwarsa (s.a.w.a).

5- Daurul A’imma Fil Hayatil Islamiyya: Mujalladi daya ne, an yi amfani da irin tsarin littafin da ya gabace shi wajen rubutu, sai dai shi yana magana ne kan sirar Imamai Ma’asumai (as) da kuma hadafin da suka yi tarayya a cikinsa wajen kokarin hakkakar da shi, haka nan kuma akwai ta’alikin sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu).

6- Al-Ma’alimul Mustakbalat Lil-Hauzatil Ilmiyya: Mujalladi daya ne.

7- Al-Riyadiyyat Lil-Fikhiyya: Mujalladi daya ne, littafi ne kwara daya tilo a wannan babin wanda ya yi sharhi a kan asasin lissafi na wani adadi mai yawa na mas’alolin fikihu a cikin babuka mabambanta.

8- Al-Mushtakku Indal Usuliyyin: Mujalladi daya ne mai rassa guda biyu, a cikinsa akwai bayanai na karatun sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu) da ya yi a kan ilimin usul karkashin bahasinsa mai suna (al-mushtakku), kuma har sayyid din ma ya buga shi a cikin daurorinsa na usul wato (Minhajul Usul).

9- Al-Shahidul Sadrul Thani Kama A’arifuhu: Mujalladi daya ne, a cikinsa akwai tattaunawar samahatul shaikh da sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu), wasiku da bahasosin da suka dinga kai-kawo a tsakaninsu, duk wadannan tarihinsu yana komawa ne tun wajajen shekarar 1985- 1986 AD.

10- Kanadilul Arifin: Mujalladi daya ne a cikinsa akwai sakonni da wasiku da suka dinga kai-komo a tsakanin samahatul shaikh da kuma sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) musamman wadanda suke da alaka da abin da ya shafi tsarkake zuciya da komawa zuwa ga Allah Tabaraka wa Ta’ala, su ma wadannan tarihinsu yana komawa ne tun wajajen shekarar 1987 AD.

11- Salasatun Yashkun: Mujalladai ne da suka kunshi littafai guda uku, yana bahasi ne a kan kukan da Qur’ani, masallaci da Imami (as) za su kai a gaba ga Allah na wofintar da su da aka yi, kuma kowanne an buga shi a matsayin littafi guda mai zaman kansa.

12- Al-Fikihul Ijtima’i: Mujalladai guda uku ne da a cikinsu aka rubuta fatawoyi masu magana a kan sha’anin zamantakewar mutane wadanda samahatul shaikh da kansa ya rubuta su gwargwadon ra’ayoyin da ya bayyanar masu wannan unwanin (Al-Ususul Amma Lil-Fikhil Ijtima’i).

13- Nahnu Wal Garb: Littafi ne da yake bayani a kan tushen dabi’u da abubuwan da turawa suka fi karkata gare su ta fuskacin wayewa ta yadda ba su da wata ka’ida, sabanin koyarwar musulunci mai nizami. Wannan littafin ya gangaro ne sakamakon cakuduwar al’adun turawa da suka shiga tsakankaninsu da na musulmi mazauna cikinsu a kasashen turawan bayan abin da ya faru a ranar 11 ga September 2001.

14- Min Wahyil Gadir.

15- Fikhu Dalabatil Jami’a.

Da dai sauransu na daga littafai da handi-awut (handout).

 

Sannan bisa la’akari da bukatuwar jama’a ga ainahin su littafai da handi-awut (handout) din, sai samahatul shaikh ya kallafawa wani sashe na manyan dalibansa rubuta littafai ta yadda yakan tsara wa dalibi yadda ya kamata fikirar rubutun ta kasance, kuma yana yi yana sa ido a kan rubutun tare da yin ‘yan gyare-gyare da suka dace har a isa ga an cimma manufa, saboda shaikh ya dinga ji a jikinsa cewa akwai nauye-nauye da yawa a kansa dangane da fuskantar abubuwan da suke bijirowa ga shi ba zai iya warware su shi kadai tilo dinsa ba, haka kuma ya yi fatan ya zama ya gina wasu ya horar da su wajen samun kudura ta yin hidima, kuma lallai ya samar da sama da mutum dari, kuma kowannensu ya yi rubutu ko dai domin cike wani gurbi ko kuma warware wata matsala wacce sakamakon kyakkyawar fikira ne aka iya haifar da irin wannan.

Kuma lallai an wallafa daruruwan muhadarorinsa game da kyawawan halaye, fikira da abin da ya shafi zamantakewa a munasabobi daban-daban wadanda da yawansu an buga su sun zama littafai, akwai kuma matsayarsa a kan siyasa – game da abubuwa daban-daban da suka faru – da tsawatarwarsa da wa’azozinsa a cikin littafin (Khidabul Marhala) wanda zuwa yanzu an wallafa mujalladi tara na littafin.

 

Tsare-Tsarensa

Shaikh Yaqubi yana da ra’ayin cewa da yawa daga cikin nauye-nauye da ayyukan da suka hau kan maraji’ai dole ne gudanar da su ya zama a karkashin mu’assasoshi ne ba mutane a daidaikunsu ba, musamman ma da ya zama ayyuka sun kara yawaita gare su bayan faduwar mulkin Saddam a watan April shekara ta 2003 AD daidai da watan Safar shekara ta 1424 AH, sai wata dama ta samu ta isar da sakon musulunci mai albarka, wanda a baya ya kasance gabaki daya an katange yin hakan.

To sai ya fara da samar da irin wadannan mu’assasoshin da faduwar gwamnatin Saddam ba tare da bata lokaci ba, ta hanyar shirya mu’utamar na assasawa inda ya gayyaci manyan masana (Jama’atul Fudala) a ranar 30 ga watan April 2003 AD daidai da 27 ga Safar 1424 AH.

Wadannan manyan masana din wadanda suka kunshi malaman Hauza Ilmiyya masu kokari sosai cikin hidimta wa al’umma sannan kuma mutane ne da suke wayar da jama’a a kan lamarin sakon musulunci da manufofinsa a cikin al’umma domin su gamsar da su shi su kuma gina rayuwarsu a karkashin koyarwarsa, haka nan kuma wadannan manyan masana din sun tashi tsaye wajen jagorantar wannan lamarin da idan bas u din ba babu wanda zai yi.

