Kamanceceniya A Tsakanin Assiddika Addahira Fatimaul Zahra (as) Da Sayyida Maryam ‘Yar Imran

| |times read : 913
Kamanceceniya A Tsakanin Assiddika Addahira Fatimaul Zahra (as) Da Sayyida Maryam ‘Yar Imran
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Kamanceceniya A Tsakanin Assiddika Addahira Fatimaul Zahra (as) Da Sayyida Maryam ‘Yar Imran*

Mu – mabiya Ahlul Bait (as) – muna da wata alaka kebantacciya ta musamman da Assiddika Addahira sayyida Maryam ‘yar Imran domin cewa lallai ita tana da wadansu kamanceceniya da sayyida Addahira Fatimatul Zahra (as) a cikin da yawa daga siffofi tare da kiyaye fifiko na sayyida Zahra (as) a kanta. Domin ta dosano haskenta ne daga hasken shugabar matan talikai sayyida Fatimatul Zahra (as), ta kasance tana walwali na haske a mahallin ibadarta (mihrab dinta), kamar yadda ya zo a ruwaya daga Imam Bakir (as): “Ta kasance mafi kyawon mata, kuma ta kasance idan tana sallah sai mihrab dinta gaba dayansa ya dinga haskakawa da haskenta”[1].

Haka nan kuma Maryam ta kasance Muhaddasa (wacce mala’iku ke magana da ita) – wannan sunan kuma yana daga cikin sunayen sayyida Fatimatul Zahra (as) – mala’iku suna magana da ita kamar yadda Allah Ta'ala ya ba da labari game da hakan: “Kuma a lokacin da mala’iku suka ce ya Maryam! Lallai ne Allah ya zabe ki, kuma ya tsarkake ki, kuma ya zabe ki (ya fifita ki) a kan matan talikai” (suratu Ali-Imran: 42) “Sai muka aika ruhinmu zuwa gare ta” (suratu Maryam: 17). Kuma an ruwaito daga Imam Sadik (as) ya ce: “An ambaci Fatima (as) da Muhaddasa ne kurum don mala’iku sun kasance suna saukowa daga sama sai su dinga kiranta kamar yadda suke kiran Maryam ‘yar Imran, suna masu fadin ya Fatima lallai Allah ya zabe ki ya tsarkake ki kuma ya zabe ki (ya fifita ki) a kan matan talikai. Ya Fatima ki kaskantar da kanki ga Ubangijinki, kuma ki yi sujjada kuma ki yi ruku’i tare da masu ruku’i. Sai ta dinga yin hira da su su ma suna yin hira da ita. A wani dare sai take ce masu: Shin wai ba Maryam ‘yar Imran ce mafificiya a kan matan talikai ba? Sai suka ce: Lallai Maryam ta kasance shugabar matan zamaninta, ke kuma Allah madaukakin sarki ya sanya ki shugabar matan zamaninki da zamaninta, kuma shugabar matan farko da na karshe”.[2]

Idan muka dawo ga siffar ‘tadhir’ lallai dangane da wannan siffar Allah Ta'ala a hakkin Maryam ya ce “Ya tsarkake ki”, haka kuma ya saukar da ayar tadhir a hakkin Ahlul Bait (as): “Kadai Allah na nufin ya tafiyar da kazanta daga gare ku, ya mutanen babban gida! Kuma ya tsarkake ku tsarkakewa” (suratul Ahzab: 33).

A cikin siffar zabi da shugabanci kuma, ya sanya Maryam shugabar matan talikai, kuma Fatima (as) ma haka, tare da bambancin da ke akwai wanda a ruwayar Mufaddal bn Umar ya ruwaito inda ya ce: “Na tambayi Abu Abdillah – Imam Sadik (as) – cewa ba ni labari game da fadin Manzon Allah (s.a.w.a) a game da Fatima cewa ita shugabar matan talikai ce, shin ma’ana shugabar matan zamaninta kenan? Sai ya ce: Wannan game da Maryam kenan domin ita ta kasance shugabar matan zamaninta ce, amma ita Fatima shugabar matan talikai ce na farkonsu da na karshensu[3]. Idan kuma ka yi riko da tsagwaron fadinsa Ta’ala cewa: “A kan matan talikai” ba ya nuni ga takaituwa ga zamaninta kamar yadda ya zo a cikin Al-Mizan, sai mu ce eh haka ne, sai dai zabin an takaice shi da wasu ayoyi wadanda suka yi masa iyaka kamar ayar da ta yi magana a kan daukar cikinta da haihuwarta, yayin da zabin da aka yi wa Fatimatul Zahra (as) mudlaki ne wannan kuma shi ne bangaren da ya bambanta tsakanin zabin da aka yi masa dori da harafin (ala) kamar yadda yake ga zabin da aka yi wa Maryam da kuma zabi mudlaki domin shi ((zabin da aka yi wa dori da harafin (ala) yana bayar da ma’anar gabatuwa ne amma ba ya bayar da ma’ana ta mudlaki wanda yake fa’idantar da ma’anar sallamawa, to kuma a kan haka zabin da aka yi mata a kan matan talikai shi ne gabatuwarta a kansu)). A saboda haka gabatuwar Maryam ya kasance ne a wasu bangarori ((ta yadda bai game dukkan bambance-bambance tsakaninta da sauran matan ba sai a sha’aninta mai ban mamaki na haihuwar Al-Masihu (as); kuma wannan shi ne bangaren daukakarta da gabatuwarta a kan matan talikai))[4].

