Dalilan Da Ke Haifar Da Jihadi A Musulunci

| |times read : 505
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Dalilan Da Ke Haifar Da Jihadi A Musulunci

Marji’in addini samahat shaikh Yakubi tare da girmamawa da fatan amincin Allah albarkarsa da ni’imominsa su tabbata a gare ku.

Da farko ina son in fara da bayyana maku kaina: Ni mutum ne ma’abocin addini amma kirista dan kasar Iraki daga birnin Mausul, amma yanzu ina zaune a birnin Paris a kasar Faransa ina karatuna a fannin ilimin addinai sashen ilimi mai zurfi wanda ke tattauna nazariyoyi a tsakanin addinai. A shekara mai zuwa ne zan shiga shekarar karshe ta karatuna a inda zan karbi shaidar digiri na biyu.

Maudu’in rubutuna na project shi ne Jihadi a Musulunci da Kiristanci… Wannan kuma wani maudu’i ne, wato kamar dai yadda ka sanshi gafarta malam lamari ne mai wuyar sha’ani… kuma a mafi yawancin lokaci a kan ma yi masa gurguwar fahimta ne wacce ta sabawa tushensa da asalinsa. Shugaban bangaren karatunmu ya matsa a kan cewa sai na fadada maudu’in kada in takaita shi a kan fikihun sunnah kurum, a’a in hada har da fikihun shi’a…

Manya-manyan littafan da na dogara da su wajen bibiyar bahasin nawa sun hada da littafan sunnah da na shi’a masu daraja kamar irinsu… Biharul Anwar, Mizanul Hikma, Man La Yahduruhul Fakih, Al-Kafi da Al-Tahzib.

Ko kuna da karin wasu littafan wadanda za ku amfanar da ni? Kuma ko za ku yi mani wasu nasihohi wadanda za ku fuskantar da su gare ni domin bahasina ya zama kammalalle? Ina mika godiyata gare ku game da wannan, sannan ina neman ku sanar da ni shin ko akwai bambanci tsakanin ma’anar jihadi a fikihun sunnah da fikihun shi’a? Kuma shin (idan akwai bambancin) to a mahangarku mene ne wannan bambancin?

Da Sunansa Madaukaki

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu

Ina taya ka murnar zagayowar idin Kirismeti (tunawa da haihuwar Annabi Isa ‘as’) wanda yake shi alami ne na soyayya, tawali’u, tsarkaka daga munanan ayyuka, koma baya, ji-ji da kai da afkawa cikin sha’awace-sha’awace da jin dadi (na duniya).

Kuma ina yi maka marhabin lale ya kai dan uwa kuma dan kasarmu, mu Irakawa a cikin garinku na Mausil da dukkan sauran biranen Iraki wadanda ake zalunta, wadanda ma’abota karfi azzalumai macuta masu danniya masu halayen dabbanci suka mamaye, muna rokon Allah Ta’ala ya tallafa mana mu da ku da kuma dukkan ahalinmu, kuma muna fatan ya kawo mana mafita daga wannan mummunan halin da muka samu kanmu a ciki.

Dangane da wannan bahasin, littafai kawai ba za su wadatar da kai sosai da sosai ba domin suna bukatar a yi masu sabon karatu gwargwadon yanayi da zamanin da muke ciki wanda abubuwa ke ta aukuwa a doron wannan kasa da canje-canje na wannan zamanin, kari a kan haka kuma wadannan mutanen ‘yan ta’adda sun riga sun munana wannan suna mai daraja na (Jihadi) a idon duniya, alhali Musulunci ya barranta da wadannan ayyukan nasu na dabbanci.

Amma da za ka yi muraja’ar rumbun tattara bayanai na hukunce-hukuncen shari'a wanda rubuta shi ya zama wata al’ada ce ta malaman fikihu domin mabiyansu su amfana, sannan ka san Risala ilimiyya dita wacce na sa mata suna (Subulul Salam) da za ka samu cewa babu babin jihadi a cikinsu, domin ni ina bukatar dogon lokaci domin in yi wa bahasin karatu na musamman da izinin Allah Ta'ala daidai da mahanga kammalalliya mai hikima (wacce ta dace da wannan zamani na wayewa da ci gaba).

Amma a takaice dan abin da zan fada maka daga wanda na fa’idantu da shi daga Qur’ani da hadisai masu tsarki na Imamai Ma’asumai (as) shi ne cewa ba ya halatta a yaki ko kashe wani mutum daga cikin mutane sai dai idan shi mabarnaci ne a doron kasa wanda yake barazana ga rayuwar mutane da tsarin al’umma na bai-daya, ko kuma yana daga cikin wadanda suke hana mutane yin akidarsu ko addininsu cikin walwala kuma yana jajircewa wajen ganin ya kaskantar da su kuma ya tilasta masu barin addininsu da karfin tsiya.

Allah Ta'ala ya ce: “Kuma ku yake su har wata fitina kada ta kasance, kuma ya kasance addini dukkansa na Allah ne” (Ma’ida, aya ta 39). Da fadinsa Ta’ala: “Abin sani kawai sakamakon wadanda suke yakar Allah da Manzonsa, kuma suna himmantuwa a cikin kasa domin yada barna shi ne a kashe su ko kuma a gicciye su ko kuma a daddatse hannayensu da kafafunsu daga sabani, ko kuma a kore su daga kasa” (Ma’ida, aya ta 33). Haka lamarin yaki ya kasance, don haka hatta yake-yaken da rundunonin musulunci suka je bai kasance domin fadada mulki ko yin tasiri ko samun ganimomin yaki ko kuma kawai saboda a tilasta wani ya shiga Musulunci ne ba, a’a an yi su ne kawai domin bayar da kariya daga fitintinun dawagitai da masu girman kai wadanda suka kasance suna danne hakkokin mutanensu suna hana su ‘yancinsu na sallamawa gaskiya, idan wadannan katangogin suka gushe (kamar yadda yake a yau dinmu) to a nan yaki ba ya halatta domin ko Allah ya ce: “Babu tilasci a addini”. (Bakara, aya ta 256).

An samu masu addinai daban-daban wadanda suka rayu a karkashin daular Musulunci kuma babu wanda ya tilasta masu cewa sai sun canja addinansu.

Idan ka ga nassosi na addini suna magana a kan yakar wasu kamar mushrikai da sauransu to ba wai suna kallon ainahin don sunansu mushrikai a kashin kansu ne ake magana ba, a’a ana dai kallon ayyukan da suka yi ne na wuce gona da iri da danniya a kan al’ummar Musulunci da kokarin tilasta masu barin addininsu. To haka dai lamarin yake, kuma da yake magana ba karewa take yi ba, sannan a cikin rubuce-rubucena na bijiro da irin wannan da yawa. Ina yi maku fatan alheri da dacewa.

Muhammad Yakubi 25/12/2014 AD.