Marji’in Addini Yaqubi: Yin Tarurrukan Addini na Ashura a Wannan Yanayi na Annobar (Korona)

| |times read : 314
Marji’in Addini Yaqubi: Yin Tarurrukan Addini na Ashura a Wannan Yanayi na Annobar (Korona)
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunansa Madaukaki

Marji’in Addini Yaqubi: Yin Tarurrukan Addini na Ashura a Wannan Yanayi na Annobar (Korona)

Babu ko shakka raya al’amarin Ashura yana daga cikin manya-manyan tarurruka na addini, wanda a albarkacin sadaukarwa da tasirinsa zama shi ne wanda ya kiyaye wanzuwar hakikanin koyarwar addini da tabbatuwarsa a cikin zukatan muminai da dawo da mutane zuwa ga Allah Ta'ala, kuma wannan shi ne mafi kololuwar girma na tarurrukan wajibi a addini.

A saboda haka raya al’amarin Ashura da muhimmantar da shi misdaki ne mafi bayyana a wannan ayar da Allah Ta'ala ke fadin: “Kuma wanda ya girmama tarurrukan ibada na ambaton Allah, to lallai wannan din suna daga cikin taqawar zukata” (suratul Hajj: 32).

Sai dai barkewar annoba wacce yanzu kusan kowace kasa ke fama da ita kuma miliyoyi suka kamu da ita har ta kai ga hukumar lafiya ta duniya ta kirata da wani bala’i mai halakarwa, to wannan yana wajabta mana a shari’ance da a hankalce a babin wajabcin tunkude cutarwa daga kai da kuma sauran jama’a mu lizimci tsare-tsaren kiwon lafiya wadanda suke karewa ga fadawa cikin kamuwa da annobar da yaduwarta.

A saboda haka ya wajaba ga mumini ya kiyaye tsare-tsaren samar da tazara, sanya takunkumi (face mask), sanya safar hannu, sassaka makari a wurare (kamar a shaguna da makamantansu), gujewa cunkoson jama’a ba tare da bayar da tazara ba a yayin tarurrukan Ashura da sauran tarurruka na addini. Idan kuma an samu na’urori masu auna zafin jiki a wadace to a kyautata gudanar da bincike mai zurfi, da tabbatar da ingancin lafiyar jama’a tare da tabbatar da cewa lallai an shaida cewa mutum yana da ingantacciyar lafiyar da zai yiwu a ba shi izinin shiga wuraren da ake taron.

Idan kuma muminai ba su da lamunin samun kayan aikin da za su iya kiyaye lafiyar jama’a to su takaita tarurrukansu a gidajensu a tsakankanin iyalansu da kuma wadatuwa da sauraren jawaban malamai masana ta hanyoyi daban-daban wadanda cikin falalar Allah Ta'ala muna da hanyoyin sadarwar zamani masu yawa a wadace.

Kuma su dage wajen karanta ziyarar Ashura a kullum domin mujarraba ce wajen samun biyan bukatu da tunkude bala’oi da warware mas’aloli da samun lada da kuma uwa-uba samun ceton Ma’asumai (as) a lahira.

Kuma ka da mu gafala ga sauran nau’oin hanyoyin raya ambaton Abu Abdillah Hasuin (as) wanda ambaton nasa zai iya kasancewa ta hanyar bayar da jini kyauta, tallafawa wadanda suka kamu da wannan annoba, ziyartar wadanda suka kamu kuma aka kaurace masu a gidajensu, aika masu da na’urorin shakar iska a gidaje da asibitoci, samar da magunguna, faranta wa marayu (yi masu alheri), yin ta’aziya da jaje ga wadanda ke cikin halin kunci da tallafa wa mabukata, ta yadda mutuncinsu zai wanzu duk domin tunawa da ambaton Imam Husain (as). Haka nan ma ana son a dinga rarraba takardu (masu kunshe da bayanai a kan Ashura), kafa alluna a kan tituna masu dauke da kalmomi da hadisan Imam Husain (as) domin al’umma ta rayu cikin haske da shiriyar da ke cikin maganganun. Sannan zai yiwu a yada ambatonsa ta hanyar zanen hotunan katun-katun masu koyar da hanyoyin kawo gyara da magance halaye marassa kyau da al’umma ke zaune a ciki, hotunan ya zama suna nuni ga hadafin da ya sa Imam Husain (as) ya fito wanda shi ne tsayar da wajabcin nan na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

Lallai Irakawa a farko-farkon bullar wannan annoba a farkon kamawar watan Rajab da suka jaraba kula tare da kiyaye bin umarnonin shari’a da na kiwon lafiya, sai ya zama annobar ba ta iya yin tasiri a kasar ba, kuma har ya zama abin da kasar take alfahari da shi a gaban kasashen duniya, har ta kai ga kungiyoyin kasa da kasa suna tambayar wai shin mene ne sirrin da ya sa wannan annobar ba ta yadu a kasar Iraki ba, tare da cewa kasashen da suke fama da ita suna kewaye da ita kuma hakan ya ci gaba da gudana har na tsawon wata uku, sai daga baya abin ya zo ya fi karfinmu aka samu sassabwa a lokacin idin karamar sallah, daga nan fa adadin ya ketare iyaka mai hadarin gaske, kuma ga kasar Iraki a wani yanayin da ba za ta iya magance irin wadannan bala’oin ba saboda yawan masu raunukan da ke zubar jini.

Muna rokon Allah Ta'ala ya yaye mana dukkan cututtuka kuma ya albarkace mu da lafiya a cikin lamurranmu ya kuma datar da mu ga yin da’a a gare shi da samun yardarsa domin shi, shi ne majibincin ni’imomi.

 

Muhammad Al-Yaqubi

19/Zulhijja/1441 AH

9/8/2020 AD