SHAFIN FARKO | | TAMBAYOYI
TAMBAYOYI

Raba labarai

Bayar Da Shawarwari Da Umarni Ga Sha’anin Tafikarwar Hukuma

8- A cikin bayananku da khudubobinku ana fahimtar cewa kuna fitar da wadansu shawarwari ga muminai da suke fita wajen fatawoyi, kuma kamar kuna ishara a kan tilascin yinsu, to shin wadannan shawarwarin umarni ne da dole a zartar da su a sha’anin hukuma?

Kuma mene ne bambancin tsakaninsu da shawarwarin da kuke gabatarwa ga ma’aikata a cikin sakonninku?

 

Da Sunansa Madaukaki

Babu bambanci a cikin wajabcin lizimtuwa da hukuncin da ya gangaro daga bangaren shari’a da shigowarsa kai tsaye ko kuma a cikin jawabai da kuma khudubobi masu tarin yawa. 

Raba labarai

Sanya Safa Ga Mata

Shin sanya safa ga mata a gaban ‘yan uwan mijinta na daga cikin abin da ya kunshi saka hijabi na shari’a tare da cewa suna zaune ne a gida guda?

Da Sunansa Madaukaki

A cikin hakan akwai yin ihtiyadi domin rufe wurin da ya karu na daga cikin yankin da ya halasta a bayyanar da shi wanda shi ne tafin kafa.

Raba labarai

Hukuncin Kifin Da Ba Shi Da Bawo (Bawon Bayan Kifi)

Shin ko za ku ambata mana dalilan karahanci ko haramci cin kifi irin wanda ba shi da bawo din nan?

 

Da Sunansa Madaukaki

Dalili ingantacce ne ya yi nuni ga haramcin cin kifi wanda ba shi da bawo, amma mai ya sa aka haramta to (fa ka sani) Allah Ta’ala ya ce: “Ba a tambayarsa ga abin da yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu” (suratul Anbiya’i: 23). 

Raba labarai

Hukuncin Iyaye Masu Hana ‘Ya’yansu Yin Azumi

Mene ne hukuncin iyaye maza da mata wadanda suke hana ‘ya’yansu wadanda ba su jima da balaga ba yin azumi da hujjar cewa har yanzu su yara ne kanana kuma wai ba za su iya yin azumin ba? Kuma mene ne ya hau kan ‘ya’yan game da wannan?

 

Da Sunansa Madaukaki

Wannan aikin nasu bai halasta ba kuma ya sabawa tsantseni, domin lallai wannan yana daga cikin abubuwa masu sauki a addini sannan wajibi ne a kansu su dinga karfafa ‘ya’yansu maimakon raunana su, su dinga koyar da su yin azumin tun kafin su balaga ta yadda lokacin da suka balaga zai zama mai sauki a gare su. Amma ga su ‘ya’yan to wajibi ne a kansu su dauki azumi, domin babu biyayya ga abin halitta a cikin sabawa mahalicci, kuma idan aka tilasta masu cin abinci to dole ne su yi ramuwa daga baya. Amma idan tsoron da ake ji na yin azumin tabbatacce ne, to wannan zai iya zama dalilin da za a ajiye azumi, amma ba wajibi ba ne a ci gaba da wannan aikin koda akwai cutuwar ba.   

Raba labarai

Halascin Kallon Mace Ga Wanda Ya Yi Nufin Aurenta

Shin ko yana daga cikin abubuwan da suka halasta ga namijin da yake son ya auri wata mace ya kalli jikinta ba tare da hijabi ba, ma’ana tun kafin auren? Kuma wadanne gabobi ne na jikin nata yake iya gani kafin auren?

 

Da Sunansa Madaukaki

Kallon fuskarta da tafukan hannayenta ne kawai aka yarje masa, domin su ne ke hakaito masa sauran sassan jikinta, amma zai iya wakilta wata mace daga cikin danginsa domin ta duba masa jikinta baki daya idan ya so hakan ko kuma idan yana tsoron akwai wata illa a jikin nata. 

Raba labarai

Tafsirin Aya Ta Shida A Cikin Suratul Jasiya

A cikin suratul Jasiya a ayarta ta shida wacce take magana kamar haka: “Wadancan ayoyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya. To da wane labari bayan (na) Allah da ayoyinsa suke yin imani?” (Suratul Jasiya: 6). Tambayata a nan: Ina da wani aboki wanda yake ikirarin cewa lallai wannan ayar ita ce babban dalili yankakke a kan cewa babu wata bukata ga hadisi. To ta yaya zan iya fahimtar ko fassara wannan ayar?

