Wace Hanya Ce Za A Bi Domin A Dawo Da Koyarwar Qur'ani

| |times read : 942
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Wace Hanya Ce Za A Bi Domin A Dawo Da Koyarwar Qur'ani

      Yanzu zan sake dawo da tambayar nan wacce na ambata cewa: Wace hanya ce za a bi domin dawo da koyarwar Qur'ani cikin rayuwa da kuma amfana daga gare shi? Nauyin wannan yana kan bangarori biyu su ne: Al'umma da kuma Hauza madaukakiya, domin ita Hauza alami ce ta kawo canji da wayewa a cikin al'umma, da dora su a kan fikira sahihiya da komawa a kan koyarwa ta addini, kuma mun riga mun fada cewa mafi muhimmancin nauyin da ya kamata Hauza ta dauka shi ne tsayuwa tsayin daka domin su samar da rubutu game da ma’anonin da karantarwar Qur'ani, nazariyoyinsa, mahangarsa, akhlak dinsa da akidarsa – abubuwan da muka yi ishara ga wasunsu – zuwa ga al'umma a bisa koyarwa sahihiya kuma mai tsarki kamar dai yadda shi Qur'anin yake so, kuma sannan a yi aikin bisa la'akari da dacewa domin ya yi tasiri ya samu karbuwa a cikin rayuwar al'umma, kuma a yi amfani da hanyoyi masu yawa kamar mimbarin Husaini, wuraren yin wa’azi, a hudubar masallatan Juma’a, a masallatai a lokacin sallar jam’i, a cikin littafai, mujalloli da jaridu da sauransu.

       Sai dai kafin wannan dole ne a komo kan koyarwar Qur'ani bisa manhaji irin na Hauza, hakan kuma zai faru ne ta hanyoyi guda biyu:

       Na Daya: Darussa a matakin farko wato a matakin shimfida, da sadahi na farko-farko, wadanda za su ba da manhajoji kamar haka[1]:

1- Hadda da kuma tilawar Qur'ani da kiyaye shi daidai da ka’idar harshen larabci da kiyaye ka’idodin tajwidinsa yadda ya dace da shari'a.

2- Yin tafsiri a takaice na lafuzzansa ko da a matakin yin sharhi ne na kalmominsa, kamar yadda ya zo a tafsirin Shubar da makamantansa, domin dalibi ya samu fikira ta bai daya game da ma’anonin kalmomin Qur'ani.

3- Koyon darussan ilimomin Qur'ani, littafin da ya fi shi ne (Al-Bayan) ko kuma mukaddimar littafin Ala’ul Rahman wanda aka buga a farkon tafsirin Shubar.

4- Gudanar da musabakoki a kan ilimomi daban-daban na Qur'ani da kuma ware kyaututtuka ga wadanda suka yi nasara da wadanda suka samu rabo a musabakar.

       Na Biyu: Darussa na koli wadanda za su kasance kamar haka:

1- Bude bangare na musamman dangane da koyon darussan Qur'ani, kuma lokacin da ya fi dacewa da wannan shi ne bayan an kammala darussa na koli ta yadda kwararren dalibi zai iya samar da manhaji mai zaman kansa kuma zai iya amfana da wasu littafai da ke akwai, bayan an yi jarabawa wacce za ta bayyana dacewa da cancantar dalibin da yake son ya samu kwarewa a wannan sashen, ta yadda zai kammala wannan bayan ya samar da wallafe-wallafe masu alaka da abin da ya yi, domin ya zama malami mai koyarwa ko malami mai tafsiri ko mi bahasi a kan Qur'ani.

2- Koyon tafsirin Qur'ani koyo mai zurfi ko dai gabaki dayan Qur'anin ko kuma wasu ayoyi da yanki-yanki nashi domin isa ga wani hadafi ayyananne, kuma zai yiwu ya dauki wani littafin tafsiri ya yi nazarinsa da ta’aliki, sharhi, yin kari a wuraren da bukatar hakan ta taso ta hanyar amfani da nukudodi na ilimi masu amfani da fa’ida wadanda kuma kae amfani da su a wajen yin tafsiri da sauran littafai. Kuma a dan gajeren tunanina mafi girman littafan tafsirai su ne: Al-Mizan da Fi Zilalil Qur'ani domin a kowane dayansu akwai ittijahi kebantacce na tafsiri wanda waninsu bai san shi ba saboda masana ne suka ilmantar da shi.

3- Sanya manhajoji na koyarwa a kan mafahim da ma’anonin Qur'ani, mahangoginsa, nazariyoyinsa, abubuwan da ya tsara da falsafarsa a kan sasanni da rayuwa, bayan dalibi ya gama koyon tafsiri a takaice na lafuzzan Qur'ani a darussan da suka gabata, kuma za a samu wannan ne ta hanyar darastar ayoyin Qur'ani darasi maudu’iy (wato maudu’i maudu’i) ba ta hanyar da aka saba ba a jere a jere, duk da dai cewa ita wannan din ita ce asasi. Kuma lallai na yi mukaranar (kamanta) wadannan manhajojin guda biyu a cikin littafina mai suna (Madkhal ila Tafsiril Qur'an) wanda yake a matsayin mukaddima na wannan bahasin.

         Littafin ya mayar da hankali ne a kan maudu’ai na ilimi ai wadanda suke da rayuwa imma na akida, akhlak ko fikira, a cikinsa alal misali an yi bahasin: Takawa, hakuri, fikihu, tauhidi, imamanci, wilaya, shaidan, da ma’ad (makoma), abubuwan da suke gina al'ummar musulmi da ginata da masu kawo masu cikas, fata da buri, wa’azi da daukar darasi, sunnonin Allah ga al’ummun da suka gabata da sauransu. To daga wannan lokacin ne za a ga canji mai yawa na fikirorinmu, domin ma’anonin da suke yawo a tsakankaninmu a halin yanzu sun saba da ainahin ma’anonin da shi Qur'anin yake nufi bisa ga bibiyar da aka yi, saboda an samu matsaloli masu tarin yawa na tawiloli, tafsirai bisa ra’ayin kashin kai, bin son rai, ta’assubanci da kuma masu yi a kan wata manufa da sauransu.[1] Samahatul shaikh Yakubi ya shigar da wadannan kalmomin (mufradat) cikin tsarin koyarwa na Jami’atul Sadar Al-Diniyya wanda yake dama shi ne shugaban makarantar.