Nauyin Da Ya Hau Kan Hauza Dangane Da Farfado Da Ayyukan Qur'ani

| |times read : 824
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Nauyin Da Ya Hau Kan Hauza Dangane Da Farfado Da Ayyukan Qur'ani

Ni a nan hadisi daya kawai zan ambata wanda zai bayyana nauyin da ke kan Hauza madaukakiya dangane da wayar da kan al'umma da shiryar da su da kawo gyara a tsakaninsu, hakika an rawaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) cewa: Ya yi huduba, bayan ya yi godiya ga Allah da yabo a gare shi, sannan ya ambaci wasu gungu na musulmi ya yabe su, sannan ya ce: ((“Mai ke damun wasu jama’a ne, ba su koya daga makwabtansu, kuma ba su yin tafakkuhi haka nan ma ba su zurfafawa cikin neman ilimi? Na rantse da wanda raina yake a hannunsa ko dai su koyar da makwabtansu kuma su koya daga gare su, ko su yi tafakkuhi a cikin addini ko su zurfafa neman sani ko kuma ni da kaina kafin Allah ya azabtar da su a lahira zan yi masu ukuba a nan gidan duniya, sannan sai ya sako (daga kan mimbari) ya shiga gidansa. Sai sahaban Manzon Allah (s.a.w.a) suka shiga tattauna maganar suna tambayar junansu cewa: Mece ce ma’anar wannan maganar? Suka ce: Ba mu san me yake nufi da wannan maganar ba, sai dai ko akwai Ash’ariyyin malamai ne fakihai amma makwabtansu kuma jahilai.

         Sai jama’a daga Ash’ariyyin suka taru suka shiga wurin Annabin Allah (s.a.w.a) suka ce: Ka ambaci wasu gungu na jama’a da alheri, amma mu ka ambace mu da sharri, to mene ne aibinmu? Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Eh haka ne, ko dai ku koyar da makwabtanku su san addininsu, su yi tafakkuhi a cikinsa, ku hore su da aikata aikin kwarai ku hane su ga mummuna ko ko kuma ni da kaina kafin Allah ya azabtar da ku a lahira zan yi maku ukuba tun a nan gidan duniya. Sai suka ce ya Manzon Allah (s.a.w.a): Ka taimaka mana da shekara guda, za mu koyar da su tsawon wannan shekarar guda har sai sun koya. Sai ya ba su damar su je su koyar da su shekara guda din. Sannan sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya karanta fadin Allah: “An la’ani wadanda suka kafirta daga bani Isra’ila a kan harshen Dawud da Isa dan Maryam, wannan kuwa saboda sabawar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta’adi. Sun kasance ba su hana juna daga abin ki wanda suka aikata, hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya munana” Ma’ida: 78-79))[1].

Wadannan su ne wani sashe na kirana da nake gabatar da su ga Hauza mai girma a dangane da wannan janibin, kuma nauyi ne da yahau kan gabaki dayanmu wato tilawar Qur'ani da amfana da shi a cikin sa’oin dare da sasannin yini. Da sannu za ka san da yawa dangane da wannan ta hanyar hadisai masu tsarki da za su zo.

       Kuma wannan nauyin na Hauza ba su kadai ta shafa ba, sai dai kawai mun ambata masu haka ne saboda kasantuwar wajabcin ya fi nauyi a kansu fiye da waninsu, in ba haka ba, ai al'umma dukkansu ababen tambaya ne su yi biyayya ga wannan daidai gwargwadon kowane mutum. To masu ilimi dan kadan su fara da karanta tafsirai matsakaita kamar tafsirin Shubar.

