Hadisai Arba’in Masu Magana A Kan Falala, Tasiri Da Ladubban Tilawa
Hadisai Arba’in Masu Magana A Kan Falala, Tasiri Da Ladubban Tilawa
A nan zan wadatu da ambaton nassosi na hadisai tare da ba su unwani wanda ya dace da abin da suka kunsa, hadisan za su zo ne a jere gwargwadon abin da ke kunshe cikinsu; amma magana kan sharhinsu da yin karin bayani na abubuwan da ke cikinsu na nukudodi to ta yiwu sai a wani mahallin daban, kuma ba ma lallai ne ya zama na iyakance adadi arba’in din ba, domin ruwayoyin da suka kwadaitar a kan haddace hadisai arba’in ba mu fahimci sharadin a’a (wato kar a haura arba’in din) a cikinsu ba, da a ce wani zai yi haddar fiye da arba’in, a saboda haka kenan karin alheri ne.
1- Lizimcin koyonsa
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Ya kamata ga mumini kafin mutuwarsa ta zo ya koyi Qur'ani ko kuma ya kasance yana cikin neman iliminsa”.
Kuma an karbo daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Allah ba zai azabtar da zuciyar da ta farka a sakamakon Qur'ani”.
Kuma an samo daga gare shi (s.a.w.a) ya ce: “Mafificinku wanda ya koyi Qur'ani ya kuma koyar da shi”.
Kuma an samo daga gare shi (s.a.w.a) ya ce: “Madauka Qur'ani a nan duniya su ne masanan a ‘yan aljanna a ranar kiyama”.
Kuma an samo daga gare shi (s.a.w.a) ya ce: “Qur'ani wada ne babu wata wadata koma bayansa kuma babu talauci a bayansa”.
Kuma an samo daga gare shi (s.a.w.a) ya ce: “Idan malami ya cewa karamin yaro: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, sai karamin yaron ma ya ce: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Allah zai wajabta barranta ga yaron, da barranta ga mahaifansa da barranta gas hi malamin nasa”[1].
Kuma an samo daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Hafizin Qur'ani kuma yana mai aiki da shi yana tare da mala’iku marubuta kuma masu daraja da da’a ga Allah”[2].
2- Koyon Qur'ani Shi Ne Mafificiyar Ni’ima
An samo daga Annabi (s.a.w.a) cewa ya ce: “Wanda ya karanta Qur'ani sai ya yi zaton cewa zai yiwu a bai wa wani abin da ya fi wanda aka ba shi, to hakika ya kaskantar da abin da Allah ya girmama, ya kuma girmama abin da Allah ya kaskanta”[3].
3- Qur'ani Shi Da Kansa Ceto Ne Kuma Mai Yin Ceto, Kuma Mai Jayayya Ne Da Gaskiya
An karbo daga Manzo (s.a.w.a) ya fada a cikin wani hadisi cewa: “Idan fitina ta rincabe maku kamar wani yankin dare mai duhu to ina horonku da Qur'ani domin shi da kansa ceto ne kuma mai yin ceto kuma jayayya ne da gaskiya, kuma wanda ya saka shi a gabansa to zai ja shi zuwa aljanna, wanda kuma ya sanya shi a bayansa zai kora shi zuwa wuta, kuma shi dalili ne da yake nuni ga hanyar da ta fi, kuma shi littafi ne a cikinsa akwai bayani dalla-dalla da bayani ain nema – har zuwa inda ya ce – abubuwan mamakinsa ba su lissafuwa kuma gano sababbin abubuwa a cikinsa ba su tsufa, shi fitulu ne na shiriya kuma haske ne na hikima”[4].
4- Siffar makarancin Qur'ani
An karbo daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Ya kamata ga makarancin Qur'ani idan ya zo ga ayar da a cikinta akwai tsoratarwa to a daidai wajen ya tsaya roki tsari daga azabar wuta da sauran bukatu”[5].
Kuma an karbo daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ni ina mamakin yadda idan ina karanta Qur'ani ba ni yin furfura”[6], daga cikin hudubar Amirul Muminina (as) yana siffanta muttakin da cewa: “Amma da daddare suna tsaye a kan duga-dugansu suna sallar dare, suna masu tilawar wani yanki na Littafi, suna jeranta karanta shi a hankali jerantawa da tadabburi, ayoyinsa suna sanya su shiga cikin halin tsoro da damuwa a kan kawukansu tare da tasirantuwa da shi saboda halin damuwa da suke ciki, suna masu kuka saboda zunubansu, idan suka zo ga ayar da a cikinta akwai tsoratarwa a kan azaba sai gabaki dayan hankalinsu ya koma jikinsu, zukatansu suna raurawa sai su shiga cikin zurfin tunani wanda za su dinga hakaito wa a ransu kamar gasu nan suna ji da kunnuwansu ana kara rura wutar azaba ga ‘yan wuta a can cikin jahannama, idan kuma suka hadu da ayar da akwai kadaitarwa a cikinta, sai wani dadi ya kama su, su kara sanya natsuwa da shaukin karantawa su dinga jin wannan busharar a matsayin sanyin idanunsu kamar don su aka yi”[7].
5- Wajabcin Girmama Mahaddatan Qur'ani Da Kuma Haramcin Wulakanta Su
An samu daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Lallai ma’abota Qur'ani suna cikin wata daraja madaukakiya daga ‘yan adam in ka cire Annabawa da Manzanni, saboda haka kada ku raunanar da hakkokin ma’abota Qur'ani, domin hakika su a wurin Allah suna da wani matsayi”[8].
6- Ladar Wanda Koyon Qur'ani Da Haddarsa Suke Yi Masa Wahala
An karbo daga Imam Sadik (as) ya ce: “Wanda Qur'ani ya yi masa wahala da tsananin ganewa yana da lada biyu, wanda kuma ya saukaka a gare shi to yana daga cikin mutanen farko”[9].
Kuma daga gare shi (as) ya ce: “Wanda yake karatun Qur'ani kuma yake shan wahala wajen haddarsa haka kuma yake da karancin haddarsa, yana da lada biyu”[10].
7- Wajabcin Karanta Basmala Kafin Fara Karatun Sura
An karbo daga Imam Sadik (as) ya ce: “Idan mutum ya ja jama’a sallar jam’i, sai wani shaidani ya zo gurin shaidanin da yake kusa da limamin sannan sai ya ce: Shin ya ambaci sunan Allah kuwa ya’ani ya karanta: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai (bismillah….) kuwa? To idan ya amsa masa eh, sai ya gudu, idan kuma ya ce masa a’a, sai shaidan yah au wuyan limamin ya zuro kafafunsa a kan kirjinsa, shaidan ba zai gushe a haka ba har sai mutanen nan sun idar da sallarsu”[11].
