SHAFIN FARKO | | TAMBAYOYI
TAMBAYOYI

Raba labarai

Yarjejeniyar Ma’aurata a Kan Dakatar Da Shigar Ciki

Shin ko yana daga cikin abubuwan da suka halasta ga ma’aurata wato miji da mata su yi yarjejeniya a tsakaninsu a kan dakatar da haihuwa, bayan Allah ya azurta su da samun ‘ya’ya maza da mata?

Da Sunansa Madaukaki

Yana halasta a dakatar da haihuwa da ma’anar cewa a hana shigar ciki din, sai dai dole ne a kiyaye hanyar da za a bin wajen hana shigar cikin wato ta zama hanya ce wacce take halastacciya, kamar fitar da maniyi a waje, ko kulle mahaifa, koda yake idan ya zama na dindindin ne to akwai ishkali kasantuwar a cikin yin hakan akwai tsayar da wata gabar jiki daga aiki.

Raba labarai

 

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Marji’in addini Ayatullahi Yakubi: Ya yi hani a kan dukkan abin da zai haifar da sabani da rarraba.

Samahat Marji’in Addini Mai Girma Ayatullah Shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa).

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh.

Lokaci bayan lokaci a kan samu wasu masu yin batanci da zagi ga ababe masu daraja na addini sukan aibata wannan ko wancan tare da tozarta shi, to mece ce matsayarku a kan wannan yanayin?

Da Sunansa Madaukaki:

Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.

Matsayarmu a game da wannan aiki, a fayyace take kuma shi ne cewa tuni muka yi hani ga aikata shi a cikin bayananmu masu yawa da kuma a cikin munasabobi daban-daban, wannan abin ya sabawa tarihin rayuwar Imamai Ma’asumai (as) da irin fuskantarwarsu ga ‘yan shi’arsu, kuma lallai ne cewa wannan abin yana haifar da rarraba, sabani da rashin jituwa, husuma da jayayya. Lallai Allah Tabaraka wa Ta’ala ya yi hani gare shi a cikin fadinsa: “Kuma kada ku yi jayyya sai hakan ya zama sanadin raunanarku”, (Anfal, aya ta 46). Don haka duk lokacin da abubuwan da suka hada wasu bangarori biyu suka kara yawaita to dole ne ya zama a kara kula da yin takatsantsan, da a ce kuma abubuwan da suka hada mu ba za su iya dunkule mu waje guda ba, to ya kamata makiyinmu wanda ba ya tsaron wata zumunta a tsakaninmu gabaki dayanmu haka nan ba ya tsaron wata amana, ya zama sanadin haduwarmu waje guda mana, hatta ma ba ya ko yin takatsantsan wajen cin fuskar mafi girman abubuwanmu masu tsarki sannan kuma yakan aikata mafi girman laifuka.

Kuma Allah shi ne wanda ake neman taimako a wajensa a kan abin da ku ke siffantawa.

                                                                                                                                      Muhammad Al-Yakubi

                                                                                                                                            15/2/1436 AH

                                                                                                                                             5/4/2015 AD

 

 

Raba labarai

Ba Ya Halasta Ga Iyaye Bincike Da Bin Kwakkwafin Na’urorin ‘Ya’yansu

 

Marji’in addini samahatul shaikh Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya ce: Lallai ba ya halasta ga iyaye maza da mata da sauran waliyyai bin kwakkwafi da bincike a cikin na’urorin da suke da alaka ta kai tsaye da ‘ya’yansu mazansu da matansu, kama daga wayoyinsu na hannu, I-pad da laptop da dai sauransu da nufin bibiyarsu don gudun kada su fada cikin sabo.

