Marja'in addini shaikh Yakubi: Tabligi da kira zuwa ga addinin Allah Tabaraka wa Ta'ala sako ne na Annabawa (as),

| |times read : 523
Marja'in addini shaikh Yakubi: Tabligi da kira zuwa ga addinin Allah Tabaraka wa Ta'ala sako ne na Annabawa (as),
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Marja'in addini shaikh Yakubi: Tabligi da kira zuwa ga addinin Allah Tabaraka wa Ta'ala sako ne na Annabawa (as), wanda (a yanzu) hakan ba zai samu ba sai idan Hauzozin ilimi sun tashi da nauyin da ya hau kansu wajen yada ilimi da fadakarwa da basira a tsakanin mutane lungu da sako.

 

DA SUNANSA MADAUKAKI:

(Bayanin Karshe na Ziyarar Arba'in ta Shekarar 1444 AH)

Laraba

3 ga Safar 1444 AH.

Daidai da 31/8/2022 AD.

Marji’in Addini Ayatullahi Yakubi (Allah ya ja kwanansa) ya yi kira a kan muhimmancin kulawa da wajabcin damfaruwa da bangarori guda biyu wadanda ba su bambaruwa da juna kamar yadda ayar ‘Annafar’ mai girma ta yi kira “Saboda haka don mene ne wata jama’a daga kowane bangare daga gare su ba za su fita domin su nemi ilimi ga fahimtar addini kuma domin su yi gargadi ga mutanen su idan sun koma zuwa gare su ba, bisa sa ran gargadin zai ratsa su” (Suratul Tauba: 122), ta hanyar rashin yiwuwar raba tsakanin biyun a kowane irin yanayi, wadannan bangarori guda biyu kuwa su ne neman ilimi da da’awa zuwa ga addinin Allah da tabligin hukunce-hukuncensa.

Kuma samahatul shaikh (Allah ya ja kwanansa) ya nuna rashin jin dadinsa – a yayin da yake magana a ofishinsa a Najaf mai tsarki a gaban wata jama’a daga ma'abota falala da wasu daliban ilimi, kafin su fara hidimar tabligi a wadannan kwanakin na ziyarar Arba’in mai albarka – game da wannan al'adar mai yaduwa a tsakankanin farfajiyar Hauzar ilimi da kuma a tsakankanin da dama daga cikin daliban ilimi a inda suke katange kawukansu ga nauyin farko kurum wanda aya mai girma ta yi kira zuwa gare shi, wato neman ilimi da shagaltuwa da darussa kawai, ba tare da la'akari da daya nauyin ba, wanda shi ne da’awa zuwa ga addinin Allah Ta’ala da tabligin hukunce-hukuncensa da yada akida ta gaskia da wayar da kan mutane da fadakar da su.

Samahatul shaikh (Allah ya ja kwanansa) ya bayyana cewa irin wannan tunani yana nuna gazawar su wajen fahimtar ayar mai girma da kuma nakasu wajen iya dabbaka misdakan ayar a sarari tare da nisantar abin da (Allah da Manzonsa da Imamai (as)) suke son su yi nuni zuwa gare shi kamar yadda ruwayoyi suka zo daga Imaman Ahlul Bait (as), an rawaito hadisi daga Imam Sadik (as) yana cewa: “Lallai irin wadannan majalisosin ina son su, don haka ku raya al'amuranmu, Allah ya ji kan wanda ya raya al'muranmu” (Biharul Anwar, j 44, sh 282 hd 14).

Haka nan ma Al-Harawi ya rawaito daga cikin Uyunu Akhbaril Ridha (as) ya ce: Na ji baban Hasan Ali ibn Musa Al-Ridha (as) yana cewa: Allah ya ji kan bawan da ya raya al'amuranmu, sai na tambaye shi: kamar yaya zai raya al'amuranku? Sai ya ce: “Ya koyi iliminmu ya koyar da mutane, domin idan mutane suka san kyawawan zantukanmu tabbas za su bi mu” (Biharul Anwar, j 2, sh 30, Uyunu Akhbaril Ridha (as)).