8- Mustahabbi Ne Karanta Qur'ani A Yayin Ziyarar Kaburbura
Ya zo a cikin (Man La Yahduruhul Fakihi) daga Imam Ridha (as): “Babu wani bawa mumini da zai ziyarci kabarin mumini sannan ya karanta masa Inna anzalnahu fi lailatil kadri kafa uku face Allah ya gafarta masa shi da wanda ke cikin kabarin”[12].
A wata ruwayar kuma: “Aminci ne daga firgitar nan mafi girma”, amma game da ma’anarsa akwai ruwayoyi masu yawa.
A wata ruwayar daban kuma, mustahabbi ne a kara suratul Fatiha da Kula’uzai da Kul huwallahu da ayatul Kursi kafa uku-uku kowaccensu, batun ladarsu ya zo a ruwaya: “Lallai Allah zai aika masa mala’ika ya dinga bautar Allah a wurin kabarin nasa kuma ya rubuta masa shi da mamacin ladar abin da wannan mala’ikan yake yi, kuma idan Allah ya tashe shi daga kabarinsa babu wani wuri mai wahala da zai wuce face Allah ya katange shi daga wannan wuyar ta hanyar wannan mala’ikan wanda aka wakilta masa har Allah ya shigar da shi aljanna”[13].
9- Falalar Koyon Qur'ani Tun Cikin Kuruciya Da Tasirinsa
An karbo daga Sadik (as) ya ce: “Wanda ya karanta Qur'ani alhali shi matashi ne mumini, Allah zai cakuda Qur'anin da jinin jikinsa da tsokarsa, kuma Allah zai sanya shi cikin jerin mala’iku marubuta kuma masu daraja da da’a ga Allah, kuma Qur'ani zai kasance mai ba da kariya a gare shi ranar kiyama, (sannan Qur'anin) zai ce: Ya Ubangiji dukkan wani ma’aikaci an ba shi ladar aikinsa, banda wanda ya yi aiki da ni, to ina rokon ka ba shi mafi girman karamcinka. Ya ce: Sai Allah mabuwayi da daukaka ya saka masa wasu tufafi na musamman na aljanna sannan ya dora masa wani kambu a kansa na karamci, sannan sai ya ce: Shin mun gamsar da kai game da lamarinsa? Sai Qur'ani ya ce: Ya Ubangiji lallai na yi fatan a yi masa fiye da haka, sai ya ce: To sai a ba shi aminci a damarsa da dawwama a hagunsa sannan sai ya shiga aljanna ana mai ce masa: Karanta (aya daga cikin ayoyi) darajarka da daukakarka su kara dagawa sama. Sannan sai a ce wa Qur'ani shin mun gamsar da kai game da lamarinsa? Sai Qur'ani ya ce: Eh na gamsu[14].
10- Lizimcin koyar da yara karatun Qur'ani
An karbo daga Manzon Allah (s.a.w.a) a cikin wani hadisi zuwa inda ya ce: “Zai tufatar da iyayensa biyu, uwarsa da ubansa – wato ainahin yaro makarancin Qur'ani – wasu nau’oi na tufafi na musamman guda biyu (na aljanna) in dai sun kasance muminai, sannan a ce masu wannan sakamakon koyar da shi Qur'ani da kuka yi masa ne”[15], akwai kuma wani hadisi daga Amirul Muminina (as) ya ce: “Hakika Allah zai himmantu cikin azabtar da ma’abota kasa gabaki dayansu ba tare da ya ware ko mutum daya daga cikinsu ba idan suka aikata sabo suka yi gigin aika munanan halaye, amma yayin da ya yi duba ga dattawa sun tsayu da kafafunsu suna ta sallah da kuma yara suna koyon Qur'ani sai ya yi masu rahama ya jinkirta masu wannan azabar”[16].
11- Kashe-Kashen Makarantan Qur'ani Da Siffar Makaranci Na Gaskiya
An karbo daga baban Ja’afar (as) ya ce: : “Makaranta Qur'ani kashi uku ne: Mutumin da ya karanta Qur'ani amma sai ya dauke shi haja ya kewaya da shi a fadar masu mulki, ya tsananta shi a kan jama’a, to wannan yana daga cikin ‘yan wuta, wani mutumin kuma ya karanta Qur'ani ya haddace haruffansa amma ya keta dokokinsa[17], ya mayar da shi abin amfani tamkar tukunya a gare shi, kada Allah ya yawaita irin wadannan daga cikin ma’abota Qur'ani, wani mutumin kuma ya karanta Qur'ani sai ya sanya Qur'anin a matsayin maganin da yake warkar da rashin lafiyar zuciyarsa, ya dinga kebencewa da shi yana karar da darensa cikin karanta shi, yana kosar da kishinsa da shi a yininsa, yana tsayar da shi a masallatai kuma sasanninsa suna nisanta daga shimfidun kwanciya domin karanta shi, to da irin wadannan ne Allah yake kare bala’oi da kuma irin su ne yake ba da nasara a kan makiya – wato yana taimaka masu ya dora su a kan makiyansu – kuma da irin su ne yake saukar da ruwan sama. Na rantse da Allah wadannan makaranta Qur'anin sun fi kibritil ahmar[18] kima da daraja”[19].
Kuma an samu daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ya kai mahaddacin Qur'an ka yi tawali’u da shi, sai Allah ya daukaka ka, kada ka yi dagawa da shi, sai Allah ya kaskantar da kai, ya kai mahaddacin Qur'ani ka yi kawa da shi domin Allah, sai Allah ya kawata ka da shi, kada ka yi kawa da shi domin mutane, sai Allah ya munanantar da kai da shi”[20].
12- Fahimtar Qur'ani Wata Martaba Ce Da Take Da Kusanci Ga Annabta
An karbo daga Manzon Allah (s.a.w.a) a wani hadisi ya ce: “Wanda ya yi saukar Qur'ani abin sani kawai shi ne za a sanya Annabta a tsakanin goshinsa sai dai kawai shi ba a yi masa wahayi”[21].