Samahatul shaikh Yakubi ya ci gaba da cewa dalilinsa a kan haka shi ne cewa bincike na kwakkwafi abu ne da Allah Ta'ala ya haramta a cikin fadinsa: “Kada ku yi binciken kwakkwafi”, Hujurat aya ta 12. Koda yake ta yiwu hadafin binciken kwakkwafin ya zama ingantacce to amma dole ne fa hanyar da za a bin ita ma ta zama wacce shari’a ta yadda da ita ce domin (son kaiwa ga manufa ba ya halasta aikata kowane abu) idan dai ta kasance ta sabawa shari’a, koda yake a nan ta hanyar wannan binciken kwakkwafin uba ko uwa za su iya gano wani kuskure a cikin dabi’u da halayen ‘ya’yansu har ma su magance shi, sai dai yin hakan zai janyo masu rashin aminci a tsakaninsu da ‘ya’yan nasu har ta kai ga babu sauran sakin jiki ko wata magana gwari-gwari a tsakaninsu, to kuma shi wannan matakin yana da hadari wanda zai kai ga rushewar kyakkyawar alakar da take tsakanin iyayen da ‘ya’yan nasu.

Amma hanyar da ta dace ita ce sanya ido ga ‘ya’yan cikin lura, gogewa da gwanancewa amma ba tare da wuce gona da iri ga ‘yancinsu ba.

Haka nan ma samahatul shaikh da ya juyo da maganarsa ga su ‘ya’yan a kan kansu ya hore su da yin biyayya ga iyaye da kuma nisantar duk abin da zai jefa su cikin damuwa, tare da duk wani abu wanda zai kawo zargi ko shakku tsakaninsu da iyayen nasu, kamar kulle masu kofa don kar su shigo cikin dakin, ko kuma noke-noke da boye-boye a kan wasu lamurra da sauran ire-iren wadannan wadanda za su jawo shakkar da za ta kai ga iyayen su fara tunanin daukar matakai na tsawatarwa.

Kamar yadda haka hukuncin yake ga ma’aurata, don su ma ba ya halasta ga kowane daya daga cikinsu ya kama bibiyar tare da bincikar kayan dan uwansa don kawai tsammanin faruwar wani abu ko shakka kan wani abu, domin kamar yadda muka fada hakan yana janyo rushewar walwala, aminci da yardar da take tsakaninsu.

Raba labarai

Fatawa Dangane Da Zagin Ababen Girmamawa Na Addini Na ‘Yan Uwa Ahlussunah.

Da Sunansa Madaukaki

Samahatul Marja’in Addini Ayatullah Al-Uzma Shaikh Muhammad Yakubi (Allah Ya Tsawaita Kwanakinku)

Ya shugabanmu mai girma, a ranar shahadar Imam Muhammad Jawad (as) an samu taron wasu matasa da suka fito suna zagin abubuwan girmamawa na addina na ‘yan uwa ahlusunnah.

To mene ne ra’ayinku dangane da wannan kuma wace nasiha ce za ku yi wa al’ummar musulmai game da hakan? 

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu Alaikum Warahmatullah wa Barakatuhu

Wannan abin ai wauta ce tsagwaronta da aikin jahilci, ba shi da wata alaka da koyarwar Ahlul Bait (as), kuma lallai ba na raba daya biyu cewa akwai wani boyayyen hannu wanda yake kara ruruta wutar fitinar nan da kambamata daga bangarori nan guda biyu, don haka mu al’ummar Musulmi tare da dukkan sabanin fahimtarmu muna da matukar bukatar taka-tsantsan da sanya ido a kan wannan bakar fitina, kuma a baya ma na tsawatar da mu a kanta a cikin zance na mai taken (Kaidin shaidan don gurbata yankunanmu), kuma mun gargadi jama’a a kan haka.

 

 

 Muhammad Al- Yakubi  

7/Zulhijja/1434 AH.

Raba labarai

Dalilan Da Ke Haifar Da Jihadi A Musulunci

Marji’in addini samahat shaikh Yakubi tare da girmamawa da fatan amincin Allah albarkarsa da ni’imominsa su tabbata a gare ku.

Da farko ina son in fara da bayyana maku kaina: Ni mutum ne ma’abocin addini amma kirista dan kasar Iraki daga birnin Mausul, amma yanzu ina zaune a birnin Paris a kasar Faransa ina karatuna a fannin ilimin addinai sashen ilimi mai zurfi wanda ke tattauna nazariyoyi a tsakanin addinai. A shekara mai zuwa ne zan shiga shekarar karshe ta karatuna a inda zan karbi shaidar digiri na biyu.