Wadannan masu wannan yunkurin mai albarka sun kasance asalinsu dalibai ne na Jami’atul Sadr Al Diniyya wadanda suka kwankwadi tarbiyya ta ilimi, kyawawan dabi’u da fikira mai kyau daga gare shi. 

Haka nan kuma ya shirya wata ziyara wacce ya yi zuwa Bagadaza a inda ya kwana uku a birnin, har ma ya jagorancin sallar Juma’a a filin masallacin Kazamain mai tsarki ranar 22 ga Safar daidai da 25/4/2003 AD, a wannan mahalli ya jawo hankalin dubunnan masallata kan abin da ya kamaci su gane kuma su fuskanta dangane da wannan sabon canji da yake aukuwa, kuma ya yi kira gare su da su fito kwansu da kwarkwata a hadu ranar litinin a filin Firdausi tsakiyar Bagadaza domin yin muzahara ta neman a samu sauyi, kuma lallai muzahara ce da ta cika ta batse makil don sai da tsawonta ya kai wasu kilomitoci.

Sannan a wannan ziyarar da ya yi ya samu ganawa da malaman jami’a da kwararru, kuma ya yi kira ga mabiyansa a kan su kafa wata lajana ta siyasa ta yadda za su iya shiga cikin siyasa a dama da su musamman a yanayin bayan faduwar daular Saddam a shekara ta 2003, domin a samu damar isa ga hadafin musulunci da na ‘yan kasa wanda dama akwai rubutu tsararre na yadda ya kamata a tafiyar da al’amuran cikin gida wanda kungiyar Hizbul Fadilatil Islami suka yi kuma yana taka rawa daidai gwargwado, kamar kuma yadda yake da wakilai a cikin majalisar kasa.

Kamar yadda samahatul shaikh ya yi karin haske mai yawa dangane da yadda za a tsara wadannan lamurran nata don karfafa irin rawar da za su taka, kamar masu jan ragamar su kasance malamai ne da kuma daliban da suka kammala jami’a a karkashin kungiyar daliban jami’a wato (Jami’iyyun) da kuma injiniyoyi a karkashin kungiyarsu (Tajammu’ul Muhandisinal Islami) da bangaren mata a karkashin (Rabidatu Banatil Mustafa (s.a.w.a) da sauransu, kuma shaikh bai gajiya ba wajen ci gaba da tallafawa wadannan mu’assasoshin.

 

Daga Cikin Mu’assasoshin Da Suke Tsaye Da Kafafunsu A Yanzu Cikin Taimakon Allah Ta’ala Baya Ga Abin Da Ya Shafi Jama’atul Fudala Akwai:

1- Jami’at Al- Sadril Diniyya: An assasa wannan jami’a a shekarar 1417 AH/ 1997 AD a karkashin kulawar sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu) kuma hadafin da ke tattare da assasata shi ne janyo hankalin daliban da suka kammala digirinsu a jami’oi na zamani zuwa makarantun Hauza domin a ba su tarbiyya irin wacce ta dace da dukkanin rassan guda biyu tare kuma da kawo sabon sauyi wanda zai karawa daliban na Hauza daraja, wannan fikira ce wacce tushenta ya fito daga sayyid shahid Sadr I (kuddisa sirruhu), to sai shi kuma sayyid shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) ya dora ta a kan tubalin gudanarwa a aikace, sannan ya zabi shaikh Yaqubi a matsayin wanda zai shugabanci jami’ar saboda shi mutum ne da yake da shaidar digiri na jami’a ta zamani kuma yana da karatu mai zurfi a Hauza, kuma lallai shaikh ya sa hikima da kwazo wajen kiyaye tare da bunkasa makarantar nan har bayan shahadar sayyid, musamman ma bayan faduwar gwamnatin Saddam ya himmantu wajen fadada makarantar da bude mata rassa a jahohi ta yadda yanzu tana da rassa fiye da 20 sannan yawan dalibanta sun kai mutum 2000 a tsakanin jahohin da suke a tsakiyar kasa da na kudancinta, guda shida daga cikinsu suna Bagadaza da kewayenta, hudu kuma suna Najaf mai tsarki wacce a cikinta Jami’ar ta asali kuma ta farko take, kuma samahatul shaikh shi ne wanda ya rubuta dokoki da ka’idodin jami’ar, manhajojin darussanta da ayyukanta tare da tsarin aikace-aikace a cikinta a cikin littafi mai suna (Jami’at Al- Sadr Al- Diniyya; Al- Hawiyyatu Wal- Injazat), tsawon muddar karatu a cikinta shekaru takwas ne, uku na farko shimfida ce mai suna kamar haka: (Attaujihul Dini Wal- Islahul Ijtima’iy, uku na biyu kuma ana horar da dalibai ne yadda za su iya koyarwa; wato (Kulliyatu I’idadil Mudarrisin), shekara ta bakwai da takwas kuma ana horar da dalibai yadda za su zama masu kwarewa; wato (Kulliyatul Ijtihadil Mukayyad) wanda wannan ana gwama shi ne tare da bahasin da ake kira Bahasul Kharij, kuma zuwa yanzu an yi yayen dalibai karo barkatai.

 

2-Jami’at Al- Zahra (as) Lil Ulum Al- Diniyya: Ita wannan jami’ar tana a matsayin kwatankwacin Jami’at Al- Sadril Diniyya a manhajin karatunta, tsarin tafiyarwarta da marhalolin karatunta sai dai ita an assasa ta ne bayan faduwar gwamnatin Saddam a shekarar 1424 AH/ 2003 AD, kuma ta kebanci mata ne kawai, zuwa yau tana da rassa guda goma sha hudu a Najaf da sauran garuruwa, tana da daruruwan dalibai, kuma an kiyaye tsarin tafiyarwarta ga hannun mata don suke jagorantarta, a cikinta kuma an gwama ta da wani sashe mai suna (Ma’ahad Al- Zahra Lil Khidaba) wanda yake sashe ne mai tarbiyyantar da dalibai su kware wajen wa’azi a kan mimbari (a bainar jama’a) domin fuskantar matsalolin zamani masu kutsowa cikin al’umma.

