Bayanin Karshe na Ziyarar Arba'in na Shekarar 1443 AH

| |times read : 668
Bayanin Karshe na Ziyarar Arba'in na Shekarar 1443 AH
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

DA SUNANSA MADAUKAKI:

Bayanin Karshe na Ziyarar Arba'in na Shekarar 1443 AH

“Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu zuwa ga wannan, kuma ba mu kasance muna iya shiryuwa ba, da ba don Allah ya shiryar da mu ba.” (A’araf: aya 43).

A wannan shekara kamar dai yadda yake a dukkan shekaru, miliyoyin Musulmai masu kaunar wannan tafarki na Imam Husaini (as), sun aika da sakon adalci da farin ciki da zaman lafiya da soyayya da 'yan uwantaka ga dukkan bil'adama, kuma sun bayyana kin jinin zalunci da rashin adalci da bautarwa da girman kai da danniya da kwace a cikin wannan tattaki na miliyoyi masu tafiya wacce ta wuce sama da tazarar ɗaruruwan kilomita wanda ke kunshe da dukkan ƙa'idodi masu daraja na ‘yan adamtaka.

A Iraki, a lokacin da muke wadannan hidimomi na kyautatawa da daukar nauyin baƙi wadanda yawansu ya haura gomomin miliyoyi a cikin tsawon wadannan kwanaki, ba mu goranta wa kowa kuma ba mu tsammanin wata lada ko godiya daga kowa. A’a maimakon haka ma, mu muna ɗaukar sa wani wajibi ne da ya hau kanmu muna masu godiya ga Allah Madaukakin Sarki mai jin ƙai wanda ya zaɓi ƙasarmu madaukakiya don ta zama mazaunin manyan waliyansa kuma ya zaɓe mu mu zama mutanen wannan ƙasa kuma masu rungumar gwamnatin adalci ta Allah wacce ya yi wa Imam Mahdi (as) alkawarin (rayukanmu fansa a gare shi) kafawa a wannan ƙasa mai albarka kuma ya rike ta a matsayin babban birnin tarayya a gare shi kuma ya yunkura don cika duniya da aminci da zaman lafiya da ni'ima.

Lallai masu jayayya sun zarge mu a kan wannan tafarki kuma sun jefa shubuhohi da shakku a kai saboda karancin basira da suke fama da ita basirar da za ta ba su damar su gane girma da albarkar da ke tattare da wannan aiki na ibada mai tsarki a kan dukkan bil'adama tun a zamanin da ya gabata da wanda muke ciki yanzu da kuma wanda zai zo nan gaba. Wanda ya ishe shi matsayi cewa shi wannan aiki a cikinsa akwai bayyana soyayya ga Ahlul Baiti (as) kuma Allah Ta’ala da kansa ya yi umarni da a so su inda yake fadin: “Ka ce ba ni tambayarku wata lada a kansa face dai nuna soyayya ga makusanta” (Shura: aya 23). Kuma (ita wannan ibadar) dalili ce ta shiriyar mutane masu yawa zuwa ga tafarkin gaskiya da mubaya'a domin ci gaba ga wannan hanya da shahidai kuma ma'abota gaskiya da salihai suka bi.

Sukan nemi mu zo masu da mu'ujizozi don mu tabbatar da gaskiyar waɗannan ayyuka na ibada, to shin mai ya fi wannan mu'ujiza ga ma'abota hankali! Wanda daga ciki akwai waɗannan dabi’un kyawawa waɗanda wadannan mahalarta sukan nuna tare da duk sadaukarwa da gaskiya da ikhlasi, abin da babu kwatankwacinsa a yau a wannan duniya wacce (al'ummarta) ta nutse cikin son alatun duniya.

Sai dai ina mai jawo hankalinsu zuwa ga ɗaya daga cikin waɗancan mu'ujizozin, wanda shi ne jerin gwanon mutane sama da miliyan goma suna tafiya a hankali tsawon kwanaki kuma suna taruwa a wurare masu cinkoso, kuma a hakan da muka tambayi rukunin likitoci waɗanda suke kan hanya domin kulawa da baƙi sai ga amsa sun ba mu a kan cewa babu wani tabbataccen sakamako da yake nuna kamuwar maziyarta daga cutar corona.

Lallai yawan adadin wadanda suka kamu da lalurar a duk jahohin Iraki wanda kafin wannan lokacin na munasaba ya kusan dubu goma to amma ya ragu a cikin wadannan kwanakin na munasaba zuwa kusan dubu biyu. Yayin da dubun dubatar mahalarta a filin wasa na London a watan Yulin da ya gabata ya haifar da hauhawar da ba a taba ganin irin ta ba a yawan kamuwa da cutar wanda har ya haura dubu hamsin a kowace rana, duk da yake cewa sama da rabin jama'ar Birtaniya sun ɗauki rigakafin coronar, abin mamaki shi ne cewa wannan ya faru ne a ranar da aka yanke shawarar ɗage takunkumi saboda corona, kuma sun kira ranar da ranar 'yanci.

Sai dai abin lura shi ne cewa magana ta ba tana sabawa daukar matakan yin rigakafin da ƙwararrun likitoci suka ba da umarni ba ne ba, a’a sai dai ni ina magana ne a kan hakikanin abin da ya faru.

Lallai lamarin tarurruka na ibada na Allah yana da babban rawar da yake takawa wajen tabbatuwar addini da karfafuwar imani a cikin zukatan mutane, kuma ba za mu iya tunanin yadda mutane za su kasance ba tare da shi ba, sai dai za su koma ga jahilcinsu na farko, kamar yadda ya faru ga sauran al'ummomi lokacin da suka nisanta daga koyarwar Annabawa (as) masu shiryarwa.

Daga karshe muna rokon Allah ya dauwamar da ni'imominsa a kanmu kuma ya kare mana kasarmu Iraki da dukkan kasashen Musulunci daga makirce-makirce da sharri da kaidin makiya kuma ya tabbatar da mu a kan tafarkin adalci, domin lallai shi majibincin ni’imomi ne.

Muhammad Al- Yakubi – Najaf mai tsarki.

20 ga Safar 1443 AH.   28 / 9 / 2021 AD.