13- Mafi Kamalar Hanya Ta Saukar Qur'ani Ita Ce Ka Faro Shi Daga Surar Farko Zuwa Karshensa, Ba Kawai Ka Dinga Karanta Surori A Warwatse Ba
An karbo daga Zuhri ya ce: “Na cewa Ali dan Husain (as): Wane aiki ne mafifici? Sai ya ce: “Alhalul murtahilu”, Sai na ce: Mene ne alhalul murtahilu? Sai Imam (as) ya ce: Faro karatun Qur'ani tun daga farkonsa ana binsa sura bayan sura har zuwa surar karshe, kenan an yi sauka daya, sannan kuma sai a sake faro karatun tun daga farko haka dai haka dai”[22], kuma a cikin Al-Nihaya an tambaye shi: Wane aiki ne mafifici? Sai ya ce: “Alhalul murtahilu, sai aka ce: Me wannan ke nufi? Sai ya ce: Mai farawa da zarar ya kammala sauka, shi ne wanda yake kammala tilawar Qur'ani sannan ya sake farowa daga farkonsa; sai ya kamanta shi da matafiyi wanda zai isa gida sannan ba tare da ya huta ko kadan a cikinsa ba sai ya sake wata haramar sabuwar fita, haka kuma yanayin karatun mutanen Makka yake idan suka kammala saukar Qur'ani ta hanyar tilawa, sai su faro sabon karatu daga kan suratul Fatiha hade da aya biyar daga suratul Bakara daga farkon surar zuwa fadin Allah: (Humul muflihuna = Kuma wadannan su ne masu cin nasara”, sai su tsaya a nan. To kuma suna kiran wanda ya aikata wannan da sunan alhalul murtahilu da ma’anar cewa wanda ya kammala saukar Qur'ani sannan ya faro shi daga farkonsa ba tare da ya rarraba tsakanin saukar da wani lokaci daban ba.
Akwai wani hadisi daga Imam Sadik (as) wanda yake dauke da irin wannan ma’anar; an tambaye shi: Ya dan Manzon Allah wadanne mutane ne suka fi, sai ya ce: “Alhalul murtahilu, sai aka ce masa: Ya dan Manzon Allah (s.a.w.a) mene ne kuma alhalul murtahilu? Sai Imam (as) ya ce: Mai farawa da zarar ya kammala, mutumin nan da yake karanta Qur'ani har ya sauke shi, to shi wannan addu’arsa a wurin Allah karbabbiya ce”[23].
14- Wasici Da Yawaita Karatun Qur'ani
Kuma daga cikin wasiyyar Annabi (s.a.w.a) ga Ali (as) ya ce: “Na hore ka da yin tilawar Qur'ani a kowane hali ka samu kanka”[24].
15- Ladar Karanta Qur'ani
An karbo daga Imam Sadik (as) a cikin wani hadisi ya ce: “Na hore ku da karanta Qur'ani domin darajojin aljanna suna samuwa ne daidai da adadin ayoyin Qur'ani, to idan kiyama ta tsaya za a ce da makarancin Qur'ani: Karanta (aya daga cikin ayoyi) darajarka da daukakarka su kara dagawa sama, to kuma duk lokacin da ya karanta to darajarsa za ta kara yin sama”[25].
Kuma an karbo daga baban Ja’afar (as) ya ce: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Wanda ya karanta aya goma a cikin dare, ba za a rubuta shi cikin gafalallu ba, wanda kuma ya karanta aya hamsin, za a rubuta shi cikin masu zikiri, wanda kuma ya karanta aya dari, za a rubuta shi cikin masu kankan da kai, wanda kuma ya karanta aya dari biyu, za a rubuta shi cikin masu tsoron Allah, wanda kuma ya karanta aya dari uku, za a rubuta shi cikin masu babban rabo, wanda kuma ya karanta aya dari biyar, za a rubuta shi cikin mujahidai, wanda kuma ya karanta aya dubu, za a rubuta masa kindari, shi kuwa kindari daidai yake da miskali dubu goma sha biyar (‘a wani kaulin’ dubu hamsin) na zinari, shi kuma miskali kiradi dubu 24 ne wanda mafi karancinsu shi ne kwatankwacin dutsen Uhudu, mafi girmansu kuma girmansa ya kai tsakanin sama da kasa”[26].
16- Lizimcin kiyaye abin da aka haddace daga Qur'ani da rashin gangancin barinsa a manta da shi.
Daga Yakub Al-Ahmar ya ce: Na cewa Abu Abdillah (as): Ina fama da bashi mai yawa har ta kai ga ina manta haddata ta Qur'ani. Sai Abu Abdillah (as) ya ce: “Shi Qur'ani Qur'ani ne, kuma lallai aya daga Qur'ani da kuma sura za su zo a ranar kiyama darajarsu za ta kai ninki dubu – wato a aljanna – sai suce: “Da ka haddace mu da mun kai ka zuwa ga waccan darajar”[27].
Ina cewa: Ya riga ya gabata gare ka cewa, lallai haddar Qur'ani mai ma’ana tana nufin kiyaye dokokinsa da koyarwarsa da kuma lazimtuwa da umarninsa da haninsa.
17- Mustahabbi Ne Yin Alwala Yayin Tilawarsa (Qur'ani)
Daga Muhammad dan Fudail daga Abul Hasan (as) ya ce: Na tambaye shi cewa idan ina cikin karanta Qur'ani sai fitsari ya kamani, sai in tafi in yi, sannan sai in kama ruwa in kuma wanke hannuna, sannan sai in dawo ga Mus’hafi in ci gaba da karantawa. Sai ya ce: A’a ka yi alwala kaga har sallah ka yi da ita”[28].
An kuma karbo daga gare shi (as): “Akwai lada dari ga makarancin Qur'ani a kowane harafi da ya karanta a cikin sallah alhalin yana tsaye, idan yana zaune kuma yana da lada hamsin, idan yana da alwala amma ba a cikin sallah ba lada ashirin da biyar, amma idan ba shi da alwala to lada goma, kuma ni ba ina ina mai fadin cewa: (wanda ya karanta) Alif, Lam, Mim, Ra (المر), lada goma za a ba shi a’a, duk harafi yana da lada goma misali Alif lada goma, Lam lada goma, Mim lada goma, Ra lada goma”[29].
18- Mustahabbi Ne Yin A’uzu Yayin Karatunsa (Qur'ani)
Daga Halabi, daga Abu Abdillah (as) ya ce: Na tambaye shi game da neman tsari daga shaidan a yayin fara karanta kowace sura, sai ya ce: Eh, ka nemi tsari ga Allah daga shaidan jefaffe”[30].