Maudu’in rubutuna na project shi ne Jihadi a Musulunci da Kiristanci… Wannan kuma wani maudu’i ne, wato kamar dai yadda ka sanshi gafarta malam lamari ne mai wuyar sha’ani… kuma a mafi yawancin lokaci a kan ma yi masa gurguwar fahimta ne wacce ta sabawa tushensa da asalinsa. Shugaban bangaren karatunmu ya matsa a kan cewa sai na fadada maudu’in kada in takaita shi a kan fikihun sunnah kurum, a’a in hada har da fikihun shi’a…

Manya-manyan littafan da na dogara da su wajen bibiyar bahasin nawa sun hada da littafan sunnah da na shi’a masu daraja kamar irinsu… Biharul Anwar, Mizanul Hikma, Man La Yahduruhul Fakih, Al-Kafi da Al-Tahzib.

Ko kuna da karin wasu littafan wadanda za ku amfanar da ni? Kuma ko za ku yi mani wasu nasihohi wadanda za ku fuskantar da su gare ni domin bahasina ya zama kammalalle? Ina mika godiyata gare ku game da wannan, sannan ina neman ku sanar da ni shin ko akwai bambanci tsakanin ma’anar jihadi a fikihun sunnah da fikihun shi’a? Kuma shin (idan akwai bambancin) to a mahangarku mene ne wannan bambancin?

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu

Ina taya ka murnar zagayowar idin Kirismeti (tunawa da haihuwar Annabi Isa ‘as’) wanda yake shi alami ne na soyayya, tawali’u, tsarkaka daga munanan ayyuka, koma baya, ji-ji da kai da afkawa cikin sha’awace-sha’awace da jin dadi (na duniya).

Kuma ina yi maka marhabin lale ya kai dan uwa kuma dan kasarmu, mu Irakawa a cikin garinku na Mausil da dukkan sauran biranen Iraki wadanda ake zalunta, wadanda ma’abota karfi azzalumai macuta masu danniya masu halayen dabbanci suka mamaye, muna rokon Allah Ta’ala ya tallafa mana mu da ku da kuma dukkan ahalinmu, kuma muna fatan ya kawo mana mafita daga wannan mummunan halin da muka samu kanmu a ciki.

Dangane da wannan bahasin, littafai kawai ba za su wadatar da kai sosai da sosai ba domin suna bukatar a yi masu sabon karatu gwargwadon yanayi da zamanin da muke ciki wanda abubuwa ke ta aukuwa a doron wannan kasa da canje-canje na wannan zamanin, kari a kan haka kuma wadannan mutanen ‘yan ta’adda sun riga sun munana wannan suna mai daraja na (Jihadi) a idon duniya, alhali Musulunci ya barranta da wadannan ayyukan nasu na dabbanci.

Amma da za ka yi muraja’ar rumbun tattara bayanai na hukunce-hukuncen shari'a wanda rubuta shi ya zama wata al’ada ce ta malaman fikihu domin mabiyansu su amfana, sannan ka san Risala ilimiyya dita wacce na sa mata suna (Subulul Salam) da za ka samu cewa babu babin jihadi a cikinsu, domin ni ina bukatar dogon lokaci domin in yi wa bahasin karatu na musamman da izinin Allah Ta'ala daidai da mahanga kammalalliya mai hikima (wacce ta dace da wannan zamani na wayewa da ci gaba).

Amma a takaice dan abin da zan fada maka daga wanda na fa’idantu da shi daga Qur’ani da hadisai masu tsarki na Imamai Ma’asumai (as) shi ne cewa ba ya halatta a yaki ko kashe wani mutum daga cikin mutane sai dai idan shi mabarnaci ne a doron kasa wanda yake barazana ga rayuwar mutane da tsarin al’umma na bai-daya, ko kuma yana daga cikin wadanda suke hana mutane yin akidarsu ko addininsu cikin walwala kuma yana jajircewa wajen ganin ya kaskantar da su kuma ya tilasta masu barin addininsu da karfin tsiya.