    

3-Rabidatu Banatil Mustafa (s.a.w.a):  Wannan wata mu’assasa ce wacce aka samar da ita domin ta kawo daidaito a cikin ayyukan mata, ta fara da kafa sakateriya a Bagadaza da wasu sakateriyoyi a sauran jahohi, kuma suna aiyuka masu dimbin yawa da suka shafi zamantakewa ta yau da kullum a cikin al’umma a karkashin gomomin mu’assasoshi da kungiyoyi, kamar kulawa tare da taimakon matan da mazajensu suka mutu, kananan yara, koyar da mata ilimin addini da ya shafi akida da hukunce-hukunce, taimakon gajiyayyu, samar da darussa (daurori) na karatu ga manya domin yaki da jahilci, koyar da computer, dinki, koyar da kiwon lafia a matakin farko (first aid), yadda za a dinga raya munasabobin addini da na al’umma, da jawo hankulan mata domin su dinga yin rangwame wajen bukukuwa da aurar da ‘ya’yansu.

Samahatul shaikh ya rubuta masu dokoki da ka’idodin wannan tafiya tasu (Rabidatu Banatil Mustafa (s.a.w.a)) da sauran tsare-tsare na ladubban da za su taimaka wajen kara tsara masu tafiyar ta yadda su matan nan masu tabligi kuma wadanda suka mallaki shaidar digirinsu a hannu a makarantun jami’oi na zamani da na addini su a kan kansu za su iya jagorantar mu’assasar da sauran rassanta har ma a dinga damawa da su a fagen siyasa.

4- Hizbul Fadilatil Islami: Bayan faduwar gwamnatin Saddam a shekara ta 2003, samahatul shaikh ya hori mabiyansa a kan su kafa jam’iyyar siyasa domin su dinga shiga fagen siyasa ana damawa da su saboda hakan zai taimaka wajen hakkakar da manufofin musulunci da na ‘yan kasa, kuma tuni mu’assasar (Hizbul Fadilatil Islami) ta samar da tsarin gudanarwa, don haka sai aka zabi kwararru ‘ya’yan Harkar Musulunci daga cikin daliban da suka kammala jami’a suka shiga cikin ayyukan siyasa gadan-gadan har ta kai ga sun sami kujeru a majalisar kasa ta Iraki da sauran majalisun jahohi, kuma tsarinsu ya bambanta da na saura wajen kiyaye ayyukan gina kasa, harshen larabci, musulunci da kiyaye hakkin ‘yan adamtaka sannan kuma suna kaucewa duk wani tsukakken tunani na son rai da duk abin da zai kawo bangaranci, samahatul shaikh ya rubuta wasu tsare-tsarensa kamar irinsu: (Tushen ka’idodin Hizbul Fadilatil Islami), (daga cikin wajibobi na shari’a akwai shiga harkokin siyasa), (tabbatattun dokoki a fagen siyasa), (ka’idodin bayyanar da komai a sarari cewa a tsaya kan gaskiya da gaskiya da tushensu daga makarantar Ahlul Bait (as)), kuma ya rubuta yadda tsarin jagorancinsa na siyasa ya kamata ya kasance da (abubuwan da suka sanya Hizbul Fadilatil Islami suka kebanta daban da saura), (tsarin da ya cancanta da hukumar Iraki), (dalilan da suka janyo manyan kwararrun mutanen nan suka zabi su kafa siyasa), sannan samahatul shaikh ya bayyana danagantar da ke akwai a tsakanin mu’assasar kwararru (Jama’atul Fudala) da jam’iyyar kwararru (Hizbul Fudala) a cikin wata takadda mai kunshe da nukudodi guda takwas.

Wannan jam’iyya tana da babbar sakateriya a Bagadaza wacce ta kunshi ofishin siyasa, ofishin watsa labarai, na tsara harkoki, na zartar da su, ofishin mata, na shirye-shirye, na bunkasa gwaninta kala-kala da al’adu da sauransu; kuma yana da sakateriyoyi a cibiyoyinsu na jahohi, da ofisoshi a gundumomi, da wasu wurare da aka kebe don gudanar da tsare-tsare a unguwanni da a kungiyance.

5- Nakabatul Sadatil Alawiyyin (Kungiya mai kula da sharifai): Makasudin kafa ta shi ne kula da zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a) daga ‘ya’yan Nana Fatima Azzahra (as) tare da biya masu bukatunsu da daukar nauyin auren matasansu, kuma wannan kungiya tana da sakateriya da cibiyarta a Najaf mai tsarki, sannan karbabbiya ce a sauran jahohi kuma tana da kujera a majalisa a cikin jerin ‘yan majalisun jam’iyyar Hizbul Fadilatil Islami, sannan samahatul shaikh Yakubi ya rubuta littafai da yawa don bayanin  dalilan kafa ta, tsare-tsaren ayyukanta da hidimar da ta ke yi a cikin al’umma.

6- Tajammu’ul Muhandisinal Islami: Kungiya ce ta samar da tattalin arziki da fasaha ga masu tabligi, ta yadda al’ummar Iraki suka samar da injiniyoyi sama da mutum dubu da yawansu muminai masu tabligi, kasar kuma tana ta samun bunkasa ta bangaren gine-gine domin kawo sabon sauyi yadda za ta iya tsayuwa da kafafunta da taimakon wadannan injiniyoyi dakakku masu iklasi. A saboda haka an kafa wannan kungiyar ne wadda ta rungumi wadannan masu iklasi ta kuma zana masu ayyukansu tare da ba su horo na musammam don gina makomar Iraki, kuma an samu kungiyoyi wadanda suke karkashin wannan tajammu’u din suna aiki bakin iyawarsu koda yake ba wani aiki ne mai girma ba, saboda irin wadannan ayyukan suna bukatar wani karfi wanda a halin yanzu babu shi sai dai ana sa rai Allah cikin ludufinsa zai kawo dauki.