Kuma an samo daga Amirul Muminina (as): “Neman tsari abu ne da Allah ya yi umarni da shi ga bayinsa a yayin da za su karanta Qur'ani da fadinsa: “Sannan idan za ka karanta Qur'ani, sai ka nemi tsari ga Allah daga shaidan jefaffe” (Nahli: 98), kuma duk wanda ya ladabtar da kansa da ladubba irin na Allah, to Allah zai tabbatar da shi a kan dacewa mai dorewa”[31].
19- Qur'ani alkawarin Allah ne, Sau Nawa Ya Kamata Mumini Ya Karanta A Kullum
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Qur'ani alkawarin Allah ne ga bayinsa, don haka lallai ya kamata ga mutum musulmi ya dinga duba zuwa ga alkawarinsa kuma ya karanta aya hamsin daga gare shi a kullu yaumin”.[32]
Na ce: A bisa lissafi sassauka mafi karancin abin da mumini zai yi shi ne ya sauke Qur'ani sau uku a shekara, domin adadin ayoyin Qur'ani sun kai sama da dubu sittin a saboda haka zai iya yin saukar a cikin kwana (120) watau wata hudu, wannan ba tare da an yi la'akari da rubanya himma da ake sa ran a yi a watan Ramadan ba.
20- Ayoyin Qur'ani Taskoki Ne, Zai Yi Kyau A Amfana Da Su Gabaki Dayansu
Daga Ali dan Husain (as) ya ce: “Ayoyin Qur'ani taskoki ne, saboda haka duk lokacin da ka bude taska, to yana da kyau ka yi duba na musamman a cikinta”[33].
21- Mustahabbi Ne Karanta Qur'ani A Cikin Gidaje
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Gidan da ake karanta Qur'ani kuma ake ambaton Allah Azza wa Jalla a cikinsa, to albarkar tana yawaita a cikinsa kuma mala’iku suna halartarsa, shaidanu kuma suna nisantarsa, kuma haskensa yana haskaka ma’abota sama kamar yadda taurari suke haskaka mutanen sama, kuma lallai gidan da ba’a karanta Qur'ani a cikinsa kuma ba’a ambaton Allah, to albarkar cikinsa za ta ragu, kuma mala’iku za su kauracewa masa, kuma shaidanu za su hallara a cikinsa”[34].
22- Kasantuwanci da neman arziki ba su hana dogewa ga karanta Qur'ani
Daga Abi Abdillah (as) ya ce: “Babu abin da zai hana dan kasuwa wanda ya shagaltu da harkokinsa na kasuwa daga cikinku idan ya dawo gidansa kafin ya kwanta bacci ya karanta wani abu daga Qur'ani, za a rubuta masa lada goma a madadin duk ayar da ya karanta kuma za a kankare masa zubbai goma”[35].
23- Koda Mutum Mahaddaci Ne To Mustahabbi Ne Ya Karanta Daga Mus’hafi
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Wanda ya karanta Qur'ani daga mus’hafinsa zai samu walwala ga idanunsa, kuma za a saukakawa mahaifansa (azabar kabari) koda sun kasance kafirai ne”[36].
Kuma an samo daga Annabi (s.a.w.a) ya ce: “Babu wani abu mafi tsanani ga shaidan kamar karanta Qur'ani ana kallon bakin ana karantawa”[37].
A wani hadisin kuma: “Kawai duba ga mus’hafi ba tare da ma ko karanta shi ba ibada ce”[38].
Na ce: Wannan dai shi ne mafi karancin nauyin da ya hau kan wanda bai iya karatu bay a bude Qur'ani ya kalli bakinsa, to sai dai kuma zai iya saurarar kira’a (ta hanyar jin sauti).
An kuma karbo daga Is’hak dan Ammar daga Abu Abdillah (as) ya ce: Na tambaye shi: Raina fansa ne gare ka, ni mahaddacin Qur'ani ne, to shin in karanto shi da ka shi ne ya fi ko in duba baki? Sai ya ce mani: Ka karanta shi kana mai duba bakinsa ya fi falala, shin ba ka san kallon bakin Qur'ani ibada ba ce ba”[39].
24- Mustahabbi Ne Ajiye Qur'ani A Gida A Matsayin Mai Ba Da Kariya
Daga Imam Sadik (as) ya ce: “Lallai abin burgewa ne yadda Allah yake wurgar da shaidanu daga duk gidan da ya kasance akwai Qur'ani”[40].
25- Mustahabbi Ne Karanta Shi Daki-Daki, Yayin Da Gaggautawa Take Makaruhi
Daga Abdullah dan Sulaiman ya ce: Na tambayi Aba Abdillah (as) game da fadin Allah Azza wa Jalla: “Kuma ka kyautata karanta Qur'ani daki-daki”, sai ya ce: “Amirul Muminina (as) ya ce: Littafi ne da ya bayyana shi a matsayin mai yin bayani ga dukkan komai, kuma kada ku mayar da shi kamar waka mai dango-dango, kuma kada ku warwatsar da shi kamar turbaya, sai dai shi yana ratsa kekasassun zukatanku, kuma kada dayanku ya mayar da hadafinsa shi ne ya ga ya kai karshen sura”[41].
A cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala: “Wadanda muka bai wa Littafi suna karatunsa hakikanin karatunsa”, an rawaito daga Imam Sadik (as) ya fadi cewa: “Hakikanin karatunsa wato tsayawa a wajen da aka ambaci aljanna da wuta, zai roki ta farko, ya kuma nemi tsari daga ta biyu”[42].
A wani hadisin kuma daga Imam Sadik (as) din dai ya zo cewa: “Lallai Qur'ani ba’a karanta shi haka kawai ba tsari, a’a, sai dai ana karanta shi ne daki-daki, kuma idan aka biyo ta kan ayar da a cikinta aka ambaci aljanna sai a tsaya a roki Allah aljannar, kuma idan aka biyo ta ayar da aka ambaci wuta sai a tsaya a nemi tsarin Allah daga azabar wuta”[43].
26- Mustahabbi ne karanta shi cikin jimami ka ji kamar yana magana da kai ne kai tsaye, sannan haramun ne shidewa da sumewa kamar yadda wasu sufaye suke yi
Daga Imam Sadik (as) ya ce: “Lallai Qur'ani ya sauka da jimami don haka ku karanta shi cike da jimami”[44].
Daga Hafsin ya ce: Ban ga wani mutum da ya fi Musa dan Ja’afar (as) tsoron (Allah) ba, kuma babu wani daga cikin mutane da ya fi shi fata, kuma karatunsa ya kasance cike da jimami, idan yana karantawa kai ka ce yana magana da wani mutum ne”[45].
