Fikihun Yadda Za a Fuskanci Kafirai Da Dawagitai

| |times read : 684
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Fikihun Yadda Za a Fuskanci Kafirai Da Dawagitai

Wannan fikihun ya game dukkan sasannin rayuwa, to mene ne ya faru ne a Qur'ani aka samar tunanin na abin da zai yiwu a kira shi da sunan fikihun yadda za a fuskanci kafirai?  Allah Ta'ala ya ce: “Kuma kada ku sassauta a cikin neman mutanen, idan kun kasance kuna jin radadi, to lallai su ma suna jin radadi kamar yadda kuke jin radadin, kuma kuna fata (ta samun rahama) a wajen Allah, abin da ba su da fata a kai, kuma Allah ya kasance masani ne mai hikima” Nisa’i: 104, to mene ne na gudun haduwa da su madamar dai kowane bangare biyun yana fuskantar damuwa? Alhali ku kun bambanta da su domin kuna da fatar samun rahamar Allah a lahira don haka baku da asara, yayin da su ba su da wata fata ta samun wani abu a lahira in ba azaba mai radadi ba.

        Da fadinsa Ta’ala: “Kuma sun yi tsammanin cewa ganuwoyinsu (kafaffu masu kauri) za su tsare su daga (azabar) Allah, sai Allah ya je masu ta wajen da ba su yi zato ba, kuma ya jefa tsoro a cikin zukatansu, suna rushe gidajensu da hannayensu da kuma hannayen muminai, to ku lura fa ya ku ma’abota basirori” Hashr: 2.

       Da fadinsa Ta’ala: “Ba ya kasancewa ga mutanen Madina da wanda yake a gefensu daga kauyawa, su saba daga bin Manzon Allah kuma kada su yi gudu da rayukansu daga ransa, wancan, saboda cewa lallai kishirwa ba ta samunsu, haka nan wata wahala, haka kuma wata yunwa a cikin hanyar Allah, kuma ba su daukar wani mataki wanda yake fusata kafirai, kuma ba su dandana wa kafirai wata damuwa ba face an rubuta masu da shi ladar aiki na kwarai, lallai ne Allah ba ya tozarta ladar masu kyautatawa. Kuma ba su ciyar da wata ciyarwa karama ko babba, kuma ba su keta wani rafi ba sai an rubuta masu, domin Allah ya saka masu da mafi kyawon abin da suka kasance suna aikatawa” Tauba: 120-121. To wai mai ya kawo ja da baya da gazawa a cikin gabatar da abin da yake kaiwa ga da’ar Allah Tabaraka wa Ta'ala na ba yin kwazo da ba da dukiya, kuma mai ya kawo munana zato ga Allah Ta'ala wannan abin da yake zowa mutane a duk lokacin da aka bukaci su sauke abin da yaau wuyayensu na hakkokin shari'a, kamar kumusi da zakka da sauransu.

      Daga ciki akwai fadinsa Ta’ala: “Sannan kuma mu kubutar da Manzanninmu da wadanda suka yi imani, kamar wannan ne tabbatacce ne a gare mu, mu kubutar da masu imani” Yunus:  103.