Amma haihuwar Ma’asumai masu tsarki (as) kuwa; to lallai Allah Ta'ala ya tsare su daga shaidan jefaffe, ya zo a hadisin Amirul Muminina (as) a lokacin aurensa da Fatima (as) da addu’ar da Annabi (s.a.w.a) ya yi gare su inda ya ce: “Mike da sunan Allah ka ce: Tare da albarka daga Ubangiji, abin da Allah ya so (shi ke tabbata) kuma babu wani karfi face a wajen Allah, kuma hakika na dogara ga Allah – sai ya zo wajena ya zaunar da ni a kusa da ita sannan ya ce: Ya Ubangiji! Hakika su ne mafi soyuwar halitta a gare ni to ka so su, ka sanya albarka a cikin zuriyarsu, ka sanya wa zuriyar mai kariya (maigadi), kuma lallai ni ina nema masu tare da zuriyarsu tsari a wajenka daga shaidan jefaffe”[5].

Haka kuma dangane da arzikin da yake zo mata a mihrabinta daga Allah Ta’ala; an samo a wata ruwaya daga babban sahabi Huzaifa bn Yamani game da wani abinci da Annabi (s.a.w.a) tare da sahabbansa suka samu a gidan Fatima alhali ba su da labarin irinsa kafin nan, har zuwa inda ya ce (sai Annabi (s.a.w.a) ya mike ya shiga wajen Fatima (as) sannan ya ce: “Daga ina kuma wannan ya zo gare ki?” Sai ta amsa masa da cewa alhalin muna sauraron tattaunawar tasu; “Daga wurin Allah yake, lallai ne Allah yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba”. Sai Annabi (s.a.w.a) ya tashi ya fita yana mai fadin: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda bai karbi raina ba sai da na gani ga ‘yata abin da Zakariyya ya gani ga Maryam domin ya kasance idan ya shiga wajenta a Mihrabi yana ganin arziki (abinci) a wajen sai ya ce: “Ya Maryam! Daga ina kuma wannan ya zo gare ki?” Sai ta ce: “Daga wurin Allah yake, lallai ne Allah yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba”[6].

Zan nakalto wadannan babobin wakar domin suna burgeni a ciki akwai kamanceceniya wacce ke tsakanin Assidikatul Kubra Fatimatul Zahra (as) da Assidika Maryam (as):

In kila Hauwa’u kulta Fatimu fakhruha

                                                                Au kila Maryamu kultu Fatimu Afdalu

Afa hal li Maryama walidun ka-Muhammadin

                                                            Am hal li Maryama mislu Fatima ashbalu

Kullun laha indal wiladi halatun

                                                      Fiha ukulu banil Basa’iri tazhalu

Huzi linakhlatiha iltajat fatasakadat

                                                           Rudban janiyyan fahiya minhu ta’akulu

Waladat bi Isa wa hiya gairu muru’atin

                                                          Anna wa harisuhal sirriyyil absalu

Wa ilal jidari wa safhatil babi iltajat

                                                        Bintul Nabiyyi fa’askadat ma tahmilu

Sakadat wa askadatil Janina wa haulaha

                                                                   Min kulli zi hasabin la’imin jahfali

Haza ya’anifuha wa zaka yadu’uha

                                                            Wa ya rudduha haza a haka yarkulu

Wa amamaha asadul aswadi yakuduhu

                                                           Bil habli kunfuz hal hakaza ma’adhalu

                                                          Tashku ila Rabbil sama’i wa ta’ulu

                                                          Bi shikayatin minhal sama’u tazalzalu[7].

  

        An buga wannan jawabin a cikin mujallar Sadikin fitowa ta 202 shafi na biyu wacce aka wallafa a ranar 27 ga Zulki’ida 1441 AH.

[1] Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an: 2/33, daga tafsirin Ayashi: 1/193.

[2] Ilalul Shara’ii: 1/216, da Tafsiri Nurul Saqalain: 1/337.

[3] Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an: 2/216, hadisi na 7 daga Ma’anil Akhbar na Saduk: 107, hadisi na 1.  

[4] Al-Mizan fi Tafsiril Qur'an: 3/218.

[5] Amalil Shaikh Dusi: 40, da Tafsiri Nurul Saqalain: 1/333.

[6] Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an: 2/216, daga Amalil Shaikh Dusi: 2/227.

[7] Diwanul Shaikh Muhsin Abul Hub Al-Kabeer / shafi na 128.