Ma'ana dai ta hanyar koyan iliminsu (Salawatullah alaihim) sannan kuma da koyar da shi ga mutane. Wannan kuma yana daga mafi fitowa sarari daga misdakin da ke a karshen ayar “kuma domin su yi gargadi ga mutanen su idan sun koma zuwa gare su, bisa sa ran gargadin zai ratsa su”, to a bisa lura da rashin wadatar wadatuwa da neman ilimi da karatu zalla (don yin hakan kawai kamar an ci rabin hanya ne (sai aka tsaya), wannan kuma ba zai bayar da sakamakon da ake bukata ba sam-sam) madamar ba’a gwama shi da sahihiyar fahimta ba saboda nauyin da yake kanmu a matsayinmu na daliban ilimin (addini), don haka yana da kyau mu yi riko da su mu kama hanyar isa gare su.

Samahatul shaikh ya bayyana cewa lallai shi tabligi sako ne na Annabawa (as) kuma wazifarsu ce: “Wadanda ke isar da sakon Allah, kuma suna tsoronsa, kuma ba su tsoron kowa face Allah, kuma Allah ya isa ya zama mai hisabi” (Suratul Ahzab: 39).

Abin fahimta daga wannan shi ne cewa ya dace ga dalibin ilimi ya yi koyi da su (Imamai (as)) domin samun kwarin gwuiwa da kuma kubuta daga wancan tsukakken tunanin da ya zama abin kwaikwayo ga kowa har aka wayi gari ya zama sananne alhali ba shi da wani asali a shari’a, ba ma haka ba, sam ya ma sabawa sirar Ma'asumai (as) da abin da ya gudana (na rayuwar) da yawa daga cikin malamai masu aiki da iliminsu wadanda suka fadi zantukansu kuma suka tsarkake niyyarsu domin Allah Tabaraka wa Ta'ala kawai, kuma ba su sanya kowa a gabansu ba face Allah Ta'ala, a saboda haka ambaton su ya wanzu a cikin littafai. Kuma duk abin da aka ce ko za a ce domin ganin an raunana daraja da kimar Hauzar ilimi, da nuna jinkirin su wajen sauke nauyin sakon tabligi, wahami ne kawai na daga sauwalawar shaidan: “Kawai wancan shaidan ne yake tsoratar da masoyansa, to kada ku ji tsoransu, ku ji tsoro na idan kun kasance masu imani” (Suratu Aali Imran: 175).

Lallai shaikh ya nuna damuwarsa dangane da wannan halin da yanayi na yaduwar wannan sakafar wadda wasu suke aiki wajen tabbatar da ita ta yadda dalibai masu yawa suke gudanar da ita bai daya ba tare da sun yi tunani a kai ba.

Yayin da shaikh ya yi tambaya cike da mamaki! Shin Manzon Allah (s.a.w.a) bai kasance mai huduba ba? Shin Amirul Muminina (as) bai kasance mai huduba ba? Shin Imam Hasan da Imam Husain (as) ba su kasance masu huduba ba? To me ya sa ake kallon zantukan malami kai tsaye ga al'umma a matsayin gazawa da aibi? Kuma me ya sa al'umma ba ta saurare daga jagoranta kai tsaye ta dauki zance tatacce daga tushensa, alhali a gaba gare mu akwai hadisai masu dimbin yawa daga Amirul Muminina (as). Daga cikin wasiyyoyinsa ga Qusam ibn Abbas gwamnansa a Makka yana cewa: “Kuma kada wani ya kasance wakilinka ga mutane face harshenka (maganarka) da shamaki tsakaninka da su face fuskarka (wato idan talaka ya bukaci ganinka to kar ka sa shamaki a tsakani) (Nahajul Balaga, j 3, sh 127). Wato ma'ana dai mutane su ji daga gare ku kai tsaye ba tare da mai shiga tsakani ya yi magana a madadinku ba, da dai sauran su. Wannan kuma ita ce siyasar Amirul Muminina (as), wannan kuma shi ne ladubban Ma'asumai (as) wanda ya dace a yi koyi da sirarsu da shiryarwarsu da riko da hakan.

