Jawabin Ta’aziyyar Rasuwar Marigayi Shaikh Muhammad Jawad Al-Mahdawi

| |times read : 585
Jawabin Ta’aziyyar Rasuwar Marigayi Shaikh Muhammad Jawad Al-Mahdawi
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

DA SUNANSA MADAUKAKI:

Jawabin Ta’aziyyar Rasuwar Marigayi Shaikh Muhammad Jawad Al-Mahdawi:


A yau Hauza ilmiyya ta Najaf mai tsarki ta rasa daya daga cikin manyan malamanta, malami wanda aka sanshi da kokari, himma, bincike da bin diddikin (mas’aloli) na ilimi da kuma jajircewa domin amfanar da dalibansa. Na san shi a kan wannan tun shekaru talatin da suka gabata a lokacin da muke jami’ar Addini ta Najaf a karkashin kulawar marigayi hujjatul Islam sayyid Muhammad Kalantar (Q. S), kuma ya karantar da dukkan marhaloli na karatu har zuwa bahasul kharij a Hauza Ilimiyya madaukakiya.

Mutum ne wanda iliminsa yake cakude da tawali’u da girmama kowa da kowa koda yaro ne karami kuwa, ga shi da kokari wajen warware wa mutane bukatunsu, musamman daliban ilimin addini. Kuma ya kasance mutum ne mai nuna kauna ga kowa, mai kyayyawar mu’amala ga jama’a, iya bakin kokarinsa yana yi wajen girmama maraji’an addini da nuna masu kauna.

Wannan rasuwar tasa da ta zo mana kwatsam ba-zato ta haifar da radadi da damuwa a tsakanin abokansa da dalibansa da duk wanda ya san darajarsa da daukakarsa, muna rokon Allah Ta'ala ya lullube shi da rahamarsa kuma ya sada shi da babban rabo da farin ciki haka nan kuma ya tashe shi da waliyyansa Muhammad (s.a.w.a) da Alayensa Tsarkaka (as).

Muhammad Al-Yakubi

17 ga Rajab 1442 AH

2/3/2021 AD