(Hikima) Batacciyar Kayan Mumini / 76

| |times read : 886
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

(Hikima) Batacciyar Kayan Mumini / 76

Samun hikima abu ne mai matukar muhimmanci ga mai neman isa ga kamala a rayuwa da mai kwadayin samun yardar Allah Azza Wa Jalla, abin da aka samu na nassosi dangane da hikima sun ambace ta a matsayin abu mai falala da sharafi kamar yadda aya ta siffanta ta a matsayin alheri mai yawa, {Kuma wanda aka ba shi hikima to lallai ne an ba shi alheri mai yawa} (Suratul Bakara aya ta 269), a saboda haka ne neman hikima na daga cikin siffofin mumini, ba tare da la'akari da daga ina aka cirato hikimar ba, wannan kuma da fadin Amirul Muminina (as) “Ita hikima batacciyar kayan mumini ce, saboda haka ka dauki hikima ko da daga wajen munafiki ta fito”.