7- Jami’iyyun: Mu’ssasa ce wacce ta hada da malamai, daliban jami’a, da sauran cibiyoyin makarantun Iraqawa, kwararru, da kuma jami’ai masu ayyuka a cikinta har da ma wadanda suka karbi kwalayensu na digiri dinsu na jami’a, kuma lallai samahatul shaikh Yaqubi ya rubuta jawabi danagane da (kafuwar Jami’iyyun, manufofinta da fatan da ake da shi daga gare ta), a ciki ya bayyana cewa kafa ta yana da asali ne da bukatar tabbatar da hadin kan ‘yan kasa wanda zai fara tun daga jami’oi, domin su ne kawai cibiyoyin da rikicin kabilanci da takaddamar siyasa ba ta ruguza su ba, kari a kan sauran manufofinta wato kulawa da cancanta da sabunta kere-kere wadanda jami’oin suke amfana da su wajen sake gina kasa da ci gabanta da sake inganta jami’oi da ma’aikatansu da sauran daliban da suke yin karatunsu a wajen jami’oin, wannan cibiya an kafa ta ne a shekarar 2006, kuma samahatul shaikh a wani taro na shekara-shekara da aka gabatar a Karbala mukaddasa a kwanukan Ashura a shekarar 1428 daidai da January 2007 ya yi kira a kan a mayar da hankali wajen farfado da ilimin kimiyya da na addini. Haka nan kuma suna taka babbar rawa gurin halartar manya taruka na addini kamar tunawa da shahadar sayyida Zahra (as) a ranar 3 ga watan Jimada Sani a Najaf mai tsarki ta kowace shekara, yayin da suke aiwatar da al’amurra da daman gaske na tunawa da shahadarta (as) a wannan dare na shahadar, ta yadda za ka samu sukan zauna cikin tsari a cikin wannan maukibi wanda yake fuskantar Haramin Imam Ali (as). 

8- Hai’atu Munazzamatil Mujtama’il Madani (Majalisar Cibiyoyin Jin Kai): Majalisa ce da take hidima ga dukkan bangarorin addini, tana da gomomin rassanta a Bagadaza da makamantansu a wasu jahohin, kuma tsare-tsarensu yana zuwa ne daga babbar cibiyar wacce take da helkwata a Bagadaza, tana da tsarin ayyuka kala-kala kamar abin da ya shafi raya al’adu, taimakon gajiyayyu, yin ayyukan gayya don tallafa wa al’umma, kulawa da marassa lafiya da sauransu dai, kuma ayyuka ne na sa kai ba wai biya ake ba, amma tare da haka za ka samu matasa masu dimbin yawa suna hidima ga jama’arsu. Samahatul shaikh Yaqubi yana da wallafe-wallafe da yawa da suke kwadaitarwa wajen kara bunkasa irin wannan cibiyoyin da kuma samar da nau’oin ayyukan daban-daban tare da samar mata da kayan aiki domin a kara inganta ayyukanta.   

9- Cibiyoyin Kafafen Sadarwa:

(a) - Kanatul Na’im Al-Fada’iyya (Na’im TV): Wannan tasha ta Na’im tashar tv ce ta tauraron dan adam ta addini wacce take yada shirye-shiryenta bisa koyarwar addini daidai da mahangar Ahlul Bait (as), haka nan ma ana koyar da darussa na kyawawan dabi’u, tarbiyya, ilimin zamantakewa masu amfani, sannnan tana warware da yawa daga cikin matsalolin da ake samu a tsakanin al’ummar Iraki, wadannan shirye-shiryen ana yada su ne daga Basra amma cibiyoyinta na asali suna Najaf mai tsarki da Bagadaza ne, sai dai kuma tana da wasu rassa a sauran jahohin Iraki. Shaikh Yaqubi yana da zantuka masu yawa da ya yi a kan muhimmancin kafafen sadarwa na zamani, da rawar da yin jawabai da irshadi a cikinsu suke takawa a rayuwar al’umma.

(b) – Radion Kasa a Bagadaza.

(c) – Fata Na Gari Radio a Basra.

(d) – Subulul Salam Radio a Nasiriyya.

(e) – Rumaitha Radio a Lardin Samawah.

 

Daga cikin tsare-tsarensa na addini akwai assasa ziyarar sayyida Fatima (as) a makwancin Imam Ali (as) a ranar 3 ga Jimada Sani  ta kowace shekara domin raya shahadar Siddika Zahra (as) wanda hakan yana da kaso mai yawa wajen fantsama al’amarin Sayyida Fatima (as) sannan kuma yana fito da girman tasirinsa ga jama’a, don dubun dubatar muminai ne suke shiga ana yin wannan jana’izar – wacce misaltata ne kawai ake yi – zuwa cikin Harami mai tsarki na Imam Ali (as), wanda a gurin samatul shaikh yakan gabatar da jawabansa da suke nuni a kan sakon da wannan munasabar take dauke da shi da kuma hakikanin abin da ya faru. Farkon raya wannan munasabar ya faro ne daga shekarar 1427 AH/ 2006 AD.

Kamar yadda bayan faduwar gwamnatin azzalumi Saddam ya shirya tarukan wayar da kai ga malaman jami’oi da dalibaita yadda mahalarta taron nan suka kai kimanin mutum dubu (20) a Karbala Mukaddasa a lokacin tunawa da waki’ar Ashura ta Imam Husain (as), kuma tarukan sun ci gaba da gudana na tsawon shekaru.

 

Ginshikan Ayyuka Na Harkar Marji’ancin Addini Na Bai-Daya

Harkar Musulunci a karkashin jagorancin samahatul shaikh Yaqubi ta ginu ne a kan wasu usulla wadanda shaikh din da kansa ya yi tarkizi a kansu a cikin littafansa da jawabansa, amma ga muhimman cikinsu a takaice:

1- Tsarkin niyya da yi domin Allah Ta’ala, saboda babban hadafi shi ne samun yardar Allah a cikin kowane motsi ko shiru, kuma lallai tushen samun nasara shi ne a kiyaye hadafi da tsara ayyuka a kan haka da katange duk abin da zai fita daga wannan da’irar.

2- Neman taimako daga gurin Manzon Allah (s.a.w.a) da Imamai Ma’asumai zuriyarsa (as), daukar Qur’ani da Sunnah mai tsarki a matsayin madogara ta shari’a, suluki da tsarin da za su gudanar da rayuwa.

3- Girmama dan adam da kallonsa a matsayin mafi daukakar halitta, dagewa wajen yi masa kowace irin hidima, sannan kiyaye masa mutuncinsa da jajircewa wajen bunkasa rayuwarsa.