Allah Ta'ala ya ce: “Kuma ku yake su har wata fitina kada ta kasance, kuma ya kasance addini dukkansa na Allah ne” (Ma’ida, aya ta 39). Da fadinsa Ta’ala: “Abin sani kawai sakamakon wadanda suke yakar Allah da Manzonsa, kuma suna himmantuwa a cikin kasa domin yada barna shi ne a kashe su ko kuma a gicciye su ko kuma a daddatse hannayensu da kafafunsu daga sabani, ko kuma a kore su daga kasa” (Ma’ida, aya ta 33). Haka lamarin yaki ya kasance, don haka hatta yake-yaken da rundunonin musulunci suka je bai kasance domin fadada mulki ko yin tasiri ko samun ganimomin yaki ko kuma kawai saboda a tilasta wani ya shiga Musulunci ne ba, a’a an yi su ne kawai domin bayar da kariya daga fitintinun dawagitai da masu girman kai wadanda suka kasance suna danne hakkokin mutanensu suna hana su ‘yancinsu na sallamawa gaskiya, idan wadannan katangogin suka gushe (kamar yadda yake a yau dinmu) to a nan yaki ba ya halatta domin ko Allah ya ce: “Babu tilasci a addini”. (Bakara, aya ta 256).

An samu masu addinai daban-daban wadanda suka rayu a karkashin daular Musulunci kuma babu wanda ya tilasta masu cewa sai sun canja addinansu.

Idan ka ga nassosi na addini suna magana a kan yakar wasu kamar mushrikai da sauransu to ba wai suna kallon ainahin don sunansu mushrikai a kashin kansu ne ake magana ba, a’a ana dai kallon ayyukan da suka yi ne na wuce gona da iri da danniya a kan al’ummar Musulunci da kokarin tilasta masu barin addininsu. To haka dai lamarin yake, kuma da yake magana ba karewa take yi ba, sannan a cikin rubuce-rubucena na bijiro da irin wannan da yawa. Ina yi maku fatan alheri da dacewa.

Muhammad Yakubi 25/12/2014 AD.   

 

 

 

Raba labarai

Daddatse Gawar Mamaci

Samahat Shaikh Ayatullah Al Uzma Yakubi Allah Ya Albarkaci Rayuwarku Ya Tsawaita Maku Ita.

Mene Ne Ra’ayinku A Kan Wannan Tambayar Mai Zuwa:

Mene ne hukuncin shari’a a kan daddatsa gawar mutum mai laifi, idan jami’an shari’a masu alkalanci na musamman kebantattu a kan bincike irin wannan suka ba da umarni ga sashen likitanci da kiwon lafia domin su yi bincike a kan gawar, ko kuma abin da aka fi sani da daddatsa gawar mutum domin a san hakikanin dalilin da ya sabbaba mutuwarsa?

Da sunansa Madaukaki:

Ba ya halatta a daddatsa gawar mamaci wato a datse wani bangaren jikinsa ko wasu bangarorin jikinsa domin alfarmar da yake da ita a halin yana mace daidai take da alfarmarsa a yayin da yake a raye, to sai dai idan har ya zama akwai wata maslaha mai muhimmanci wacce za ta jawo a daddatse wasu gabobinsa din kamar tabbatar da kubutar wanda ake tuhuma ko biyan hakkin wani mutum, ko domin rarrabewa a tsakanin mutum biyu masu husuma, ko tunkude wata babbar cuta, kuma idan ya zama dole tabbatuwar hakan ta dogara ne kawai ta hanyar daddatse gawar, to ya halatta.