Daga Jabir daga Abu Ja’afar (as) ya ce: “Na ce akwai wasu jama’a idan suka ambaci wani abu daga littafi ko suka yi hirarsa sai dayansu ya suma har ta kai ga da za a datse hannunsa ko kafarsa ba zai ji ba. Sai Imam ya ce: Subhanallah! Wannan daga shaidan ne, mene ne wannan suke siffantuwa da shi! Shi ba wani abu ba ne face mai sanya tausasawa, saukakawa, saurin yin hawaye da sanya zukata su firgita”[46].
27- Mustahabbi ne karanta Qur'ani da sauki mai karfi
Daga Mu’awiya dan Ammar ya ce: “Na cewa Abu Abdillah (as): Wani mutum ne shi ba ya ganin ya yi wata addu’a ko karatun Qur'ani madamar bai daga sautinsa ba. Sai ya ce: Babu laifi, lallai Ali dan Husain (as) ya kasance mafi kyawon mutane sauti a karatun Qur'ani kuma ya kasance yana daga sautinsa har mutane cikin gidansa suna jinsa, kuma Abu Ja’afar (as) ya kasance mafi kyawon mutane sauti a karatun Qur'ani, kuma ya kasance idan ya mike zai yi sallar dare yana daga sautinsa hatta mai wucewa a kan hanya na daga masu ban ruwa da sauransu suna tsayawa suna sauraren karatunsa”[47].
28- Haramcin rera karatun Qur'ani (kamar ana rera waka)
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ku karanta Qur'ani da muryar larabawa da kuma sautinsu, kuma na hane ku yin amfani da muryoyin mutane fasikai da masu girman kai, domin kuwa a bayana wasu jama’a za su zo wadanda za su dinga rera Qur'ani kamar yadda ake rera waka, jan karatun tare da lankwaya shi, ba ya ketare makogwaronsu kuma zukatansu a juye suke da zukatan wanda duk karatun nasu ya burge shi”[48].
29- Wajibi ne bisa kyautatawa saurarar karatun Qur'ani amma a shari'a mustahabbi ne sai dai idan a sallah ne
Daga Abdullah dan Abu Ya’afur daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Na ce masa mutum ne yana karanta Qur'ani, shin wajibi ne ga wanda yake jinsa ya kame bakinsa ya saurare shi? Sai ya ce: Eh, idan ana karanta Qur'ani a inda kake wajibi ne ka kame bakinka ka saurara”[49].
A cikin hadisin Zurara daga baban Ja’afar (as) ya ce: “Idan ana karanta Qur'ani a cikin sallar farilla alhali kuna bayan liman, to ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru, tsammaninku a yi muku rahama”[50].
30- Mustahabbi ne saukar Qur'ani sau daya a kowane wata
Daga Muhammad dan Abdullah ya ce: Na cewa Abu Abdillah (as): Zan iya karanta Qur'ani da daddare? Sai ya ce: Ba zai ba ni mamaki idan ka karance shi a kasa da wata guda ba”[51].
31- Mustahabbi ne yin kyautar ladar karatun Qur'ani ga Ma’asumai (as) domin samun rubanyar lada
Daga Ali dan Mugira daga Abu Hasan (as): Na ce masa idan a ranar idin karamar sallah na yi sauka sai na bai wa Manzon Allah (s.a.w.a) kyautar ladar[52], a wata ranar kuma sai na ba Ali (as), a wata ranar kuma Fatima (as) sannan na dinga ba Imamai (as) har na iso gare ka, na ba ka kyautar daya tun daga farawata zuwa yanzu, to ko wani abu zai yi saura gare ni? Ya ce: Ai a albarkacin wannan za ka kasance tare da su ranar alkiyama, sai na ce: Allahu akbar! Yanzu ni ke duk wannan haka? Sai ya ce: Eh, kwarai kuwa har sau uku”[53].
32- Mustahabbi ne yin kuka ko yunkurin yin kuka a yayin sauraron Qur'ani
Daga Imam Sadik (as) ya ce: “Lallai Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo gurin wani matashi daga Ansar ya ce: Ni ina son zan karanta gare ku to duk wanda ya yi kuka yana da aljanna, sai ya karanta karshen surar Zumar: “Kuma aka kora wadanda suka kafirta zuwa jahannama jama’a-jama’a” zuwa karshen sura, sai mutanen Ansar gabaki dayansu suka yi kuka face wancan matashin; sai ya ce: Ya Manzon Allah hakika na yi yunkurin kuka amma idanuna sun ki zubar da hawaye, sai ya ce: Zan sake maimaita karanta maku, duk wanda ya yi yunkurin kokawa to zai samu aljanna, sai ya sake karanta masu, sai gaba dayan mutanen suka yi kuka amma shi yaron yunkurin kuka kawai ya yi sai gabaki dayansu suka shiga aljanna”[54].
33- Dukkan Ilimi yana cikin Qur'ani
An rawaito daga Ali (as) cewa an ce masa: Shin kuna da wani abu daga wahayi? Sai ya ce: A’a, ina rantsuwa da wanda ya yi halitta sai dai idan Allah ne ya ba wani bawa fahimta ta Littafinsa”[55].
Kuma an samo daga Ibrahim dan Abbas ya ce: “Ban taba ganin an tambayi Ridha (as) wata tambaya ba face ya santa, kuma ban ga wani wanda ya fi shi ilimi ba tun daga zamanin farko har zuwa lokacinsa da zamaninsa, kuma Ma’amun ya kasance yana yawan jaraba shi da tambayoyi game da komai da komai sai kuma ya ba shi amsarsu, kuma maganganunsa da jawabansa gabaki dayansu suna zuwa ne daga Qur'ani”[56].
Ya zo a cikin Nahajul Balaga: “Wannan Qur'anin idan kuka nemi ya yi magana ba zai yi magana ba, amma ni zan ba ku labara game da shi: Ku saurara! Lallai a cikinsa akwai ilimin abin da zai zo, da labarin abin da ya gabata, da maganin cutukanku da gyara ko daidaita tsakankaninku”[57].
34- Qur'ani waraka ne daga dukkan ciwo
Daga Abu Abdillah (as) ya ce: “Da za ka karanta alhamdu ga mamaci sau saba’in, sannan a dawo masa da ransa wannan ba zai zama abin al’ajabi ba”[58].
35- Qur'ani hasken zuciya ne
Daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Hakika wannan zuciyar tana yin tsatsa kamar yadda karfe yake yi, amma hakika abin da yake haskakata shi ne karatun Qur'ani”[59].
