Fa’idar Maimaita Kissoshi A Cikin Qur'ani

| |times read : 487
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Fa’idar Maimaita Kissoshi A Cikin Qur'ani

7- Bayar da magani tare da maimaitawa a kai a kai da rashin gamsuwa ga bayarwar sau daya kurum a yayin da aka fuskanci yin gyara na wani hali wanda ya kauce daga hanya ko toshe wata gazawa ko magance wani kuskure da al'umma ke fama da shi ko gyaran wata akida da suluk dinsu, alal misali za ka samu kissoshin wasu Annabawan an maimaita su sau gomomi kuma kowane zuwa da kissar yana da tasa fa’idar, tasiri da kuma rawar da yake takawa a cikin isar da sako kuma yana barin gurbin da wanda waninsa ba irin wannan yake bari ba, duk da yake gabaki dayansu kusan duk abu daya suka kunsa.  

Yanzu a yayin da muke son tattaunawa game da tabarruji da fajircin mace a gaban namiji da mayar da kanta shaidaniya wanda hakan yake kangewa daga ambaton Allah Ta'ala da yi masa biyayya wato a matsayin siffanta fadin iblis a aikace: “Lallai ne, zan zauna in katange masu tafarkinka madaidaici (wato zan batar da su). Sannan kuma hakika, zan je masu daga gaba gare su, kuma daga baya gare su, kuma daga bangarorin damarsu da bangarorin hagunsu, kuma ba za ka sami mafi yawansu masu godiya ba” A’araf: 16-17, kuma lallai wadannan fasikan matan suna koyon hanyoyi kala-kala na wasanni da maza da jefa su cikin sabo ta hanyar tafiya tsirara (babu wata shigar kirki) da suke yi a kan tituna da sauran rangwade-rangwade a cikin manyan makarantu da kirkirar nau’oi na tabarruji, da wasanni na motsa jiki, da wuraren koyar da fitsara fannoni daban-daban.

To a yayin da muke son mu fuskanci wannan domin magance wannan cutar mai rushe tarbiyyar al'umma, za mu iya magance ta hanyar amfani da littafi mai suna: Zahirin al'ummar da ta saki hanya, da littafi mai magana a kan abubuwan da suke da alaka da mata, da littafin da yake magana tasirin motsa jiki da fannoni masu tarwatsa kyawawan halayen al'umma, da littafi da yake magana a kan matsalolin daliban jami’a da halin kuncin da sukan samu kansu a ciki da abubuwan da suke so, da littafi mai magana a kan duk abubuwan da suka shafi matasa, da littafi mai magana a kan fikihun iyali sannan kuma ya kunshi alakokin da e akwai tsakanin iyalai da dangi da al'umma daidai da koyarwar shari'a da sauransu, lallai wadannan mishkilolin masu hadari sukan shiga cikin dukkan abubuwan can da muka zayyano, sai dai tataunawa kowace mushkila daga cikin mishkilolin takan dauki wani salo na daban sabanin salon da wata mushkilar take dauka, to kuma za mu ga akwai karin bayani da sharhi a cikin wadancan littafan da muka yi magana a kansu, wanda sakamakon haka za a samu cikakken bayani idan aka hada dukkan bangarorin[1].

8- Yin amfani da halaye daban-daban tare da bin hanyoyi nau’i-nau’i domin shiryar da dan adam, kuma kasantuwar abubuwa guda uku ne suka hadu suka yi mutum wadanda su ne rai, hankali da zuciya, to za ka samu cewa gabaki dayansu a shirye suke domin yi wa Allah Tabaraka wa Ta'ala biyayya, tabbas na yi wannan bayanin a wadace a cikin darasina mai suna: (Mu koma ga Qur'ani).

Za ka samu danadam yana yawan amfana da fidira dinsa yana tasirantuwa da ita kuma lallai an sifanta dalilin saukar Qur'ani a cikin wasu hadisan da cewa: “Domin ya yi tasiri tare da habbaka fidirarsu) domin sanin kai (wujdani) shi ne dalili mafi karfin bayyana kuma mafi gaskatarsa, babu wanda ke musu a kan wannan, saurara ka ji inda Allah Ta'ala yake magana da fidira a wajen tabbatar da mahalicci: {“Shin maniyyin da kuke zubawa a (cikin mahaifar matayenku) kun gan shi? Shin ku ne kuke halitta shi, ko kuwa mu ne masu halittawa?}, {“Shin abin da kuke shukawa, kun gan shi? Shin ku ne kuke tsirar da shi ko kuwa mu ne masu tsirarwa?}, {“Shin ruwan da kuke sha, kun gan shi? Shin ku ne kuk saukar da shi daga girgije ko kuwa mu ne masu saukarwa?}, {“Shin wutar da ku ke kyastawa (hasawa), kun gan ta? Shin ku ne kuke kaga halittar bishiyarta, ko kuwa mu ne masu kagawar?} Waki’a: 58-72. Akwai kuma inda Allah Ta'ala yake magana yana mai aibata ko zargin mutum mai sabo da cewa: “Shin kyautatawa na da wani sakamako?! Face kyautatawa” Arrahman: 60, gas hi kuma kai kana ta rayuwa cikin arziki da ni’imar Allah Tabaraka wa Ta'ala: “Kuma idan da (za ku so) ku kididdige ni’imomin Ubangiji ba za ku iya lissafe su ba” Ibrahim: 34.  

 



[1] An riga an gama wallafa wadannan kananan littafan kuma sun kunshi gabaki dayan wadancan darussan da aka ambata cikin falalar Allah Tabaraka wa Ta'ala.