Samahatul shaikh (Allah ya ja kwanansa) ya sake jaddada kiransa a kan a amfana da wannan yanayi na ziyarar Arba’in mai albarka wajen yin kira zuwa ga a komawa Allah Tabaraka wa Ta'ala da ilimantar da mutane da shiryar da su da kaucewa duk wani abu da zai haifar da sabani da yankewar zumunci, domin kuwa mutane sun yi ta jiran zuwan wannan ziyara shekara bayan shekara kuma wata dama ce mai girma ga miliyoyin mutane su samu ganawa da dalibai na Hauza ilmiyya su ji daga gare su kai tsaye, kuma su shaidi maukibobi masu wayar da kan jama’a da shiryatar da su, su kuma rayu rayuwa mai dadi mai sa a tuna Allah irin wacce Allah Ta’ala ya karrama uban ‘yantattu da ita (as), domin mutane wadanda a tsawon shekara aka yanke su daga markazozi na addini kasantuwar sun shagaltu da matsalolin rayuwa ta yau da gobe.

Har ila iyau, cikin falalar Ubangiji an wayi gari wannan ziyara mai albarka sannu a hankali ta zama mahada ta babban taron duniya inda al'ummomi daban-daban suke haduwa. Wannan mahada kasuwa ce shahararriya wadda ta dace a yi amfani da ita wajen kira zuwa ga addinin Allah da yada ilimi da fadakarwa, ta hanyar shaidawa da hadisin nan mai daraja da Sayyida Zahra (as) ta rawaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) a yayin da ta ce na ji babana (s.a.w.a) yana cewa: “Lallai malaman ‘yan shi’armu za a tara su, sannan sai a lullube su da haske na karamci daidai gwargwadon yawan iliminsu da himmarsu a cikin shiryatar da bayin Allah, har za ta kai ga an lullube dayansu da dubu sau dubu na haske, sannan mai kira sai ya yi kira Ubangiji madaukaki: ya ku masu rikon marayun iyalan Muhammad (s.a.w.a) masu rainon su yayin rabuwar su da ubanninsu! (Biharul Anwar, j 7, sh 282 hd 225).

Samahatul shaikh ya yi ishara a kan lamurra guda biyu masu muhimmanci wadanda suka zo a cikin hadisin, wadanda su ne sharadin nasara ta hanyar lullubewa da haske na karamci; na dayan su: (yawan iliminsu) sai dai wannan shi kadai din sa ba ya wadatarwa wajen isa ga abin nema, sai dai fa’idarsa kawai za ta iya komawa ga dalibi ne misali, ya wayi gari ya zama (Allama), ko kuma yana ba da karatu mai zurfi kamar (Kifaya da Makasib), kuma dalibai masu yawa su tattaru a gewayensa, duk wannan shi karan kan sa ba ya wadatarwa, madamar sharadi na biyu bai cika ba wanda kuwa shi ne (Himmar su wajen shiryatar da bayin Allah) wannan ko shi ne hadafi mafi muhimmanci da kuma matukar abin nema. To a cikin karshen hadisin mai daraja inda ake cewa: (ya ku masu rikon marayun iyalan Muhammad (s.a.w.a) kuma masu rainon su yayin rabuwar su da ubanninsu; wadanda su ne Imamansu, domin wadannan mutanen marayu sun yanke ne daga ubanninsu na hakika, kuma ba su samu albarkacin damar rayuwa tare da su ba: (a hadisi Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce): “Ya Ali! Ni da kai mu ne ubannin wannan al'ummar” (Biharul Anwar, j 36, sh 282 hd 11).

