Zamantakewar Mace Da Miji Mai Bayyanar Da Alfasha
Zamantakewar Mace Da Miji Mai Bayyanar Da Alfasha
Yaya zan yi a matsayin mace musulma kuma uwar yara in yi ma’amala da mijin da ba zai yiwu a siffanta shi da mutum musulmi ba a ma’anar musulunci ta hakika? Domin mutum ne da ba ya sallah da azumi kuma shi mai bayyanar da sabo a fili ne?
Da Sunansa Madaukaki
Idan dai har bai gaza wajen ba ku wajen zama da sauran bukatun rayuwa ba, sannan kuma bai tilasta maku barin wajibai ba – kamar salloli biyar na yau da kullum da azumin watan Ramadana – haka nan ma bai tilasta maku a kan aikata haramun ba – kamar ya saka ku cire hijabi a gaban wadanda ba muharramanku ba; to ku ci gaba da yin hakuri da shi, ku dinga yi masa nasiha cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, kada ku fada masa maganar da za ta tunkuda shi ga dawwama a kan sabon.
Kuma wani abu mai muhimmanci shi ne ki yi kokarin tarbiyyantar da ‘ya’yanki tarbiya mai kyau ki dinga zama da su kina tattaunawa da su a kai a kai har ki samu natsuwa da su. Da fatan Allah ya tallafa miki a kan wannan nauyi da ya hau kanki.