      Daga ciki akwai wadannan ayoyin masu albarka na suratu Muhammad, idan kaso ma za ka iya daukar ruhinka, tunaninka da zuciyarka ka kaisu wancan zamanin mai dadi wanda mutum ya rayu a cikinsa ka hakaito cewa kana cikin taron muminai wadanda ke kewaye da Manzon Allah (s.a.w.a) wanda a farkon saqo aka sha wahala a yayin da suka kasance ‘yan kadan masu rauni Kuraishawa suka dandana masu azaba kala-kala, har aka kai lokacin da suka kafirai suka yi rauni suka fidda tsammani bayan yakin Ahzab lokacin da reshe ya juye da mujiya al’amari ya dawo hnnun su Manzon Allah (s.a.w.a) kuma nasararsu ta dinga zuwa tun daga fat’hu Hudaibiyya zuwa fat’hu Khaibar da fat’hu Makka da Da’if sannan Yaman da Aljazira, sannan ka hakaito cewa kana gurin lokacin da Qur'ani yake sauka irin wannan magana ta Qur'ani mai girma daga gurin Ubangijinka mai tafiyar da lamurranka, mahaliccin sammai da kasa yana magana da kai kai tsaye yana ce maka: “Da sunan Allah mai rahama mai jin kai”. “Wadanda suka kafirta kuma suka kange mutane daga tafarkin Allah, (Allah) ya batar da ayyukansu. Kuma wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai, kuma suka yi imani ga abin da aka saukar ga Muhammad, alhali kuwa shi ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) ya kankare masu munanan ayyukansu, kuma ya kyautata halayensu. Wannan kuwa saboda lallai wadanda suka kafirta sun bi karya, kuma lallai wadanda suka yi imani sun bi gaskiya daga Ubangijinsu, kamar wannan ne Allah yake bayyana wa mutane misalansu. Saboda haka idan kun hadu da wadanda suka kafirta (a fagen yaki), sai ku yi ta dukan wuyoyinsu har a lokacin da suka yawaita masu kisa to ku tsananta daurinsu sannan inma karamci a bayan haka ko biyan fansa, har yaki ya saukar da kayansa masu nauyi, wancan da Allah naso da ya ci nasara a kansu (ba tare da yakin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) domin ya jarraba sashenku da sashe, kuma wadanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah to ba a batar da ayyukansu ba. Zai shiryar da su kuma ya kyautata halayensu. Kuma ya shigar da su aljanna (wacce) ya siffanta ta a gare su. Yaku wadanda suka yi imani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku kuma ya tabbatar da dugaduganku. Kuma wadanda suka kafirta, to mutuwa ya tabbata a gare su, kuma (Allah) ya lalata ayyukansu. Wannan saboda lallai su sun ki abin da Allah ya saukar domin haka ya lalata ayyukansu. Shin ba su yi tafiya ba a cikin kasa, domin su gani yadda akibar wadanda ke a gabaninsu ta kasance? Allah ya darkake a kansu, kuma akwai misalan wannan akibar ga kafirai (na kowane zamani). Wancan, saboda lallai Allah ne majibincin wadanda suka yi imani, kuma lallai kafirai babu wani majibinci a gare su[1]. Lallai ne Allah na shigar da wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan kwarai a gidajen aljanna kogunan ruwa suna gudana daga karkashinsu, kuma wadanda suka kafirta suna jin dan dadi (na duniya) suna ci kamar yadda dabbobi suke ci, kuma wuta ita ce mazauni a gare su. Kuma da yawa akwai alkarya, ita ce mafi tsanani ga karfi daga alkaryarka wadda ta fitar da kai, mun halaka ta, sannan kuma babu wani mai taimako a gare su. Shin wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa zai zama kamar wanda aka kawace masa mugun aikinsa, kuma suka bibiyi son zuciyarsu” Muhammad: 1-14, “Allah ya yi wa’adi ga wadanda suka yi imani daga gare ku, kuma suka aikata ayyukan kwarai, lallai zai shugabantar da su a ban kasa kamar yadda ya shugabantar da wadanda suke daga gabaninsu, kuma lallai ne zai tabbatar masu da addininsu wanda ya yardar masu, kuma lallai ne yana musanya masu daga bayan tsoronsu da aminci, suna bauta mani ba su hada komai da ni, kuma wanda ya kafirta a bayn wannan to wadancan su ne fasikai” Nur: 55.

              Kuma a tsakankanin wannan lokacin Qur'ani ya yi ta gargadin munafukai a kan hankoron da suke yi don yaudarar muminai a kan cewa kada su yi fito na fito da makiya, a lokaci guda kuma suna yi masu izgili saboda raunin da suka lura suna fama da shi da kuma rashin wadatattun kayan yakin da za su iya fuskantar makiya, sai dai wani abu da suka gafala a kansa shi ne sirrin karfin muminai wanda shi ne kusancinsu da mannuwarsu ga Allah Tabaraka wa Ta'ala, saurara ka ji abin da Allah Ta'ala yake fada: “A lokacin da munafukai da wadanda suke fama da cuta a cikin zukatansu, suke cewa: Wadannan (mutanen) addininsu ya rude su, (to amma) wanda ya dogara ga Allah to lallai ne Allah mabuwayi ne mai hikima” Anfal: 49.

       Kuma yana shigowa cikin wannan siyakin – ina nufin fito na fito da kafirai – dukkan alkawuran Allah na bayar da nasara da galaba da gadon kasa, da kuma cewa akiba ta su ce, haka kuma lallai Allah yana tare da su, kuma mala’iku suna sauka gare su domin su samar masu da natsuwa, da kwaranye tsoro da bakin ciki daga gare su. Kuma suna kulla yarjejeniyar cinikayya a tsakaninsu suna saye daga gare su kawukansu da dukiyoyinsu, kuma kudaden cinikin nasu su ne aljanna. Haka nan kuma da rubanyawar rancen da aka bai wa Allah Tabaraka wa Ta'ala da bayar da infaki dominsa. To wannan dai a takaice, kasantuwar ba a samu damar fadawa fiye da haka ba.   