Daga nan sai samahatul shaikh (Allah ya ja kwanansa) ya fuskanci wannan taron da ya hada ma'abota falala da manyan malamai na Hauza Ilmiyya mai tsarki da jawabinsa yana mai cewa: “Ya ku malamai ku sani ku ne magada Annabawa kamar yadda ya zo a hadisi mai daraja (Malamai magada Annabawa ne), kuma ku din dai ku ne a matsayin ubannin wannan al'umma don haka wadannan mutanen (marayunku ne) kuma suna a karkashin mas’uliyyar ku don haka ku yi gaggawa kada ku noke wajen shiryatar da su da kula da su. Wa ya sani, watakila wasu daga cikin wadannan (marayun) za su tsayar da mu ranar kiyama, su cakumi kwalarmu, su ce ni ne makwabcin ka ko ni ne mai sayar da kayan abinci da ka saba saya a wajen sa ko ni ne direban tasi da ka saba dauka ta haya in kai ka duk inda ka ke so ko kuma ni abokin aikin ku ne a wurin aiki ko kuma ni abokin tafiyar ku ne a tafiyar aikin Hajji, mun kwashi lokaci tare amma ba ka koya min wannan mas’alar ba, ba ka gyara min alwala da sallah ba kuma ba ka shiryar da ni zuwa ga wannan alheri ba kuma ba ka gargade ni a kan wannan sharri ba, kuma ba ka yi min wa’azi ba, da dai sauransu.... Haka dai haka dai, ku ma za ku iya kakkarawa da kan ku.

Shin mutane nawa ne za su tsayar da mu ranar kiyama, kuma lallai za a tambaye mu game da su da kuma game da hakkinsu?  

A karshen jawabinsa, samahatul shaikh ya yi kira ga muballigai a kan ya zamana suna da yalwataccen kirji wajen isar da sakon nan ta yadda za su tantance me ya kamata su fada ga maziyarta bisa la'akari da bambancin kabilarsu da mazhabarsu, gwargwadon yadda yanayi yake hukuntawa da abubuwan da suke kai komo na zamani da sababbin batutuwa da matsaloli na fikira da akida da zamantakewa da aklaq.

Kuma mafi muhimmanci daga wannan shi ne kwadaitar da mutane a game da tsayar da sallar jam’i a dukkan lokutan sallah da yi masu bayanin hukunce-hukuncen shari'a na asasi kamar alwala da sallah da kuma komawa zuwa ga marji’in addini wanda ya cika dukkan sharudda a cikin sauran lamurra, dadi a kan haka kuma yin wa’azi da shiryarwa da fayyace masu abin da zai amfane su dalla-dalla musamman a cikin wannan yanayi na fitintinu da suke ta bijirowa duniyar Musulunci, ta yadda ba za su zama sun fada cikin shubuhohi da zame-zame ba.

Kuma su karanta abin da ya shafi wannan yunkuri na Imam Husain (as) cikin hikima da basira, kamar yadda muke siffanta shi (as) a cikin ziyarar Arba’in da cewa shi: “ya fansar da ransa saboda kai (Allah Ta'ala) domin ya tsamar da bayinka daga duhun jahilci da rudun bata” (Mafatihul Jinan: Ziyarar Arba’in), don ba daidai ba ne mutane su dawo daga ziyararsa (as) amma ba tare da sun dawo da guzuri na tsoron Allah a ransu ba.

Haka nan kuma samahatul shaikh (Allah ya ja kwanansa) ya yi wasicci a kan ambaton Imam Mahdi (as) da bayyana lamarinsa da fadin hanyoyin da za a bi wajen raya ambatonsa da kuma shimfida hanya sahihiya domin warware zarge-zargen da ake jingina masa ta hanyoyi daban-daban.