36- Yawaita karanta shi a cikin watan Ramadan
Daga Abu Ja’afar (as) ya ce: “Kowane abu yana da kaka, kuma ita kakar Qur'ani watan Ramadan ce”[60].
An karbo daga Ali dan Hamza ya ce: “Na shiga wurin Abu Abdillah (as) sai Abu Basir yace masa: Raina fansa gare ka, shin in dinga saukar Qur'ani a kowane dare a watan Ramadan? Sai ya ce: A’a, a dare biyu fa? Ya ce: A’a, ya ce: A dare uku fa? Sai ya ce: Wannan, sannan ya yi nuni da hannunsa sannan ya ce: Ya Aba Muhammad, lallai watan Ramadan yana da wani hakki kuma kimarsa bata misaltuwa da sauran watanni”[61].
A cikin wata hudubar Annabi (s.a.w.a) a Juma’ar karshe ta watan Sha’aban ya ce: “Wanda ya karanta daga cikinsa – ai cikin watan Ramadan – wata aya daga Qur'ani za a ba shi ladar saukar Qur'ani a waninsa daga cikin watanni”[62].
37- Tilawar Qur'ani hakikanin tilawarsa
A cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala: “Wadanda muka bai wa Littafi suna karatunsa hakikanin karatunsa” Bakara: 121, Imam Sadik (as) ya ce: “Suna karanta ayoyinsa, kuma suna fahimtarsa, kuma suna aiki da hukunce-hukuncensa, kuma suna kwadayin alkawuransa, kuma suna tsoron horonsa, kuma suna fa’idantuwa da kissoshinsa, kuma suna horo da umarninsa, kuma suna yin hani ga abubuwan da ya hana. Wallahi ba wai kawai haddace ayoyinsa, sanin haruffansa, tilawar surorinsa da koyar da ushurinsa da khumusinsa ba ne ba. Sun haddace haruffansa, sai dai sun keta iyakokinsa, alhali shi abin da ake so shi ne ayi tadabburin ayoyinsa da aiki da hukunce-hukuncensa Allah ya ce: “Littafi ne, mun saukar da shi a gare ka mai albarka, domin suyi taddaburi a cikin ayoyinsa” (Sad: 29)[63].
38- Malamai ba su koshi daga Qur'ani
Daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya fada a cikin wani hadisi yayin da yake siffanta Qur'ani: “Shi igiyar Allah ce mikakkiya, kuma ambato ne mai hikima, kuma hanya ce madaidaiciya, kuma son rai ba ya karkata zuwa gare shi, kuma malamai ba su koshi da shi, kuma harsuna ba su rikice masa, kuma yawan karanta shi ba ya sa shi tsufa, kuma abubuwan ban al’ajabinsa ba su yankewa, wanda ya fada daga gare shi ya yi gaskia, wanda ya yi hukunci da shi ya yi adalci, kuma wanda ya yi aiki da shi za a ba shi lada kuma wanda ya yi kira zuwa gare shi zai shiriya zuwa ga hanya madaidaiciya”[64].
39- Qur'ani a cikin Nahajul Balagha
“Ku koyi Qur'ani domin shi ne mafi kyawun zance, ku yi tafakkuhi a cikinsa domin shi dausayin zukata ne, ku nemi waraka daga haskensa domin shi waraka ne ga kiraza, ku kyautata tilawarsa domin shi ne mafi amfanin kissoshi, kuma lallai duk mai aiki ba da iliminsa ba daidai yake da rudadden jahili wanda ba ya farkawa daga jahilcinsa, a’a sai dai ma hujja mai girma da za ta kasance a kansa kuma an lizimta masa yin asara kuma shi a wajen Allah abin zargi ne”[65].
40- Addu’ar Imam Sajjad (as) a yayin saukar Qur'ani
Ya Allah lallai kai ka tallafa mani wajen yin saukar Littafinka wanda ka saukar da shi a matsayin haske, kuma ka sanya shi mai yin rinjaye a kan dukkan littafan da ka aiko, kuma ka fifita shi a kan dukkan labarin da ka bayar, mai rarrabewa ne tsakanin halal da haram, kuma ka sanya shi abin karantawa mai bayani a kan shari’oinka da hukunce-hukuncenka, kuma Littafi ne da ka bayyana shi ga bayinka daki-daki, kuma wahayi ne da ka saukar da shi dalla-dalla ga Annabinka Muhammad salatinka a gare shi da Iyalansa, kuma ka sanya shi haske wanda muke shiryuwa da shi daga duhun bata da jahilci ta hanyar biyayya gare shi, kuma waraka ga wanda ya saurare shi da fahimta ta gaskatawa, kuma ka sanya shi ma’auni na adalci ba ya karkata daga furta gaskiya, kuma ka sanya shi hasken shiriyar da ba ya mutuwa ga wanda ya shaidi hujjojinsa, kuma alami na tsira ba ya batar da duk wanda ya yi aniyar raya sunnarsa, kuma wanda ya yi riko da shi ba ya halaka. Ya Ubangiji idan ka taimaka mana muka yi tilawarsa, kuma ka kwance duk wani kulli daga harsunanmu da ibarorinsa kyawawa, to ka sanya mu cikin masu kiyaye shi hakikanin kiyayewa, masu addinantuwa gare ka da akidar sallamawa ga hukunce-hukuncen ayoyinsa, kuma ka taimaka mana wajen sallamawa da yin ikirari ga ayoyinka mutashabihai da wadanda aka bayyana su dalla-dalla. Ya Ubangiji lallai ka saukar da shi ga Annabinka Muhammad (s.a.w.a) a dunkule, kuma ka yi masa ilhamar ilimin abubuwan al’ajabinsa kammalallu, kuma ka gadar mana ilimin tafsirinsa kuma ka daukaka mu a kan wanda ya jahilci iliminsa, kuma ka karfafe mu domin daukaka mun da ka yi a kan wanda ba zai iya jurewa daukarsa ba. Ya Ubangiji kamar yadda ka sanya zukatanmu gurin daukarsa kuma ka sanar da mu da rahamarka daukakarsa da falalarsa, ka yi salati ga Muhammad wanda yake magantuwa da Qur'ani, da alayensa taskokin iliminsa, kuma ka saka mu cikin wadanda suka yi ikirari da cewa tabbas daga gare ka yake, don kada shakka ta bijiro gare mu cikin gaskata shi, kuma kada zamiya ta same mu daga kan hanyarsa. Ya Ubangiji ka yi salatinka ga Muhammad da alayensa, ka sanya mu cikin wadanda suka yi riko da igiyarsa, kuma wadanda ka kiyaye daga fadawa cikin rudu game da ayoyinsa mutashabihai, ka sanya mu cikin mazauna inuwar shiriyarsa, kuma masu shiryuwa da hasken safiyarsa, masu bin hanyarsa mai haskawa, masu haskakuwa da fitilarsa wadanda ba su neman wata shiriya daga waninsa. Ya Ubangiji kamar yadda ka sanya Muhammad (s.a.w.a) alami wanda zai shiryar da mutane zuwa gare ka, kuma ka sanya alayensa a matsayin hanyar isa zuwa ga yardarka da amincinka, to ka yi salati ga Muhammad da alayensa, kuma ka sanya Qur'ani ya zama tsaninmu zuwa ga mafi daukakar gidaje a karamci da kuma tsanin da zai kai mu ga mafi kololuwar mahallin aminci kuma ya zama sababin da za mu samu tsira a filin kiyama, kuma abin hawanmu wanda zai kai mu zuwa gidanmu na har abada. Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da alayensa, kuma muna rokon ka sauke mana nauyin zunubanmu daga kafadunmu, ka ba mu alheran da kake ba masu kyautatawa, kuma ka sanya mu cikin danshin wadanda suke tsayuwa dominka sa’oin dare da sasannin yini, don ka tsarkake mu daga dukkan datti da tsarkin Qur'ani, ka sanya mu cikin wadanda suka haskaku da hasken shiriyarsa, wadanda guri bai shagaltar da su daga tsayuwa ga aiki ba ballanta ya yaudare su da girman kansa. Ya Ubangiji ka yi salati ga Muhammad da alayensa, ka sanya Qur'ani gare mu a cikin duhun dare mai samar da natsuwa, kuma mai kiyayewa daga yaudarar shaidan da hadarurrukan waswasi, ka kuma kare kafafunmu daga takawa zuwa ga sabo, da harsunanmu daga afkawa cikin bata, da dukkan gabobin jikinmu daga afkawa cikin sabo, ka kuma warware mana matsalar fadawa cikin halin gafala mai sarkakiya, saboda zukatanmu su iya kai wa ga fahimtar abubuwansa na ban al’ajabi, da misalansa wadanda suka gajiyar da duwatsu daga iya juriyar daukarsu. Ya Ubangiji ka yi salatinka ga Muhammad da alayensa, don alfarmar Qur'ani ka dauwamar da gyaruwarmu ta zahiri, kuma ka katange mu don alfarmarsa daga sharrin wasiwasi a can cikin zukatanmu, kuma don alfarmar Qur'anin ka wanke dukkan dattin da ke zukatanmu da dukkan abubuwan da suke da alaka da sabo, kuma don albarkacinsa ka daidaita mana dukkan lamurranmu da suke a warwatse, ko kosar da mu daga kishirwar tsayuwar yinin kiyama da albarkarsa, ka tufatar da mu tufafin aminci a ranar firgitar nan mafi girma idan an tashe mu (daga kaburburanmu) don albarkar Qur'ani. Ya Allah ka yi salatinka ga Muhammad da alayensa, kuma don albarkacin Qur'ani ka samar mana mafita na halin talauci da kuncin da muke fama da shi, kuma ka yalwata mana rayuwa sassauka da yalwatar arziki, kuma ka nisantamu daga dabi’u abin zargi da munanan halaye, kuma ka tsare mu daga fadawa cikin halaka ta kafirci da abubuwan da ke jawo munafunci, ta yadda a ranar kiyama za mu samu kanmu ana jagorantarmu zuwa ga yardarka da aljannarka, kuma mu kasance tun a duniya muna cikin wadanda suka tsira daga fushinka kuma masu kiyaye iyakokinka da dokokinka, kuma masu shaidawa ga abin da ke wajenka na halatta halalinsa da haramta haram dinsa. Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da alayensa, kuma don albarkacin Qur'ani ka saukaka mana a yayin zare rai kar mu fuskanci tsananin nan da kwaratsin fitar rai da numfasawar nan mai fita daya-daya a lokacin da rai ya isa ga makogwaro, kuma aka ce wane ne mai cetonsa, kuma mala’ika ya bayyana wanda kafin wannan lokacin idanu ba su iya ganinsa, domin karbar ran, ran da zai fada cikin tsananin firgici na rabuwa, daga baya ya saka shi cikin sauran rayuka cikin zafi da dacin fitar rai kamar kofin da ke cike da sammu. Kuma kusantowarmu da lahira kullum kara matsowa yake yi, kuma za a wayi gari ayyuka an kanannade su a wuya, kaburbura kuma za su zama sune makoma daga nan kuma sai wucewa ranar tsayuwa. Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da alayensa, ka albakaci shigowar mu gidan jarabawa, da tsawon zama a tsakankanin kasa, kuma ka sanya kaburbura bayan bankwana da duniya mafi alheran mazauninmu, kuma ka yalwata mana don rahamarka tsukewar kabarinmu, kuma kada ka kunyata mu a gaban mahalarta tsayuwar ranar kiyama a saboda laifukanmu masu halakarwa, kuma ka yi mana rahama a lokacin da za mu tsaya a gabanka, kuma don alfarmarsa ka tabbatar da dugaduganmu daga girgizar tsallake siradi a yayin wucewa ta kansa, kuma ka haskaka kabarinmu don albarkacin Qur'ani kafin ranar tashi, kuma ka tseratar da mu daga dukkan azabar ranar kiyama da tsananin wannan rana, kuma ka haskaka fuskokinmu ranar da za ka bakanta fuskokin azzalumai a ranar tashi da nadama, kuma ka sanya soyayyarmu a ckin kirazan muminai, kuma kada ka sanya rayuwa a kanmu mai tsanani. Ya Ubangiji ka yi salati ga Muhammad bawanka kuma Manzonka, kamar yadda ya isar da sakonka, ya kuma bayyana al’amuranka, ya yi nasiha ga bayinka, ya Allah ka sanya Annabinmu tsirarka ya tabbata a gare shi da alayensa a ranar kiyama ya zama mafi kusancin Annabawa a gare ka, kuma mafificinsu wajen yin ceto, kuma mafi alkadarinsu a wajenka, mafifincinsu a wajenka matsayi da iso. Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da alayensa, ka daukaka ginuwar addinin da ya zo mana da shi, ka girmama hujjojinsa, ka nauyaya mizaninsa, ka karbi cetonsa da kusancin wasilarsa, ka haskaka fuskarsa ka cka masa haskensa, ka daukaka darajarsa, ka rayamu a kan sunnarsa, ka datar da mu a kan addininsa, ka dora mu a kan manhajinsa, ka bar mu a kan hanyarsa, ka saka mu cikin masu yi masa biyayya, ka tashe mu a karkashin inuwarsa, ka shigar da mu tabkinsa, ka shayar da mu daga kofinsa. Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da alayensa, salatin da za ka isar da shi ga mafi falalar abin da aka yi buri daga alhairai da falalarka da karamcinka kai ma’abocin rahama ne mai yalwa da falala mai karamci. Ya Allah ka saka masa ga abin da ya isar na sakonka da ayoyinka, da nasihar da ya yi ga bayinka, ya jihadin da ya yi a kan hanyarka, fiye da abin da ka saka wa wani daga mala’ikinka makusanta da zababbun Annabawanka mursalai, kuma aminci a gare shi da alayensa masu tsarki da rahamar Allah da albarkarsa[66].