4- Hadin kai, jituwa da masu ra’ayi mabambanta, yunkuri don ganin an samar da ayyuka nau’oi daban-daban, kaucewa  kowace irin rarraba, kiyayya da cukudewar lamurran da za su haifar da batawa da lalacewar zumunci.

5- Sanya ido sosai wajen zaben wadanda za su jagoranci al’umma bisa la’akari da ma’aunan da aka shimfida domin jagorancin al’umma shi ne tushe kuma abin dogaro ga rayuwar al’umma.

6- Tarbiyyantar da ruhi da kyawawan dabi’u da tsarkake zuciya har a koma zuwa ga Allah da kubutacciyar zuciya.

7- Tsamar da al’umma daga duhun jahilci, zaman kashe-wando koma-baya da munanan zato, dora su a kan yadda za su rungumi ilimi da ci gaba, addini da tsantseni.

8- Yin bayani a kan ma’anar musulunci na hakika, bayyana bangarorin karfinsa da girmansa, jawo hankulan mutane a kan su yi riko da shi tare da yin biyayya ga dokokinsa, wayar da kan mutane a kan su yi nazari game da illoli tare da raunin al’adun masu inkarin samuwar Allah da addini, gazawarsu a tunani da nizami wadanda su ne suke samarwa dan adam cikar kamala.

9- Tsari da sanya ido sosai a cikin ayyukan mu’assasa ta yadda zai zama kamar daukar jinka kowa ya kama bangarensa don aiki ya tafi daidai wa daida.

10- Yakar cin hanci da rashawa, barna da wuce gona da iri, zalunci da jiji da kai, mulkin mallaka, danniya ba tare da hakki ba, zage damtse da tsayin daka wajen taimakon raunana bakin gwargwado.

Wasu manyan malamai da masana sun wallafa littafai wadanda suke magana a kan tarihin rayuwar samahatul shaikh Yaqubi, jagorancin addininsa (marja’iyyarsa ta addini) da tsare-tsarensa, daga cikin littafan akwai: (shaikh Muhammad Yakubi Minal Zat Ilal Mujtama’i), (Nazariyyatu I’idadil Badil), (Al- Yaqubi Ka’idan) da dai sauransu.

Kalaman Sayyid Shahid Sadr II (kuddisa sirruhu) A Kan Samahatul Shaikh Yaqubi

1- A cikin mukaddima ta farko cikin littafin ‘Mushtak’ kalamansa sun zo kamar haka. Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godia ta tabbata ga Allah shugaban talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga mafi alherin halittarsa Muhammad da alayensa tsarkaka, la’ana ta din-din-din ta tabbata a kan gabaki dayan makiyansu. Bayan haka, daga ni’imomin Allah wanda tsarki ya tabbata a gare shi a kan addini da mazhaba bai-daya da kuma ni a kebance, ni wannan bawa da nake makaskanci mai kuskure, shi ne cewa Allah ya azurta ni da dalibai masu hazaka, iklasi, kwazo da jajircewa, ina fatan Allah ya saka masu da mafificin alheran da yake sakawa masu kyautatawa. Kuma hakika wanda ya fi sauran girma da muhimmanci daga cikinsu shi ne wannan babban shehin kuma allama madaukaki mai girma da daraja shaikh Muhmmad Musa Al- Yaqubi (Allah ya kara masa daukaka), hakika ya lizimci darussanmu na ilimin Usul, kuma lallai ya debi rabo mai tsoka wajen fahimtar karatun da yin rubutu a kansa da koyar da shi, yanzu haka a gabana ga shi nan a cikin wannan littafin nasa yana nuna mana himmarsa, kwazonsa da zurfin tunaninsa, lallai na bibiyi littafin daki-daki sai na same shi yana da cikakkiyar masaniya dangane da abin da ake da bukata na bahasin kuma cike yake da mas’alolin usul, a saboda haka sai nake kallonsa a matsayin mawallafin asali, duk da cewa mas’alolin da aka bijiro da su a littafin asalinsu da tushensu daga gare ni suka gangaro. To sai dai ni lallai na yaba masa domin ya kiyaye amanar ilimi kuma ya yi sharhi mai yalwa a kan mabna din bahasin nawa. Kuma lallai babu shakka irin wannan himma sannu a hankali za ta kai shi ga isa yin ijtihadi na ilimi da bayar da kariya ga mazhaba, ina yi masa fatan alheri a nan gaba a cikin yi wa ilimi da aiki hidima kuma ina fatan ya zama daga cikin maraji’ai masu iklasi kuma shugabanni na kwarai, Allah ya saka masa da mafi alherin da yake sakawa masu kyautatawa, daga karshe sai mu ce godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. An rubuta wannan a ranar tara ga watan Ramadan mai albarka 1418 AH, Muhammad Sadr.

2- Maganarsa a cikin mukaddimar juzu’i na biyu na littafin ‘Mushtak’: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, bayan sallama da godiya da addu’ar neman taufiki a gare ku, da fatan Allah ya tsawaita rayuwa, zan karanta wannan ayar mai girma da yin bayani iyakar fahimtata: “Kuma ka yi hakuri, hakurinka bai zamo ba face domin Allah, kuma kada ka yi bakin ciki saboda su, kuma kada ka kasance a cikin kuncin rai daga abin da suke yi na makirci. Lallai ne Allah yana tare da wadanda suka yi takawa da wadanda suke su masu kyautatawa ne”. To a iyakacin fahimtata: Lallai wadannan batutuwa da ka rubuta lallai bahasosi ne masu kyau sosai, amma zai yiwu a cikinsu – ala ayyi halin – ka kara fadada wasu ilimomin da ta yiwu kila za ka bukace su, koda dai cewa bahasosi ne masu karfafawa don haka ina fatan su zama sanadin haskakawa a cikin Hauza, jama’a da a cikin mazahabar baki dayanta, da kuma a kebe tun da yake bahasosi ne wadanda zuwa wani mikidari sun game abin da magabatan da da na yanzu suka rubuta don haka zai yiwu daliban Hauza, masana da masu fahimta su amfana, to kuma wannan wani lamari ne da ya cancanci asha wahala a kansa, muna fatan Allah ya albarkaci wannan kwazo naku kuma ya sanya ya zama an girbi alherinsa ta yadda za’a amfana da shi a kebe da kuma a bai-daya. To koma dai mene ne lallai wannan wani aiki ne da ya cancanci yabo sosan gaske, domin aiki ne wanda yake bukatar sadaukarwa mai girma a iyakar ganina, don haka ina ganin lallai akwai bukatar ya zama an ci gaba da gabatar da irin wannan lamarin mai girma, kuma hatta a batutuwan da suka yi tsauri ban ga wata tubka da warwara a cikin bahasin ba, kuma karshe dai lamari yana gare ku farkonsa da karshensa. Allah ya saka maku da mafi alherin da yake sakawa masu kyautatawa, dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, da fatan Allah ya barku tare da wannan miskinin.   