 

Da Sunansa Madaukaki

Bukatuwa zuwa ga sunnah madaukakiya abu ne da yake tabbatacce a cikin Qur'ani mai girma Allah Ta'ala ya ce: “Kuma abin da Manzo ya zo maku da shi, to ku rike shi, kuma abin da ya hane ku, to ku bar shi”, kuma Allah Ta'ala ya ce: “To, aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba har sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya saba a tsakaninsu”, a wani guri kuma Allah ya ce: “Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa. (Maganarsa) ba ta zamo ba face wahayi ne da ake aikowa”, haka nan ma Allah Ta'ala ya ce: “Kuma da zai fadi wata magana ya jingina ta gare mu. Da mun kama shi da dama. Sannan lallai ne da mun katse masa jijiyar zuciyarsa”.

Da a ce babu wata bukata ga Annabi da hadisansa, idan dai haka ne to mene ne dalilin da ya sa Allah Tabaraka wa Ta’ala ya aiko shi ya kuma hado shi da wahayi alhali zai iya wadatuwa da saukar da Qur'anin zalla.    

Raba labarai

Zamantakewar Mace Da Miji Mai Bayyanar Da Alfasha

Yaya zan yi a matsayin mace musulma kuma uwar yara in yi ma’amala da mijin da ba zai yiwu a siffanta shi da mutum musulmi ba a ma’anar musulunci ta hakika? Domin mutum ne da ba ya sallah da azumi kuma shi mai bayyanar da sabo a fili ne?

 

Da Sunansa Madaukaki

Idan dai har bai gaza wajen ba ku wajen zama da sauran bukatun rayuwa ba, sannan kuma bai tilasta maku barin wajibai ba – kamar salloli biyar na yau da kullum da azumin watan Ramadana – haka nan ma bai tilasta maku a kan aikata haramun ba – kamar ya saka ku cire hijabi a gaban wadanda ba muharramanku ba; to ku ci gaba da yin hakuri da shi, ku dinga yi masa nasiha cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, kada ku fada masa maganar da za ta tunkuda shi ga dawwama a kan sabon.

Kuma wani abu mai muhimmanci shi ne ki yi kokarin tarbiyyantar da ‘ya’yanki tarbiya mai kyau ki dinga zama da su kina tattaunawa da su a kai a kai har ki samu natsuwa da su. Da fatan Allah ya tallafa miki a kan wannan nauyi da ya hau kanki.

Raba labarai

Mace Mai Bibiyar Rayuwar Miji

Shin ko mace tana da hakkin ta hana mijinta zuwa shagon shan coffee da kuma ma’amala da abokansa?

 

Da Sunansa Madaukaki

A shari’ance ba ta da hakkin ta hana shi yin duk wani aiki madamar ba shari’a ce ta haramta masa ba, kuma ina da tabbacin maganin wannan ba a hanawar yake ba, a’a sai dai a cikin samar da kusanci da nuna kauna da tsare gaskiya da fito da komai a sarari ba tare da noke-noke ba.

Raba labarai

Aiki Tare Da Marassa Kula Da Addini

Kasantuwar rashin wadatuwar samun aiki, na yi aiki a wajen wani mai sayar da shayi da daddare, sai dai mutumin ba shi da kirki, kuma mutum ne mai yasassun maganganu, kuma na sha yi masa nasiha ba sau daya ba ba sau biyu ba, amma ina ya kafe a kan dabi’arsa; shin yin aiki tare da shi a irin wannan halin ya dace kuwa?

 

Da Sunansa Madaukaki

Babu hani ga yin aiki da shi, sai dai ka ci gaba da yi masa wa’azi da irshadi, da sannu wa’azin zai zamo wani abu wanda zai dinga kai-komo a ransa, haka nan yana da karfi ta yadda tasirinsa zai dinga bibiyarsa, kuma ni ma zan dinga saka ku a addu’ata.

 

Raba labarai

Sakin (Aure) ta waya (telephone)

Shin yana halasta a gudanar da shedar sakin aure ta hanyar kiran waya ga wanda ke nesa da gida misali?

 

Da Sunansa Madaukaki

An shardanta ga masu shedar (sakin aure) su saurara su ji furucin sakin (siga) daga bakin mai sakin a lokaci guda a tare, to idan hakan zai hakkaku ta hanyar hanyoyin sadarwar zamani to babu laifi madamar akwai amincin cewa wata yaudara ko jirkita lamarin da sauransu ba za su faru ba. 

1 2 3 4 5
total: 47 | displaying: 11 - 20

OFISHIN MARJI’IN ADDINI

SHAIKH MUHAMMAD YAQUBI (ALLAH YA TSAWAITA KWANANSA) AIKO DA TAMBAYOYINKA

NAJAF MAI TSARKI