Farin Ciki Na Hakika / 57

| |times read : 862
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Farin Ciki Na Hakika / 57

Mutum yakan yi farin ciki idan ya samu dukiya, mukami da…. Sai dai dukkan wadannan masu gushewa ne, jin dadinsu ma na dan lokaci ne, ga shi kuma ba su da wata damar faranta ran mutum, amma sa’ada da farin ciki na hakika su ne mutum ya sarrafa wadannan ni’imomin a wajen neman isa ga hadafi na hakika wato neman yardar Allah, ta hanyar jajircewa wajen yin da’a a gare shi, domin wannan ne abin da yake kawo sa’ada ta hakika ga mutum. {Ka ce da falalar Allah da rahamarsa, sai su yi farin ciki da wannan, shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa} (Suratu Yunus, aya ta 58).