[1] Hadisi na 1,2,3,4,5 da 6 dukkansu daga Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Salat, Babin karatun Qur'ani koda ba a cikin sallah ba, ……………..
[2] Masdarin da ya gabata: Babi na 5, hadisi na 1.
[3] Masdarin da ya gabata, babi na 2, hadisi na 3.
[4] Masdarin da ya gabata, babi na 3, hadisi na 2 da 3.
[5] Masdarin da ya gabata, babin da ya gabata hadisi na 6.
[6] Masdarin da ya gabata, babin da ya gabata, hadisi na 6.
[7] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Salat, Babin karatun Qur'ani koda ba a cikin sallah ba, hadisi na 6
[8] Masdarin da ya gabata, babi na 4, hadisi na 1.
[9] Masdarin da ya gabata, babi na 5, hadisi na 3.
[10] Masdarin da ya gabata, hadisi na 2.
[11] Biharul Anwar: 20:82.
[12] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Dahara, babin sallar jana’iza, babi na 57, hadisi na 5.
[13] Jami’u Ahadisil Shi’a: Kitabul Salat, babin ziyartar kaburbura, babi na 2 a cikinsa akwai hadisai goma.
[14] Al-Kafi: 2/604.
[15] Nahjul Sa’ada: 7/ 223.
[16] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Salat, babin hukunce-hukuncen masallaci, babi na 3, hadisi na 3.
[17] Kuma su wadannan su ne mutanen nan da suke kiyaye ka’idodin tajwidi hakikanin kiyayewa wadanda su da kansu suka samar da su, amma sai dai suna gafala a kan ma’anonin abin da suke karantawa.
[18] A baya an yi karin haske a kan ma’anar wannan.
[19] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul salat, Abwabu kira’atil Qur'an wa lau fi gairil salat, babi na 8, hadisi na 1.
[20] Masdarin da ya gabata, hadisi na 3.
[21] Masdarin da ya gabata: babi na 11, hadisi na 18.
[22] Masdarin da ya gabata: babi na 11, hadisi na 2.
[23] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul salat, Abwabu kira’atil Qur'an wa lau fi gairil salat, hadisi na 8.
[24] Masdarin da ya gabata, babi na 11, hadisi na 1.
[25] Masdarin da ya gabata, hadisi na 10.
[26] Masdarin da ya gabata, babi na 17, hadisi na 2.
[27] Masdarin da ya gabata, babi na 12, hadisi na 3.
[28] Masdarin da ya gabata, babi na 13, hadisi na 1.
[29] Masadarin dai hadisi na 3.
[30] Masdarin da ya gabata, babi na 14, hadisi na 2.
[31] Masdarin da ya gabata, hadisi na 1.
[32] Masdarin da ya gabata, babi na 15, hadisi na 1.
[33] Masdarin da ya gabata, hadisi na 2.
[34] Masdarin da ya gabata, babi na 16, hadisi na 2.
[35] Masdarin da ya gabata, babi na 11, hadisi na 6.
[36] Masdarin da ya gabata, babi na 19, hadisi na 1.
[37] Masdarin da ya gabata, hadisi na 2.
[38] Masdarin da ya gabata, hadisi na 6.
[39] Masdarin da ya gabata, babi na 19, hadisi na 4.
[40] Masdarin da ya gabata, babi na 20 hadisi na 1.
[41] Masdarin da ya gabata, babi na 21, hadisi na 1.
[42] Masdarin da ya gabata, babi na 27, hadisi na 7.
[43] Masdarin da ya gabata, hadisi na 3.
[44] Masdarin da ya gabata, babi na 22, hadisi na 1.
[45] Masdarin da ya gabata, hadisi na 3.
[46] Masdarin da ya gabata, babi na 25, hadisi na 1.
[47] Masdarin da ya gabata, babi na 23, hadisi na 2.
[48] Babi na 24, hadisi na 1.
[49] Masdarin da ya gabata, babi na 26, hadisi na 4.
[50] Masdarin da ya gabata, hadisi na 5.
[51] Masdarin da ya gabata, babi na 27, hadisi na 1.
[52] Na daga abin da ya karanta a watan Ramadan.
[53] Masdarin da ya gabata, babi na 28, hadisi na 1.
[54] Masdarin da ya gabata, babi na 29, hadisi na 1.
[55] Tafsirul Safi: 1/39. Kuma akwai hanyar hadisin ta littafan yan uwa ahlul Sunnah.
[56] Wasa’ilul Shi’a: babi na 27, hadisi na 6.
[57] Nahajul Balaga, huduba ta 158, Juzu’i na 1.
[58] Al-Kafi: 2/624.
[59] Irshadul Qulub: shafi na 78.
[60] Sawabul A’amal: 1/129, babin ladar karatun Qur'ani.
[61] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul salat, Abwabu kira’atil Qur'an fi gairil salat, babi na 27, hadisi na 3.
[62] Uyuni Akbaril Ridha (as): shafi na 162.
[63] Al-Mizan Fi Tafsiril Qur'ani: 1/260, daga Irshadil Qulub na Dailami.
[64] Sunanul Darami: 2/435, Kitabu Fadha’ilul Qur'an; haka nan ma akwai hadisin a cikin littafan Shi’a.
[65] Nahajul Balagha: Juzu’i na daya, huduba ta 110.
[66] Al-Sahifa Al-Sajadiyya: Addu’ar (Imam Sajjad (as)) yayin saukar Qur'ani.