MATAKAN DA SUKA DACE A DAUKA DANGANE DA GABATOWAR JUYAYIN ARBA’IN:

| |times read : 710
MATAKAN DA SUKA DACE A DAUKA DANGANE DA GABATOWAR JUYAYIN ARBA’IN:
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

MATAKAN DA SUKA DACE A DAUKA DANGANE DA GABATOWAR JUYAYIN ARBA’IN:

Marji’in addini shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya karfafa wajabcin yin duk wani abu wanda zai faranta ran Imam Mahdi (as), kuma zai gamsar da shi, kuma zai kai ga samun kusanci zuwa gare shi, kuma zai zama sanadin gaggautowar bayyanarsa, kuma zai yi shimfida ta shirye-shiryen jiran ranar zuwansa wato ranar da aka alkawarta ta bayyanarsa da izinin Allah Ta'ala, sai hakan ya za ma cikawa ta wannan kururuwa tare da daga muryoyi sama na miliyoyin jama’a suna masu yin addu’a da roko da magiya a wajen Allah Ta'ala na ya gaggauta bayyanar Waliyyinsa mai girma kuma Hujjarsa a cikin halittunsa (rayukan dukkan talikai su zama fansarsa). Lallai samun miliyoyin muryoyi suna masu roko a kan wata bukata guda daya kuma a cikin ranakun Allah Ta'ala (masu tsarki) ba roko ne da cikin sauki za a ki karbarsa ba. A sakamakon haka ne ma shaikh ya ambato wasu nukudodi wadanda ya kamata a yi la'akari da su:

1- Kusanto da ma’anar nan cewa Allah yana tare da ku; kamar yadda ya zo a Qur'ani: “Kuma yana tare da ku a duk inda kuka kasance” (Hadid: 4). Da dukkan ma’anar da take bayarwa na albarkoki, na farkonsu kuwa shi ne tsantseni wajen barin abin da Allah Subhanahu ya haramta, sannan sai taimako da rangwame da kyautatawa, sannan sai kuma kasantuwa tare da Allah Ta'ala din da kuma wadansu abubuwan da muka ambata a cikin tafsirin wannan aya mai girma[1].

2- Tsayar da sallah da jajircewa a kanta da yinta a kan lokaci daidai gwargwadon iko, kuma abin da aka fi so shi ne yinta a masallaci cikin jam’i idan har da akwai ikon yin hakan.

3- Takaita yawan sabani, musu da jayayya da nisantar kaskantar da waninka ko rusa darajarsa da batanci a cikin zantuka, sannan sai a yi kokarin warware matsaloli cikin hikima kamar dai yadda Allah Ta'ala yake so kuma yake yarjewa.

4- Kyautata wa iyaye da yi masu biyayya, sada zumunci ga ‘yan uwa, kyautatawa ga makwabta da yin kyakkyawar ma'amala tare da kowa da kowa.

5- Kame hannaye, harshe, ciki da ido tare da tsarkake su daga aibobi, sannan kuma da kamewa daga sha’awace-sha’awace da jaraba.

6- Dagewa wajen fahimtar addini, kulla alakoki masu kyau da makarantun Hauzozin ilimi ta duk hanyar da ta samu ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani.

7- Yin sa’ayi da kokari wajen biyan bukatun jama’a da faranta masu rayukansu da kuma nisantar cutar da su.

8- Taimakon mabukata, musamman ma masu kamun kai daga cikinsu da daukar nauyin marayu na abin da ya shafi bukatun rayuwarsu da tarbiyyarsu da kuma ilmantar da su, sannan da aurar da matasa masu kamun kai daga cikin hakkokin shari'a (dukiyar baitul mali) da dukiyoyin da ake bayarwa don tallafi.

9- Ilmantar da mutane da wayar da su, shiryar da su da nuna masu hanyar da ta dace ga lamurransu na duniya da lahira da warware masu shubuhohin da ake bijiro da su tare da amsa masu tambayoyinsu.