3- Kalaman da suka zo a cikin mukaddimar littafin Kanadilul Arifin a cikin wata wasika ta musamman da samahatu Ayatullah kuma madaukakin shahidi sayyid Muhammad Sadr (kuddisa sirruhu) ya aika wa samahatul shaikh Muhammad Yaqubi (Allah ya tsawaita rayuwarsa) a ciki ya rubuta: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, ya kai babban shehi ina fatan Allah ya kara maka daukaka, bayan sallama, gaisuwa da fatan alheri a gare ka, ina fatan za ka duba wadannan nukudodin kamar haka:

Kai da kanka ka san cewa ba ni da wani dalibi da ya fi ka a wajena tun a baya har zuwa yanzu, kuma kai ne ka fi su tsarkin zuciya, mafificinsu adalci da gaskiya, ta yadda da wani abu zai gudana a nan gaba a tsakanin masu neman marji’anci zan so al’amarin marji’ancin nan ya wanzu a hannun masu adalci, masu warware wa mutane bukatunsu na yau da kullum ba irin wadannan mutanen masu kekasasshiyar zuciya da kwadayin duniya ba, a saboda haka sai da ta kai ga na yi dogon tunani, har sai da na kure tunanina a kan cewa in sanya ka ka dinga yin limancin sallah a madadina a lokutan da ba na nan, a matsayin shimfida da nufin cewa a bayana kai ne za ka jibinci lamurran jama’a, kuma har yanzu ina nan a kan wannan tunanin, kuma wannan wasikar da na aiko maka ba za ta hana yiwuwar yin hakan ba, tun da yake har zuwa yanzu ban sami wani dalibi daga cikin dalibaina tare da yawansu da bambance-bambancen kwazonsu wanda ya kai ka cika dukkan sharudda kuma nake da fata daga gare shi kamar ka ba, a saboda haka ina rokon Allah ya tallafa maka cikin taimkonsa da kudurarsa. 1 ga Jimada Sani 1418 AH. Wani bangare a farko-farkon littafin “Al- Shahidul Sadr Kama A’arifuhu”.

4- Daga cikin zantukansa (sayyid shahid Sadr (kuddisa sirruhu)) wanda ya yi a Jami’atul Sadr, a ranar 5 ga Jimada Sani 1419 AH, (wato kafin shahadarsa da kimanin wata 5 kenan) yana cewa: “Yanzu zan iya cewa mutum daya tilo wanda zai iya neman marji’iyya a Hauzar nan tamu shi ne samahatul shaikh Muhammad Yaqubi, idan har Allah ya ara min rayuwa har na shaidi ijtihadinsa domin ba na kin a ce ya zama shi ne zai jagoranci Hauzar gaba dayanta a bayana.

Domin neman karin bayanai na rayuwarsa a duba abubuwan da suka zo a littafansa:

1- Al- Shahidul Sadr Kama A’arifuhu.

2- Kanadilul Arifin.

3- Al- Shaikh Musa Al- Yaqubi; Hayatuhu, Shi’iruhu.

4- Khidabul Marhala.

5- Al- Ma’alimul Mustakbala Lil Hauzatil Ilmiyya.

 

 

Jagorantar Lamurran Al’umma

Shi wannan bangaren yana kunshe ne da wasu ayyuka kamar haka:

1- Kula da al’amuran al’umma – a daidaiku da a bai-daya – kiyaye masu maslahohinsu, warware masu matsalolin da ke damunsu da kuma biya masu bukatunsu.

2- Tsayin daka wajen ganin an kare hakkokin al’umma a dukkan bangarorin addini, tattalin arziki, siyasa, fikira, halayen kwarai da zamantakewa.

3- Kiyaye wa al’umma hadin kanta su zama tsintsiya madaurinki daya, da kiyaye masu izzarsu da karamcinsu.

4- Shiryatar da al’umma zuwa ga kamala, dora su a kan tafarkin da zai zama sanadin samun tsirarsu a nan duniya da gobe kiyama.

5- Fuskantar zalunci, barna da wuce gona da iri, sannan kuma samar da wani yanayi wanda zai ba da dama wajen yada umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

6- Tsayin daka da himma wajen kare tsarin zamantakewar da ya hada kowa da kowa. 

7- Tsayuwa tsayin daka wajen ganin an tsayar da al’amuran jama’a wadanda baya halatta a wofintar da su haka kurum, kamar gudanar da sallar Juma’a, samar da nizami game da yadda za a sarrafa makamai, kayyade yadda za a sarrafa dukiyar al’umma da kiyaye hakkin masu hakki, kiyaye adalci wajen amfani da arzikin da Allah ya hore wa bayinsa da wurare na gama-gari da makamantansu. 

8- Tsoma baki cikin lamurran da sai an tantance shakkun da ke tattare da su wato (Al-shubuhatul maudu’iyya)[1], wacce a nan ba aikin mufti ba ne ba, a’a wannan aiki ne na jagora kuma majibincin al’amuran al’umma (waliyu amril umma), kamar tabbatar da tsayuwar wata, ba da damar a dauki makami domin ba da kariya ga Haramomi masu tsarki ga wadanda suke yunkurin sai sun tozarta guraren da makamantansu.