Kuma ni ina yi wa kowane musulmi nasiha – wannan wani abu ne da ni da kaina na gwada shi – ya fara rayuwarsa tare da Qur'ani, ya dinga karanta shi daga mus’hafin da yake da tafsiri, kamar dai wanda muka ambata domin ya taimaka masa wajen fahimtar kalmomin da ke cikin ayoyin Qur'ani a yayin da yake tilawarsa, ya kuma ci gaba a kan wannan halin har ya yi sauka mai yawa ta yadda zai iya samun wani ilimi dunkulalle a kan Qur'ani, sannan ya dawo ya dinga karanta mus’hafi tare da auna fahimtarsa yana kuma kara fadada karatun nasa ta hanyar karanta littafan tafsiri wadanda bayaninsu ya gabata kamar Al-Mizan da Fi Zilalil Qur'an, ya kuma karanta littafan da suka yi sharhi a kan ma’anoni da mafahim na Qur'anin ko kuma suka yi tafsiri na maudu’i maudu’i, ta yadda zai dauki dayansu a matsayin unwani na bahasinsa sannan ya dinga fitar da kowace aya-aya da ta yi magana a kan wannan unwanin ya tattara su sannan ya fitar da natija game da ra’ayi da nazarin Qur'ani a kan wannan unwanin da ya dauka – ni a nan ina aron wadannan isdilahohin fikirori din ne domin na saka maku natsuwa a cikin rayuka ina kuma mai kulawa – wanda ake sa ran ya iya magance wata mushkila da kuma hakikanin yadda rayuwar al'umma take gudana, shin rayuwar nan a kan akida ce ko akhlak ko fikira ko waninsu.

       Amma ina ganin a cikin gabatar da bahasin idan za a dinga bibiyar manya na Hauza mai girma zai fi domin za su taimaka sosai wajen bayar da amsa a kan abin da ya shiga duhu da kuma kara dora mutum a kan hanya domin ya amfana, tunda yake ita Hauza da al'umma dayansu yana zama mai cika daya ne. Hauza tana wayar da al'umma game da sanin addininsu, al'umma kuma suna kwankwasar Hauza domin ta tsaya a kan nauyin da yake a kanta da kuma daidai bukatar al'umma gare ta a irin zamanin da suke rayuwa, to daga nan za ka samu Hauza ta kai koluluwa na isa ga kamala fiye da waninta kuma al'umma za ta san waye mai gyara ta.

          Yana daga cikin ayyuka na dole yin bahasi a kan daya daga cikin darussan Qur'ani bisa la'akari da tarihin saukarsa, dukk da cewa yin hakan a warware a wadace abu ne mai wahala saboda rashin samun dalili yankakke a kansa, sai dai za a iya tsinto wasu sashe na abubuwan da suka zo kuma a yi amfani da su a wannan bahasin kuma a fa’idantu mai yawa game da sanin matakan da Qur'ani ya dauka wajen gyaran al'umma tunda kamar yadda aka sani ya sauka ne daki-daki a hankali a hankali (tadriji) daidai gwargwadon yadda abubuwa suka dinga faruwa.

    Lallai wannan saukar da Qur'ani ya dinga yi daki-daki daya bayan daya maimakon sauka lokaci guda tana da wani sako da wani tasiri na musamman a aikace a cikin yanayoyi da ya magance su, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma (Qur'ani ne) da muka karkasa da rarraba shi domin ka karanta shi ga mutane a kan jeri-jeri, kuma sun saukar da shi saukarwa” Isra’i: 106, kuma madamar littafi ne na tarbiyya, shiryarwa da rayuwa to fi ma la budda ya zama daki-daki cikin tausasawa don haka sai ya dinga siffanta yadda zai dinga bayar da maganin da ya dace  a lokutan da suka dace a kuma daidai gwargwado babu ragi babu kari, kuma ba kafin faruar abu ko bayan faruwarsa ba, a’a a daidai lokacinsa. Kuma kamar haka ne wannan Qur'anin ya kama hannun wannan al'umma da abokantaka domin tasamu kanta bayan wani dan lokaci cikin daukaka, kamala, wadata, karfi da kuma izza.[1] Al-Mizan Fi Tafsiril Qur'an: 6/84, a karkashin tafsirin ayar, daga littafin Durrul Mansur.