Girman Kan Mai Dukiya / 64
Girman Kan Mai Dukiya / 64
Qur’ani mai girma ya yi ishara ga wanda yake dagawa da ji-ji da kai saboda ganin shi mai dukiya ne a kan cewa to ya sani fa lallai yana cikin bakin ciki da asara ne {A’aha! Lallai ne mutum hakika yana girman kai. Domin ya ga kansa cikin wadata} (Suratul Alak, aya ta 6-7). Saboda shi wannan ciwon na ruhi ya sabawa fidirar da aka halicci mutum a kanta kamar yadda ya sabawa abin da hankali ke hukuntawa, domin abin da ya kamata ga wanda ya samu dukiya shi ne yin godiya, tawalu’u da kyautatawa, ba girman kai, kafircewa ni’ima da kangarewa ba.
To kuma shi wannan ciwon na ruhi ya fi ciwon gangar jiki muni da hadari, saboda na biyun yana rushe jin dadin rayuwar duniya ne mai gushewa, amma na farkon shi yana rushe rayuwar lahira ne wacce take madawwamiya.