Kuma lallai wadannan unwanonin suna dauke ne da ayyuka da hidindimu masu yawan gaske wadanda suke da bukatar a ware fili na musamman domin a yi bayani a kansu.[2]

Amma a takaice shi malami wanda ya cika dukkan sharudda a matsayinsa na na’ibin Imami Ma’asumi (aj) na’ibanci na gama-gari – ba na’ibanci kebantacce ba, wacce ita wannan niyabar kebantacciya tana nufin kebantacciyar ayyanawa kai tsaye da nassi daga shi Imam din – to yana da dukkanin cancanta da nauyayen da Allah Ta’ala ya dora su ga Imami Ma’asumi (as) wadanda suka shafi tafiyar da sha’anonin al’umma na addini da na duniya, kuma su ne wadanda yanayi ya sa Imamul Ma’asum kuma Hujjar Allah wanda yake cikin gaiba a halin yanzu ba zai samu damar gudanar da su ba, wanda Allah ya bar wa kansa sanin dalilan boye lamarin bawansa ga mutane, koda yake akwai togaciya a aikin na malami kamar abin da ya shafi tabligi kai tsaye daga Allah Ta’ala da kuma siffofi kebantattu na Imam din kamar ma’asumanci.

Dalilin da yake nuni a kan wannan wilaya ta na’ibin Imam (as) – a wannan lokacin na gaibarsa – shi ne dai ainahin dalilin samuwar Imam din, wanda kuma shi ne hukuncin sanya jagora wanda za a koma zuwa gare shi domin kiyaye kasa da tsara al’amurran mutane na addini da na duniya, shi ya sa ma za ka samu Imam Ali (as) yana ambatawa game da wannan wajabcin a cikin maganarsa: “Babu makawa ga mutane ya zama suna da shugaba na kwarai ne ko fajiri, ta yadda mumini zai ci gaba da rayuwarsa ta yau da kullum, shi ma kafiri ya wataya a rayuwarsa a karkashin mulkin, har zuwa lokacin da Allah zai bayyanar da ma’abocin lamarin, ya dawowa da musulmi dukiyarsu ta baitul-mali, ya yaki makiya, albarkacinsa hanyoyi su samu aminci, a kwato wa gajiyayyu hakkinsu daga hannun karfafa, har ta kai ga mutumin kirki ya sarara a kuma hutar da shi daga cutarwar fajirai” [3].

To a saboda tabbatar wannan kaulin na ‘babu makawa’ to zai kasance lazim ne ya zama Allah ya sanya wanda zai jibinci lamarin al’umma daga gare shi, kuma dole ne wannan din ya kasance malami ne masanin dokokin Ubangiji kuma mai iko wajen lakantar masdarorin shari’a tare da cirato hukunci daga gare su, sannan kuma ya kasance mai tsananin kamewa da rashin biyewa son zuciyarsa da duniya, kuma ya zama mai komawa ga Allah Ta’ala ta yadda a koda yaushe yana tuna Allah a ransa haka nan kuma ya zama na Allah wato mai halayen kwarai[4].

Haka nan wannan hukunci na hankali yana samun karfafawa tare da irshadi daga abin da aka rawaito daga Bn Shazan daga Maulana Abil Hasan Al-Rida (as) a cikin wani hadisi yana cewa: “To idan ya ce mai ya sa aka wajabta masu sanin Manzanni da kuma yin imani da su da wajabcin yi masu da’a, to sai a ce masa: tun da yake su mutane a cikin halittarsu da zantukansu ba su iya samarwa kawukansu cikakkiyar amfanarwa ba, kuma a lokaci guda Mahaliccinsu wanda ya Daukaka a kan a iya ganinsa a zahiri, kuma gazawarsu da rauninsu sun bayyana karara cewa ba za su iya riskarsa da idirakinsa ba, don haka babu wata dama da ta yi saura illa ya aiko Manzo Ma’asumi wanda zai kasance jakada mai isar da sakonsa tsakaninsa da bayinsa ya sanar da su umarnin Allah da haninsa, ladubbansa, ya tsayar da su a wurin da zai amfane su, ya kautar da su daga wurin da zai cutar da su, domin ko a halittarsu ba su da ilimi a kan abin da zai cutar da su ko ya amfane su, don haka idan sanin Manzo da yi masa da’a ba su wajaba a kansu ba to zai zama zuwan Manzon ba shi da wani amfani kenan haka nan ma bai magance wata bukata ba, da kuma tabbatar da shi ya zama wasa ba tare da wata ma’ana ko fa’ida ba, alhali wannan ba sifofin mai hikima wanda ya kyautata kowane abu ba ne; idan kuma ya ce: to mai ya sa ya sanya ma’abota al’amari (ulul amr) kuma ya umarci a yi masu da’a, ka ce, ai kasantuwar mafi rinjaye a kan haka shi ne cewa su mutane yayin da aka dakatar da su a kan wata iyaka aka kuma nusar da su a kan kada su ketare ta domin hakan zai zama sanadin lalacewarsu, wannan dokar ba za ta gudana ba matukar ba an sanya amintacce wanda zai dinga hana su ketare iyakar da shiga cikinta ba, domin in dai bai zama haka din ba, to za ka samu wani fa ba zai iya barin jin dadinsa da abin da zai amfane shi kurum don abin da yake yin zai cutar da waninsa ba, don haka ne aka sanya masu mai sa’ido a kansu wanda zai dinga hana su yin barna kuma zai dinga tsayar da haddi a kansu da hukunce-hukunce. Kuma a kan haka ne mu lallai ba mu taba samun cewa akwai wata jama’a ko wani addini daga cikin addinai da suka rayu suka wanzu ba face sai suna da mai sa’ido kuma jagora a cikinsu domin babu makawa dole ne faruwar hakan a lamurransu na duniya da addini, a saboda haka ne ba zai yiwu cikin hikimar mai hikima ya bar halitta sakaka haka kurum ba alhali ya san babu makawa, lamurra ba za su taba tafiya daidai ba sai da samuwar amintaccen jagora ba, wanda zai yaki makiyansu, ya raba hakkokin  baitul mali ga mutane, ya tsayar masu da sallarsu ta Juma’a da ta jama’a, ya katange su daga zaluncin azzalumai, kuma da a ce Allah ba zai sanya masu Imami, tsayayye, amintacce, mai kiyaye masu hakkokinsu ya yi gadin dukiyoyinsu ba, to da al’umma ta rushe da an rasa addini, da an caccanza sunna da hukunce-hukunce da kuma an samu yawaitar ‘yan bidi’a da karancin wadanda ba su yarda da samuwar Allah ba sai kuma duk su danganta hakan ga musulmai, domin lallai mun ga gazawar mutane kuma suna cike da bukata kuma ba kammalallu ba tare da bambance-bambancensu, da sassabawar soye-soyen zukatansu, da warwatsewar su dama da hagu, to idan da ba a sa masu wani tsayayyen jagora mai kiyaye abin da Manzo (s.a.w.a) ya zo da shi ba, da sun lalace irin yadda muka bayyana, da sun caccanza shari’oi, sunnoni, hukunce-hukunce da Imani da kuma hakan ya zama lalacewar gabaki dayan halitta” [5].