       Amma dai akwai wata hakika mai girma da Qur'ani ya tabbatar da ita cewa tabbas nasara da rinjaye a kan makiya na zahiri wato na waje – kafirai – lallai ba komai ba ne su face wani reshe daga cikin rassan nasara da rinjaye a kan makiyi na can cikin jikin mutum wato rai mai yawan umarni da mummunan aiki sai kuma shaidan, za ka same shi (Qur'anin) yana alkawarta wa muminai cewa su ne za su kalifanci ban kasa su gajeta da duk abin da ke kanta, to amma sai dai tun a farko ya riga sanya cewa gyaran kai (tarbiyyantar da kai) tare da yin riko da manhaji da tsarin Allah su zama a gaba, wato mutum ya fara da tarbiyyantar da kansa tun a farko, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma muna nufin mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasar, kuma mu sanya su shugabanni (imamai), kuma mu sanya su magada. Kuma mu tabbatar da su a cikin kasar, mu nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu abin da suka kasance suna tsoro daga gare su” Kasas: 5-6, a farko sai ya sanya su imamai, wanda hakan yake nufin tsarkake zatinsu da tafiyar da duk wata kazanta daga gare shi, kuma yana tabbatar da cewa babu wata kima ga kowace irin nasara a kan kafirai madamar nasarar ba ta kasance tana tare da yin nasara da galaba a kan shaidan ba, da kuma yin aiki saboda Allah shi kadai, domin duk aikin da bai kasance don neman yardar Allah ba, to da su da kafiran duk babu wani bambanci, kuma dukkansu sun zama ma’abota duniya kuma zai zama dukkansu ba su da wani rabo a lahira.

Alal misali lokacin da reshe ya juye da mujiya ga musulmi bayan galabar da suka yi a yakin Uhud, yayin da hakan ya jawo babbar asara gare su, Allah subhanahu wa Ta’ala yana magana da su cewa: “Lallai ne wadanda suka juya daga gare ku a ranar haduwar jama’a biyu, shaidan kawai ne ya zamar da su, saboda sashen abin da suka aikata (na sabo)” Aali Imran: 155. To a nan da galabarsu da juyawarsu sun faru ne sakamakon abubuwan da suka aikata na sabo, kuma a makwafin wannan Allah Ta'ala yana cewa: “Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku” Muhammad: 7. Kuma nasarar Allah tana samuwa ne idan ana yin da’a a gare shi in ba haka ba kuwa domin shi mawadaci ne ga barin talikai, kuma waccan ayar da ta gabata mai cewa “Allah ya yi wa’adi ga wadanda suka yi imani daga gare ku”. Daga nan ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi magana da mujahidai wadanda suka dawo daga wajen yaki: “Maraba da ku, kun kammala karamin yaki, yanzu babban yaki ne ya yi maku saura, sai aka ce: Mene ne wannan babban yakin ya Manzon Allah? Sai ya ce: Yaki da son rai”[2].    

 



[1] Kuma wannan ayar tana misalta tsari na gabaki daya na wannan gaba da gaba din ga muminai, domin su suna da majibinci lamari wanda yake kula da su yana kuma daukar nauyin tarbiyyantar da su, kula da walwalar su da kuma maslahohinsu, wanda yake shi ne Allah Tabaraka wa Ta'ala, a yayin da kafirai ba su da majibinci in ma suna da shi din to bai wuce shaidan mai rauni ba wanda yake guduwa a yayin da aka yi gaba da gaba ga kuma mugun hali na zillewa: “Kuma a lokacin da shaidan ya kawace masu ayyukansu, kuma ya ce: Babu marinjayi a gare ku a yau daga mutane, kuma ni makwabci ne gare ku, to a lokacin da kungiyoyi biyu suka hadu, ya koma a kan digadigansa, kuma ya ce: Lallai ne ni barantacce ne daga gare ku, ni ina ganin abin da baku gani, ni ina tsoron Allah, kuma Allah mai tsananin ukuba ne” Anfal: 48.

[2] Al-Kafi: 5/12, babin fuskokin jihadi (wujuhul jihad).