10- Sanya ikilasi a cikin aiki da sauke nauyin da ya hau kanka da gudanar da shi bisa kwarewa tare da kaucewa duk wata gazawa a cikinsa.

11- Kaucewa duk wani wasa da wargi, idan kuma rai ya dan bukaci yin nishadi to babu laifi a yi nishadi daidai gwargwado.

12- Raya tarukan addini da tarayya a cikinsu.

13- Karanta abin da ya sauwaka daga littafin Allah Qur'ani mai girma koda rabin juzi’i a kullum.

14- Tsayuwa da abin da yake mustahabbi ne, musamman sallolin dare koda raka’a daya ce, da wanzuwa cikin alwala a koda yaushe iya yadda mutum zai iya ba tare da an takura kai ba ko kuma tasirantuwa da nauyin da yake kan wasu.

15- Yin addu’a a kullum-kullum ga Imamul Hujja (as) (sananniyar addu’ar nan wato: Allahumma kun li waliyyikal….) da addu’ar (Ya man tuhallu bihi ukadul makarih…) da karanta ziyarar Ashura da ba da sadaka a madadin Imam da kuma sanya wa duk wani aikin da mutane, kungiyoyi ko mu’assasoshi suke yi sunan Imam domin yada ambatonsa mai albarka da karfafa alakar mutane da shi (as).

Kuma an ambata cewa samhatul shaikh (Allah ya tsawaita kwanansa) ya fitar da sanarwa tun a shekarar da ta gabata ya lakaba mata suna da: (Arba’in din Faraj…..daga Ashura zuwa Arba’in)[2] a ranar 8 ga Muharram / 1441, wanda a ciki ya yi kira da a saka jari domin wadannan kwanakin na Arba’in masu alaka da Imam Husain (as), kwanakin da suka fara tun daga Ashura har zuwa ziyarar Arba’in, domin yin kururuwa ga Allah Ta'ala da kaskantar da kai gare shi da kuma tawassuli gare shi domin ya gyara mana lamurramu da suka lalace albarkacin kyautatawarsa da kuma cewa kasantuwar wannan Arba’in din ta dace da irin wannan kururuwa da kaskantar da kai domin irin damfaruwar da ke akwai tsakanin Arba’in da shi kansa Imam Husain (as) da kafa daular adalci ta Allah, kuma saboda cewa Arba’in din Imam tana kawo dukkan alherai kuma jigo ce ta karfi ga dukkan ma’abota shiriya da masu neman kawo gyara. A cikin zancen Imam Sadik (as) ya zo cewa: “Lokacin da azaba ta tsawaita ga Bani Isra’ila, sun yi kururuwa da kuka ga Allah safiya (kwana) Arba’in, sai Allah ya aika zuwa ga Musa da Haruna (as) domin su tseratar da su daga Fir’auna, to sai ya ketarar da su har tsawon shekaru dari da saba’in, haka nan ku ma da za ku aikata to da lallai Allah ya kawo mana dauki da faraji, amma idan ba ku kasance irin haka ba, to lallai lamari zai kai ga wa’adinsa na asali”.

Muna rokon Allah Ta'ala ya datar da mu da ku ga duk abin da zai faranta ran Imamuna Al-Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa) da nisantar duk abin da zai bakanta masa ya kuma sosa masa ransa mai tsarki, lallai (Allah) mai jin addu’a yake.

Ofishin marji’in addini shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwansa).

14 Muharram 1442 AH

3/9/2020 AD         

#Arba’in_MaiCikedaFatanSamunFaraji

#QabasatulMarja’iyyatilRashida

#DagaAshuraZuwa_Arba’in

#Ku_raya al’amuranmu

#YunkurinHusainFarkarwaCe

#QabasatulMarja’iyyatilRashida

 

   

         [1] - https://yaqoobi.com/arabic/index.php/5/1/7418.html

[2] -  https://yaqoobi.com/arabic/index.php/news/6978.html