ranar Ashura

| |times read : 487
ranar Ashura
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

1- Rayuwa Mai Tarin Albarka Ta Shugaban Shahidai (as)

Idan motsawarmu ta wuni guda kadai a cikin rayuwa madaukakiya ta Imam Husain (as) wato ranar Ashura tana bayar da wata natija mai girma irin haka, wacce take haifar da natijoji masu girma masu tasirin da duniya ta shaide su…. To yaya ka ke ganin shekarun rayuwarsa (57) da ya yi masu daraja da a ce za mu karance su a fagage daban-daban (kuma mu aikata su)?

2- Aikin Imam Husain Shi Ne Kawo Gyara:

Lallai shari’ar musulunci wacce take ita ce cikamakon shari’oin da Allah (ya aiko) kuma mafi kammalarsu bai takaita kurum gurin gina mutum da gyaransa kawai ba a’a, lallai shi addini ne wanda dokokinsa da hukunce-hukuncensa suka game dukkan bangarori na al’amuran rayuwar mutane, kuma Imam Husain (as) wanda yake magajin Annabawa mai dauke da sakonsu gabaki dayansa ya ambaci hakan inda ya yi ishara a cikin zantukansa madaukaka ga dukkanin bangarorinsu. Misali a bangaren gina mutum da gyara a kan addininsa ya ce: “Kuma lallai ni ban fito domin dagawa da alfahari ko a matsayin mabarnaci da azzalumi ba a’a, na fito ne kawai domin neman kawo gyara ga al’ummar kakana (s.a.w.a), ina son in yi umarni da kyakkyawa kuma in yi hani ga mummuna, kuma ina son in yi koyi da sirar kakana (s.a.w.a) da ta babana Ali ibn Abi Dalib (as)”. Haka nan ma wajen karfafa dokoki ya ce: “Ni mai kiranku ne zuwa ga littafin Allah da sunnar Annabinsa (s.a.w.a), domin tabbas an kashe sunna kuma an raya bidi’a, kuma idan ku ka ji zancena ku ka yi biyayya ga umarnina, zan shiryar da ku zuwa ga tafarkin shiriya”.  Wato Kenan cewa su wadancan dawagitan sun riga sun kaucewa yin aiki da tsarin mulki (na musulunci), a saboda haka shi Imam (as) yana kiransu ne a kan su dawo wa yin aiki da tsarin mulki – wanda shi ne Qur'ani – da kuma dokokin da suke fassara shi – wato Sunnah madaukakiya – Kuma a bangaren siyasa ta addini da bayanin siffofin wanda ya cancanta da jagoranci, shugabanci da jibintar lamurran al’umma yana cewa: Ina rantsuwa cewa ba wani ne shugaba (imami) ba sai mai aiki da littafin Allah, mai riko da adalci, mai addinantuwa da gaskiya kuma mai kiyaye kansa a gaban zatin Allah”. Sannan Imam (as) ya fayyace cewa abin da ya jawo wannan lalacewar, barnata dukiyar, lalacewar zamantakewar al’ummar, gurbacewar halayen kwarai da addini, gushewar hakkoki da rashin adalci shi ne jibintar da jagororin da a shari’ance ba su da hakkin su jagorancin al’amuran jama’a.

Imam (as) bayan da nauyin jagorantar al’umma da kawo gyara ya hau kansa yana cewa: “Duk wanda ya ga wani shugaba ja’iri, mai halasta haram din da Allah ya haramta, ko kuma mai kin cika alkawarin da ya yi wa Allah, kuma mai sabawa sunnar Manzon Allah (s.a.w.a), sannan yana cutar da bayin Allah ta hanyar sabo da ketare iyaka, sai bai canja shi ta hanyar magana ko aiki ba, to hakki ne a kan Allah ya shigar da shi mashigarsa”. A kokarin fayyace zancensa sai yake cewa: “Kuma kun sani cewa lallai wadannan mutanen sun lizimci biyayya ga shedan kuma sun juya baya ga da’ar Mai Rahama, kuma sun bayyanar da fasadi, sun ketare haddodi, sun yi babakere a kan dukiyar al’umma, sun halasta abin da Allah ya haramta, sun haramta abin da ya halasta. Kuma ni na fi wanina cancanta a kan wannan al’amari saboda kusancina ga Manzon Allah (s.a.w.a)”. A wata ruwayar daban kuma cewa ya yi “Ni ne mafi cancantar in tsayu a kan taimakon addinin Allah, da daukaka shari’arsa da yin jihadi a tafarkinsa, domin kalmar Allah ta zama ita ce madaukakiya”.

