Daddatse Gawar Mamaci
Daddatse Gawar Mamaci
Samahat Shaikh Ayatullah Al Uzma Yakubi Allah Ya Albarkaci Rayuwarku Ya Tsawaita Maku Ita.
Mene Ne Ra’ayinku A Kan Wannan Tambayar Mai Zuwa:
Mene ne hukuncin shari’a a kan daddatsa gawar mutum mai laifi, idan jami’an shari’a masu alkalanci na musamman kebantattu a kan bincike irin wannan suka ba da umarni ga sashen likitanci da kiwon lafia domin su yi bincike a kan gawar, ko kuma abin da aka fi sani da daddatsa gawar mutum domin a san hakikanin dalilin da ya sabbaba mutuwarsa?
Da sunansa Madaukaki:
Ba ya halatta a daddatsa gawar mamaci wato a datse wani bangaren jikinsa ko wasu bangarorin jikinsa domin alfarmar da yake da ita a halin yana mace daidai take da alfarmarsa a yayin da yake a raye, to sai dai idan har ya zama akwai wata maslaha mai muhimmanci wacce za ta jawo a daddatse wasu gabobinsa din kamar tabbatar da kubutar wanda ake tuhuma ko biyan hakkin wani mutum, ko domin rarrabewa a tsakanin mutum biyu masu husuma, ko tunkude wata babbar cuta, kuma idan ya zama dole tabbatuwar hakan ta dogara ne kawai ta hanyar daddatse gawar, to ya halatta.
Amma indai domin kawai ana son a san dalilin da ya sabbaba mutuwar ne, wannan ko kadan ba ya zama hujjar da za ta jawo a daddatse gawar mamaci, kuma lallai mun fadakar da hukumomin da abin ya shafa dangane da wajabcin kiyaye ka’idodin shari’a, tare da takaituwa a yayin daddatsewar ga wuraren da shari’a ta ba da dama a kansu, da zarar ba hakan aka yi ba, to wadanda suka aikata sabanin haka sun aikata mummunan laifi, muna neman tsari daga Allah. Wanda ya datse wata gaba ta mamaci kai tsaye ba tare da kiyaye hukuncin shari’a ba to shi ne zai dauki nauyin biyan diyyar wannan danyen aiki da ya aikata ga ‘yan uwan mamacin, wacce an riga an fadi kwatankwacin abin da za a bayar din na diyya a cikin babin diyya (kitabul diyyat) a cikin littafin Risalatul Amaliyya.
Muhammad Al-Yaqubi
28 ga Muharram 1436 AH. 21/11/2014 AD