Tunatarwa Ga Yin Azumi A Ranar Farko Ta Muharram Ana Karbar Addu’a

| |times read : 463
Tunatarwa Ga Yin Azumi A Ranar Farko Ta Muharram Ana Karbar Addu’a
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunansa Madaukaki

Tunatarwa Ga Yin Azumi A Ranar Farko Ta Muharram Ana Karbar Addu’a

Shaikh Saduk ya rawaito a cikin Majalis da Uyunil Akhbar da sanadinsa daga Rayyan ibn Shabib ya ce: “Na shiga wajen Imam Rida (as) a ranar farko ta Muharram sai ya ce: Ya kai Ibn Shabib shin kana azumi kuwa? Sai na ce: a’a, sai ya ce: Lallai wannan ranar ita ce ranar da Zakariyya (as) ya roki Ubangijinsa Mai Girma da Daukaka ya ce: “Ya ce: Ya Ubangijina! Ka ba ni zuriyya dayyiba daga gurinka, lallai ne Kai Mai Jin addu’a Ka Ke” (Aali Imran: 38) Sai Allah ya amsa masa, kuma ya umarci mala’iku suka kira Zakariyya: “Alhali kuwa shi yana tsaye yana sallah a cikin masallaci; (suka ce) lallai ne Allah yana maka bushara da Yahaya” (Aali Imran: 39), don haka wanda ya azumci wannan ranar sannan ya roki Allah Mai Girma da Daukaka, Allah zai amsa masa kamar yadda ya amsa wa Zakariyya (as); (Wasa’ilul Shi’a: 10/469).

Don haka abin da ake nema a wajen mumini da mumina shi ne su yi azumi a ranar Juma’a wacce take ranar farko ga Muharram kuma su yi tawassuli ga Allah Ta'ala domin neman biyan bukatunsu duk yadda suke, amma mafi girman bukatu shi ne neman gaggautowar bayyanar Maulanmu Sahibul Asr wal Zaman (as) da kiyaye shi, ba shi nasara, karfafarsa da kuma addu’ar Allah ya sanya mu cikin masu taimakonsa, masu dafa masa kuma wadanda za su rabauta da samun ceton Annabi (s.a.w.a) da Alayensa (as).

 

Idan ka amsa wannan kira to jefa kuri’arka ta hanyar zabar (Eh) a wannan kewayen da ke kasa: 

https://t.me/yaqoobioffice/4722

#Ku_raya al’amuranmu

#YunkurinHusainFarkarwaCe

#QabasatulMarja’iyyatulRashida

T.me/yaqoobioffice