Marji’in addini Ayatullahi Yakubi: Ya yi hani a kan dukkan abin da zai haifar da sabani da rarraba.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Marji’in addini Ayatullahi Yakubi: Ya yi hani a kan dukkan abin da zai haifar da sabani da rarraba.
Samahat Marji’in Addini Mai Girma Ayatullah Shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa).
Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh.
Lokaci bayan lokaci a kan samu wasu masu yin batanci da zagi ga ababe masu daraja na addini sukan aibata wannan ko wancan tare da tozarta shi, to mece ce matsayarku a kan wannan yanayin?
Da Sunansa Madaukaki:
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Matsayarmu a game da wannan aiki, a fayyace take kuma shi ne cewa tuni muka yi hani ga aikata shi a cikin bayananmu masu yawa da kuma a cikin munasabobi daban-daban, wannan abin ya sabawa tarihin rayuwar Imamai Ma’asumai (as) da irin fuskantarwarsu ga ‘yan shi’arsu, kuma lallai ne cewa wannan abin yana haifar da rarraba, sabani da rashin jituwa, husuma da jayayya. Lallai Allah Tabaraka wa Ta’ala ya yi hani gare shi a cikin fadinsa: “Kuma kada ku yi jayyya sai hakan ya zama sanadin raunanarku”, (Anfal, aya ta 46). Don haka duk lokacin da abubuwan da suka hada wasu bangarori biyu suka kara yawaita to dole ne ya zama a kara kula da yin takatsantsan, da a ce kuma abubuwan da suka hada mu ba za su iya dunkule mu waje guda ba, to ya kamata makiyinmu wanda ba ya tsaron wata zumunta a tsakaninmu gabaki dayanmu haka nan ba ya tsaron wata amana, ya zama sanadin haduwarmu waje guda mana, hatta ma ba ya ko yin takatsantsan wajen cin fuskar mafi girman abubuwanmu masu tsarki sannan kuma yakan aikata mafi girman laifuka.
Kuma Allah shi ne wanda ake neman taimako a wajensa a kan abin da ku ke siffantawa.
Muhammad Al-Yakubi
15/2/1436 AH
5/4/2015 AD