Sashen Ladubba Da Mustahabbai Na Tilawar Qur'ani

| |times read : 1814
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Sashen Ladubba Da Mustahabbai Na Tilawar Qur'ani

      A nan ina son in ambato wani sashe na ladubba da sunnoni da mustahabbai wadanda suke da alaka da karanta Qur'ani da abubuwan da za a amfana da su daga ruwayoyi madaukaka:

1- Mustahabbi ne yin saukar Qur'ani a wata sau daya, kuma ba a son a wuce tsawon wata hudu ba a yi sauka guda ba, wato kenan a shekara za a yi sauka uku, wannan banda karin da ake son a yi a cikin watan Ramadana mai albarka.

2- Karatun ya kasance a jere da niyyar yin sauka wato a faro daga farkon Qur'ani zuwa karshensa, ba a dinga cankar surori nan da can ana karantawa barkatai ba duk irin muhimmancinta kuwa, saboda an fi so a dinga ratsawa ta cikin Qur'anin gabaki dayansa kuma a samu dukkan albarkokinsa, a kan haka ne aka ambaci hadisi mai girma da cewa: “Alhallul murtahilu: wato kenan a faro karatun Qur'ani tun daga farkonsa ana binsa sura bayan sura har zuwa surar karshe, an yi sauka daya kenan, sannan kuma sai a sake farowa daga farko haka dai haka dai”[1].

3- Mustahabbi ne ranar saukar Qur'ani ta zama Juma’a ce, kuma a yayin kammala saukar a addu’ar nan ta musamman ta saukar Qur'ani, addu’ar kuwa tana nan cikin Sahifa Sajjadiyya.

4- Bayan ya kammala saukarsa har zuwa surar karshe, to kada ya tsaya jiran wani abu ya jona sabuwar sauka nan take kawai, koda kuwa suratul Fatiha ce ya fara karantawa sai kuma ya hada da ko aya biyar ce daga suratul Bakara.

5- Ya kasance cikin tsarki, ya kuma zauna a wajen yin sallarsa yana mai fuskantar alkibla.

6- Ya zo a cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri kuma ku yi juriya, kuma ku yi zaman dako” Aali Imran: 200, lallai daga cikin masu zaman dako akwai wanda yake wanzuwa a kan wajen sallarsa yana jiran shigar lokacin sallar farilla, to domin samun falalar masu zaman dako sai muminai suka dinga ribatar wannan damar ta jiran shigowar lokacin sallah suna tilawar Qur'ani, sai ladar kuma ta kasance mai girma idan ya zama a cikin masallaci ne ana jiran shigar lokacin sallar jam’i.

7- Kuma an rawaito cewa mustahabbi ne yin bacci da alwala da kuma karanta Qur'ani kafin mumini ya kishingida a kan shimfidarsa, a cikin wani hadisi ya zo cewa: “Wanda ya yi hadasi (bawali dss) amma bai yi alwala ba, hakika ya bai kyauta min ba, wanda kuma ya yi alwala bai yi sallar nafila raka’a biyu ba, hakika shi ma bai kyauta min ba, wanda kuma ya yi sallar nafila raka’a biyu amma bai rokeni komai ba shi ma bai kyauta min ba, wanda kuma ya rokeni amma sai ban amsa masa ba, to bai kyauta masa ba, to sai dai ni ba Ubangiji ne marar kyautatawa ba”[2], idan kuma aka kara mustahabbancin sallar dare a kan wannan, da kuma mustahabbancin kewayawa bandaki kafin bacci da asawaki, to a nan mun fita daga layin da yawan jama’a, saboda muhimmin wuridin da mumini ya yi riko da shi kafin yin barcinsa domin zai kwanta a kan shimfidarsa yana mai tsaftace hakoransa, sannan ga alwala, ga sallar dare, ko gabaki dayanta ko wani yanki daga gare ta, wasu suna karfafa cewa  a yi ta kafin ketowar alfijir, sannan a karanta daidai gwargwado na Qur'ani mai girma sannan a roki Allah ga kai da kuma ga muminai saboda mumini ya samu ya hada dukkan wadannan mustahabban. Amma mutumin da yake bata dare a kan wasu shirye-shirye da kallon fina-finai na fasadi wadanda suke gajiyar da kwakwalwarsa, zai yi ta rayuwa cikin wahala da kunci ne kawai.

8- Tilawar Qur'anin ta kasance musamman ga ‘yan koyo su dinga hadawa da tafsirin Shubar wanda ya kunshi fa’idodi masu yawa domin tsarin bugunsa irin tsarin bugu ne na Qur'ani marar tarjama amma a gefen rubutun akwai tafsiri a dunkule na ma’anonin kalmomin Qur'ani, shi ne kuma abin da muka fada cewa zai zama cikin manhajin karatu na sababbin dalibai, kuma a cikinsa akwai mukaddima ta ulumul Qur'an wanda kuma wannan wani darasi ne daban, kuma yana dauke da shafi sunkutukum mai nuna maka lambar shafin kowane lafazi na Qur'ani a ina z aka same shi (content) ta yadda kowace aya idan kana son ka san a ina take za ka duba shafin sai ka ga lambar shafin da take. Kuma a cikinsa akwai kira’oi daban-daban game da kalma kwara daya wacce za ka sameta a kasan mus’hafin (Hamish). A cikinsa an jera yadda saukar kowace sura ya kasance, kuma a unwanin kowace sura zai ce ta sauka ne bayan sura kaza, dukkan wadannan fa’idodin suna cikin wannan littafi mai daraja.

9- Yana da kyau ya fara yin saukarsa da bayar da kyautar saukar ga Manzon Allah (s.a.w.a), sauka ta biyu kuma ga Amirul Muminina (as), haka dai haka dai har zuwa ga dukkan Ma’asumai goma sha hudu (as), domin an samu ruwaya game da wannan, su kuma su ne mafiya karamcin halittu sannan za su dawo maka da kyautar daidai da girman karamcinsu a ranar alkiyama.

10- Daga sauti a yayin tilawar Qur'ani, ya kuma zama wannan yana karatun tare da nuna damuwa da yin tadabburin ma’anoninsa, kada ya zama hankoron dayanku shi ne ya gay a kai karshen sura. Kamar yadda yake a hadisi.

11- Mustahabbi ne yin karatun da mus’hafi koda mutum mahaddaci ne, kuma mustahabbi ne ya zama kowa da kowa a gidan ya zama yana da kwafi daya na mus’hafinsa nasa na kashin kansa, sai ya dinga sanya alamar a inda ya tsaya.

12- Sauraron karatun Qur'ani da yin tadabburin abin da yake ji na ayoyin Qur'ani.

      Ina rokon Allah Ta'ala ya rayar da mu, rayuwa ta Qur'ani ya datar da mu cikin wadanda zai yi wa ceto, ya sanya mu cikin wadanda suke shiryuwa da shiryarwarsa, suke haskaka da hasken iliminsa, shi majibincin ni’imarmu ne, kuma shi mai tausayi ne ga bayinsa, daga cikin ludufinsa gare mu ya shiryar da mu zuwa ga addininsa kuma ya ba mu littafinsa mai girma da Annabinsa mai daraja da Ahlul Baiti (as) madaukaka kuma tsarkaka.

(Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu ga wannan, ba mu kasance shiryayyu ba ba domin ya shiryar da mu ba).

                     Muhammad Al-Yakubi

                       Muharram 1422  [1] Al-Kafi: 2/ 605.

[2] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Dahara, Abwabul wudu’i, babi na 11, hadisi na 2.