Daga littafin: Qabasat min Nuril Qur'an – Al-Qabs 58.

3- Dorewar Nasarar (Tsayuwar Imam) Husain (as)

Imam Husain (as) a yinin Ashura yayin da ya dinga maimaita fadin: (Shin ko akwai wanda zai kawo (mana) dauki) bai kasance yana tsammanin wani taimako daga wadancan dawagitan wadanda Allah ya dusashe hasken shiriya da gyaruwa daga zukatansu ba, a’a kadai yana da bukatar cewa ainahin ita wannan kalma ta wanzu ta zama wata kururuwa mai dorewa a cikin dukkan al’ummomin karni bayan karni har illa masha-Allahu domin su taimaka su dafa masa domin ganin hakkakuwar wannan hadafin nasa, kuma kiran ya ci gaba da wanzuwa madamar akwai fasadi da zalunci, abubuwan da Imam Husain (as) ya tsayu a kansu domin ganin ya gyara su da kuma kawo canjin da ya fi cancanta – kuma wannan kowa zai yi gwargwadon ikonsa ne wajen taimakonsa – ta yiwu wasu su iya tsara shiri na raya ambaton Ashura a yayin da wasu kuma ba hakan za su yi ba, saboda abin nema a wajensu wani abin daban ne, don haka sai a kula da kyau.

4- Taimako Na Hakika Ga Imam Husain (as)

Hakkakuwar wannan za ta faru ne ta hanyar aiwatar da ka’idodin shi wannan yunkurin na Imam Husain (as) da kuma yin yunkuri na ganin tabbatar hadafinsa, lallai ne har yanzu kiran nan na Imam Husain (as) wato (Shin ko akwai wanda zai kawo (mana) dauki) yana nan yana ci gaba da ratsawa a ban kasa, kuma ba yana neman mataimaka masu takobi da makamantansa ba ne a’a, domin kaddarar Ubangiji ta gudana ne a kan ya yi shahada tare da Ahlul Batinsa (as), sai dai yana neman mataimaka ne wadanda za su tallafa masa wajen tsayar da aikinsa da cikasa sakonsa na kawo gyara a cikin al’umma da horo da kyakkyawa da hani ga mummuna da kuma tsayuwa a gaban jagororin bata da azzalumai mabarnata, da kuma ‘yantar da mutane daga damkar dawagitai da shaidanun mutane da aljanu.   

 

5- Yaya Za Mu Iya Kasancewa Cikin Ma’abota (Ya Kaitonmu! Da Mun Kasance Tare Da Ku)?

Dukkan mu muna ambaton Imam Husain (as) da sahabbansa masu biyayya da harsunanmu da dukkan samuwarmu muna cewa: (Ya kaitonmu! Da mun kasance tare da ku, don mu rabauta rabo mai girma), kuma wani abin damuwa shi ne cewa mu ba mu samu kanmu cikin wadanda suka rayu da Ma’asumai (as) ba, ba mu samu wannan daukakar ta ganawa da su ba, ba mu rabauta da taimakonsu ba har mu kwankwadi zakin shahada a gabansu ba; alhali kuma mu mun yi imani a kan cewa tabbas Allah adali ne yana bayar da dama wadatacciya ga bayinsa har su iya samun kusanci gare shi da ita, to shin Allah Ta'ala ya so wa mutanen wancan karnin wannan garabasar ce mu kuma ya haramta mana ita? Wannan ya sabawa waccan hakikar tabbataciya (ta adalcin Allah), to mece ce damar mu wacce ta dace da hakan? Ita ce tsayar da wajabcin yin horo da kyakkyawa da hani ga mummuna, daga cikin kalmomin Amirul Muminina (as) yana cewa: “Ayyukan bayi dukkansu, da jihadi a kan tafarkin Allah ba komai ba ne ba idan aka kwatanta su da horo da kyakkyawa da hani ga mummuna sai kamar numfasawa a cikin teku mai zurfi”.