Amma indai domin kawai ana son a san dalilin da ya sabbaba mutuwar ne, wannan ko kadan ba ya zama hujjar da za ta jawo a daddatse gawar mamaci, kuma lallai mun fadakar da hukumomin da abin ya shafa dangane da wajabcin kiyaye ka’idodin shari’a, tare da takaituwa a yayin daddatsewar ga wuraren da shari’a ta ba da dama a kansu, da zarar ba hakan aka yi ba, to wadanda suka aikata sabanin haka sun aikata mummunan laifi, muna neman tsari daga Allah. Wanda ya datse wata gaba ta mamaci kai tsaye ba tare da kiyaye hukuncin shari’a ba to shi ne zai dauki nauyin biyan diyyar wannan danyen aiki da ya aikata ga ‘yan uwan mamacin, wacce an riga an fadi kwatankwacin abin da za a bayar din na diyya a cikin babin diyya (kitabul diyyat) a cikin littafin Risalatul Amaliyya.

Muhammad Al-Yaqubi

28 ga Muharram 1436 AH.   21/11/2014 AD    

 

Raba labarai

Da Sunansa Madaukaki

Marji’in Addini Samahatul Shaikh Muhammad Yakubi (Da fatan Allah ya yawaita albarkarsa a gare ka).

A kwanukan baya-bayan nan a cikin wannan zamanin namu akwai wani wasan da ya yadu wanda ake yinsa a cikin wayar hannu da kwanfuta wanda aka lakabawa suna da (clash of clans). Wannan wasan yana daukar lokuta masu yawa na samari, sannan wasu suna sayar da wasan har su amshi kudi daga hannun wasunsu. Yadda wannan wasa yake kuwa shi ne wani wasa ne da ya kumshi girka rundunar sojoji da gina masu gari tare da katange garin, sannan sai a dinga kai hari ga makiya domin a tara maki, to duk lokacin da makin wannan gari ya yi yawa to daraja da tsadar garin za su yi sama, kamar kuma yadda dan wasan zai dinga rugurguza duk wani babban mutumin da aka kaddara samuwarsa a cikin wadancan makiya din. To kamar dai yadda ku ka sani ya samahatul shaikh cewa bahasosin ilimi na baya-bayan nan sun tabbatar da cewa wasu daga cikin wasannin kwamfuta (na zamani) suna kara rura wutar kiyayya a tsakankanin yara da matasa, kari a kan irin lokutan da irin wadannan wasannin na kwamfuta suke cinyewa a cikin gidaje ne ko a gidajen kallon wasanni da shagunan masu sayar da neskafi, kuma wannan wasan kai tsaye yana jan hankalun yara da matasa ta hanyar canja masu nauo’in dabi’unsu a rayuwa. Shin samahatul shaikh ko wannan wasan yana halasta a yi shi, kuma ko yana halasta a shiga cikin gidajen da ake yinsa.

Muna jiran amsarku, mun gode.

 

 

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu

Mun yi bincike a kan wannan wasa da yadda ake yinsa da wadanda ake yin wasan da su, sai muka samu cewa akwai wadansu abubuwa wadanda suke tilasta yin hani ga aiwatar da shi, kuma muna da maganganu da yawa da aka yada su tun bayan faduwar gwamnatin Saddam a shekarar 2003 a yayin da muka fayyace hadurran irin wadannan wasannin ga hankulan yara da tarbiyyar jama’a, aklak dinsu, addininsu da tattalin arzikinsu, kuma wadannan kadai sun isa su sa a hana yin wadannan wasanni.

A saboda haka muna yin nasiha ga waliyyai da su sanya ido a kan matasansu domin katange su daga wannan hadarin kuma su kula sosai a kan gabaki dayan kai-komonsu, kamar yadda muke yin kira ga shuwagabannin kananan hukumomi da na jahohi a kan su kafa doka da kuma gudanar da ita a kan masu gidajen kallo da shagunan shan neskafi, domin kada ya zama an barsu har su fi muhimmatar da tara dukiya a kan gyara tarbiyyar yaranmu da kasarmu, a wajen Allah muke neman taimako.

 

Muhammad Yakubi

8 ga Rabi’ul Sani 1437 AH.      

1 2 3 4 5
total: 47 | displaying: 41 - 47

OFISHIN MARJI’IN ADDINI

SHAIKH MUHAMMAD YAQUBI (ALLAH YA TSAWAITA KWANANSA) AIKO DA TAMBAYOYINKA

NAJAF MAI TSARKI