Mas’ala: Mace ba ta zama jagorar al’umma (wilayatu amril umma).

Mas’ala: Kamar yadda yake cewa malami wanda ya cika dukkan sharudda na’ibi ne ga Imam (aj) a matsayi da cancanta to haka kuma shi na’ibinsa ne a cikin daukar nauyi da dawainiya da tsayuwa kan nauye-nauyen da Imam (aj) din da kansa yake tsayuwa da su, kuma mun ambaci da dama daga cikin irin wannan a cikin littafin (Dauratul A’imma Fil Hayatil Islamiyya).

Mas’ala: Yayin da ya zama nizamin siyasa ba yana tafiya a kan koyarwar musulunci ba ne kuma malami fakihi bai da yalwataccen iko a hannunsa, to a nan zai ba da izinin a kan cewa tasarrufat din da hukuma take yi in dai zai kiyaye nizami na zamantakewa ta bai-daya kuma ba za su sabawa shari’a ba to wannan hukuma za ta zama kamar tana wakiltarsa ne a cikin wadannan tasarrufofin, domin ko shi ne mamallakinta na hakika, a saboda haka ne ma aka shardanta neman izininsa wajen yin wadannan tasarrufofin, a sakamakon haka dukkan abubuwan da hukuma ta aiwatar na gine-gine, kafa cibiyoyi, zuba hannun jari da sauransu to mamallakinsu na hakika shi ne Imam (aj) kuma idan za a sarrafa su to ana bukatar izini daga na’ibin Imam (aj) wanda yake shi ne marji’i, don haka ba abu ne da ba a san mai shi ba ko kuma a ce ai wannan mallakin jama’a na bai-daya ne, ta yadda wani kawai zai bugi kirji ya ce ya mallake su, a’a ba haka abin yake ba.

Mas’ala: Malami (fakihi) ba ya tilastawa mutane sai sun yi masa biyayya a kan dole, sai dai an shardanta su al’ummar su nufi hakan da kansu su kuma samu gamsuwa a kan yi masa biyayyar, na’am a nan al’umma da muka ce ba muna nufin dukkanin al’umma ba ne, haka nan ma zaben waliyul fakih ba ya tabbatuwa da zaben dukkanin mutane, a’a abin nufi shi ne zababbun mutane da ake kiransu (ahlul khibra) wato kebantattun da wannan lamari ya shafa kuma su ne manyan mutane malaman Hauzar ilimi madaukakiya wadanda suka siffatu da tsantseni, tsarkin zuciya kuma masana a kan ayyukan da suka dace da al’umma da dabbaka tsare-tsaren musulunci mai albarka.

Mas’ala: Ya wajaba a kan malami (fakihi) ya tsara da aiwatar da zantuka da ayyuka daidai gwargwadon yadda Allah Ta’ala ya saukaka masa domin shawo kan mutane zuwa ga musulunci da nizamin musulunci da nuna cewa musulunci ya cancanci ya ja ragamar mutane zuwa ga samun tsira da aminci.

1436 AH.

2015 AD. 

 



[1] (Al-shubhatul maudu’iyya) tana nufin abin da asalin hukuncinsa sannane a wajen mukallafi wato yasan halal ne ko haram, to sai dai bai sani ba shin wannan abin da yake gabansa misali yasan shan najasa haramun ne amma yana shakku a kan cewa shin wannan ruwan da ke gabansa tsarkakke ne ko mai najasa.

[2] Domin shi (waliyu amril umma) mai gadon wanda ba shi da wanda zai yi gaje shi ne, mai jibintar dukiyar wanda ya bace, mai ikon sakin matarsa idan shekaru hudu suka shude ba tare da an ganshi ba, mai tilasta wanda ya boye kayan abinci sai sun yi tsada a kan ya fitar da kayan ya sayar nan take, mai kayyade farashi idan aka tsananta tsadar kaya ga mutane, yana da ikon shiga domin warware abubuwan da ake da shakku a kansu wadanda ake kira (Al-shubhatul Maudu’iyya) wadanda suke shiga cikin tsarin rayuwar mutane, kuma an shardanta neman izininsa domin a iya yin amfani da dukiyar da ba a san mai ita ba, yana da ikon sanya baki cikin duk aikin da zai zama an kawar da wata cutarwa ga mutane, kamar fadada masu tituna, rushe gine-ginen da ke shirin rushewa da kansu kuma za su iya cutar da wasu, zai karbi hakkokin Imam (aj) (kamar khumusi) ya sarrafa su wurin da ya dace, shi ne yake da iko a kan ayyana wa zai zama marikin yaro karami, wawa da mahaukaci, shi ne mai jibintar wakafofi na gama-gari, shi ne zai tsayu tsayin-daka wajen ganin an kiyaye nizamin zamantakewar mutane, kamar gina gadoji, makarantu, asibitoci, tono ma’adanai da gyaran filaye, kuma shi ne dai wanda zai ba da umarni wajen tsayar da haddi, ya saki matar mutumin da yake danne hakkokin matar da sauransu masu yawa…

[3] Nahjul Balaga Huduba ta 40 daga cikin zantukansa (as) a kan Khawarij yayin da ya ji zancensu suna fadin: “Babu hukunci sai na Allah”.

[4] Domin Karin bayani ka duba littafinmu mai suna: (Al-Uswatul Hasana Lil-Kadatil Musallahin).

[5] Ilalul Shara’ii Na Shaikh Saduk (r)