Tafsirin Aya Ta Shida A Cikin Suratul Jasiya

| |times read : 442
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Tafsirin Aya Ta Shida A Cikin Suratul Jasiya

A cikin suratul Jasiya a ayarta ta shida wacce take magana kamar haka: “Wadancan ayoyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya. To da wane labari bayan (na) Allah da ayoyinsa suke yin imani?” (Suratul Jasiya: 6). Tambayata a nan: Ina da wani aboki wanda yake ikirarin cewa lallai wannan ayar ita ce babban dalili yankakke a kan cewa babu wata bukata ga hadisi. To ta yaya zan iya fahimtar ko fassara wannan ayar?

 

Da Sunansa Madaukaki

Bukatuwa zuwa ga sunnah madaukakiya abu ne da yake tabbatacce a cikin Qur'ani mai girma Allah Ta'ala ya ce: “Kuma abin da Manzo ya zo maku da shi, to ku rike shi, kuma abin da ya hane ku, to ku bar shi”, kuma Allah Ta'ala ya ce: “To, aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba har sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya saba a tsakaninsu”, a wani guri kuma Allah ya ce: “Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa. (Maganarsa) ba ta zamo ba face wahayi ne da ake aikowa”, haka nan ma Allah Ta'ala ya ce: “Kuma da zai fadi wata magana ya jingina ta gare mu. Da mun kama shi da dama. Sannan lallai ne da mun katse masa jijiyar zuciyarsa”.

Da a ce babu wata bukata ga Annabi da hadisansa, idan dai haka ne to mene ne dalilin da ya sa Allah Tabaraka wa Ta’ala ya aiko shi ya kuma hado shi da wahayi alhali zai iya wadatuwa da saukar da Qur'anin zalla.