Wajabcin Tsamar Da Iyali / 49

| |times read : 690
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Wajabcin Tsamar Da Iyali / 49

Qur’ani ya yi ishara a kan a ba da kulawa ta musamman ga iyalai a cikin ayoyi masu yawa: {Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kare iyalanku da kawukanku wata wuta wacce makamashinta mutane ne da duwatsu} (Suratul Tahrim, aya ta 6). Ayar tana koyar da darasi kan wani nauyi da ya hau kan mutum na jagoranci a cikin iyalai da al’ummar da ke kewaye da shi, kari a kan haka akwai hadisin da yake kara bayyana wannan batu: “Ku saurara! Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne game da kiwonsa”, wannan nauyi da aka dora wa bayi zai kara fitowa a sarari sosai duba da wannan zamani na takanolaji da abubuwan ci gaba na zamani wadanda ake amfani da su wajen yada barna, fasadi da kauce hanya.