Samuwar Yahudawan Sahayina Dalili Ne Na Cuta, Magance Cutar Za A Yi Daga Tushenta

| |times read : 376
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Samuwar Yahudawan Sahayina Dalili Ne Na Cuta, Magance Cutar Za A Yi Daga Tushenta

A yayin da al'ummar musulmi a yau suke cikin damuwa game da al’amarin haramtacciyar gwamnatin sahayina kuma suna ta kokari wajen ganin sun gusar da ita, to ya kamata su farga a kan cewa wannan gwamnatin fa ba wata aba ba ce face wata cuta wacce ta fito a jikin al'ummar musulmi sakamakon samun wata boyayyar cutar da ita ce tushe kuma asali na samuwar wannan cutar, cutar kuwa ita ce nisanta da juya bayan da musulmi suka yi wa manhaji da tsarin Allah a cikin rayuwarsu, don haka bai kamata su dinga fifita damuwa da abubuwan da a sakamakon cutar ne suka bijiro ba, da kuma gafala a kan ainahin tushen cutar, sai misalinsu ya zama kamar abin da yake gudana a yayin karawar bajiman sa – kamar yadda wani daga cikin mufakkirai ya kamanta[1] - domin bajimin sa yana mayar da dukkan kwazonsa, shiryawarsa, fushinsa da karfinsa gabaki daya a kan jan kyelle ne amma sai ya gafala ga barin abokin karawarsa wanda ke rike da kyallen, to sai wannan mai rike da kyallen hankali kwance ya gagara masa wuka a wuyansa alhali yana gafalalle daga barinsa sai ya mace ya zama tarihi. To kada halinmu ya zama iri daya da halin bajimin sa fa?! Kuma kai kana ganin al'umma tana kusantar yin nasara a kan makiyanta duk lokacin da ta kusanci yin nasara a kan ranta, a daidai gwargwadon yadda ta iya koma wa Allah Tabaraka wa Ta'ala.



[1] Wannan mutumin kuwa shi ne: Shaikh Jaudat Sa’id.