Ba Ya Halasta Ga Iyaye Bincike Da Bin Kwakkwafin Na’urorin ‘Ya’yansu

| |times read : 460
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Ba Ya Halasta Ga Iyaye Bincike Da Bin Kwakkwafin Na’urorin ‘Ya’yansu

 

Marji’in addini samahatul shaikh Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya ce: Lallai ba ya halasta ga iyaye maza da mata da sauran waliyyai bin kwakkwafi da bincike a cikin na’urorin da suke da alaka ta kai tsaye da ‘ya’yansu mazansu da matansu, kama daga wayoyinsu na hannu, I-pad da laptop da dai sauransu da nufin bibiyarsu don gudun kada su fada cikin sabo.

Samahatul shaikh Yakubi ya ci gaba da cewa dalilinsa a kan haka shi ne cewa bincike na kwakkwafi abu ne da Allah Ta'ala ya haramta a cikin fadinsa: “Kada ku yi binciken kwakkwafi”, Hujurat aya ta 12. Koda yake ta yiwu hadafin binciken kwakkwafin ya zama ingantacce to amma dole ne fa hanyar da za a bin ita ma ta zama wacce shari’a ta yadda da ita ce domin (son kaiwa ga manufa ba ya halasta aikata kowane abu) idan dai ta kasance ta sabawa shari’a, koda yake a nan ta hanyar wannan binciken kwakkwafin uba ko uwa za su iya gano wani kuskure a cikin dabi’u da halayen ‘ya’yansu har ma su magance shi, sai dai yin hakan zai janyo masu rashin aminci a tsakaninsu da ‘ya’yan nasu har ta kai ga babu sauran sakin jiki ko wata magana gwari-gwari a tsakaninsu, to kuma shi wannan matakin yana da hadari wanda zai kai ga rushewar kyakkyawar alakar da take tsakanin iyayen da ‘ya’yan nasu.

Amma hanyar da ta dace ita ce sanya ido ga ‘ya’yan cikin lura, gogewa da gwanancewa amma ba tare da wuce gona da iri ga ‘yancinsu ba.

Haka nan ma samahatul shaikh da ya juyo da maganarsa ga su ‘ya’yan a kan kansu ya hore su da yin biyayya ga iyaye da kuma nisantar duk abin da zai jefa su cikin damuwa, tare da duk wani abu wanda zai kawo zargi ko shakku tsakaninsu da iyayen nasu, kamar kulle masu kofa don kar su shigo cikin dakin, ko kuma noke-noke da boye-boye a kan wasu lamurra da sauran ire-iren wadannan wadanda za su jawo shakkar da za ta kai ga iyayen su fara tunanin daukar matakai na tsawatarwa.

Kamar yadda haka hukuncin yake ga ma’aurata, don su ma ba ya halasta ga kowane daya daga cikinsu ya kama bibiyar tare da bincikar kayan dan uwansa don kawai tsammanin faruwar wani abu ko shakka kan wani abu, domin kamar yadda muka fada hakan yana janyo rushewar walwala, aminci da yardar da take tsakaninsu.