Aiki Tare Da Marassa Kula Da Addini
22/07/2020 09:21:00 |
30/ZULKI’IDA/1441|times read : 401
Aiki Tare Da Marassa Kula Da Addini
Kasantuwar rashin wadatuwar samun aiki, na yi aiki a wajen wani mai sayar da shayi da daddare, sai dai mutumin ba shi da kirki, kuma mutum ne mai yasassun maganganu, kuma na sha yi masa nasiha ba sau daya ba ba sau biyu ba, amma ina ya kafe a kan dabi’arsa; shin yin aiki tare da shi a irin wannan halin ya dace kuwa?
Da Sunansa Madaukaki
Babu hani ga yin aiki da shi, sai dai ka ci gaba da yi masa wa’azi da irshadi, da sannu wa’azin zai zamo wani abu wanda zai dinga kai-komo a ransa, haka nan yana da karfi ta yadda tasirinsa zai dinga bibiyarsa, kuma ni ma zan dinga saka ku a addu’ata.