Darussan Da Za A Amfana Da Su Daga Qur'ani Na Gyaran Al'umma

| |times read : 1056
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Darussan Da Za A Amfana Da Su Daga Qur'ani Na Gyaran Al'umma

A nan yana da kyau yin ishara a kan wasu daga cikin darussan da za a amfana da su daga Qur'ani a cikin gyara da saita al'umma da shiryar da ita:

1- Mayar da hankali a kan abin da ke haifar da cuta fiye da yadda za a maganceta, kuma lallai wani abu ne mai muhimmanci da ba makawa gare shi; domin lokacin da marar lafiya ya ziyarci likita, ya yi masa bayanin matsalolin da yake fama da su, to abu mafi muhimmancin da likita yake farawa shi ne gano ainahin cutar, sannan ya rubuta masa magani, amma wadatuwa da yin magani na wadansu abubuwa da ka iya bijirowa marar lafiyar kamar ciwon kai, zafin ciki ko tsanantar zafin jiki ba tare da ya gano ainahin ciwon ba, to wannan ainahin kwaba kenan. Alal misali wanda yake son ya magance tabarrujin da ya fito fili ko kwaikwayon da matasa suke yi wa turawan yamma ko yana son ya magance matsalar rashin ba da kumusi ko rashin yin sallah, ko kuma ainahin sabo da mutane suke yi kamar shan giya da luwadi, ko kuma ka ce: gabaki dayan rashin bin shari'ar Allah da mutane suke yi da gangancin saba mata; to ba ya wadatarwa ya zo yana fada masu cewa abu kaza wajibi ne ku aikata shi, abu kaza kuma haramun ne ku guje shi, domin su ai musulmai ne kuma sun san da hakan. Dole ne ya fara da gano cutar wacce ta jawo masu suka yi rauni wajen bin addininsu wanda shi ne zai taimaka wajen dabbakawa, sannan sai a tafi ga magani, kuma shi yin rauni a wajen bin addini abin da yake kawo shi shi ne rauni a bangaren tarbiyya da akida ga al'umma, shi ya sa Qur'ani ya mayar da hankali kan wannan a Makka – wato tun a farko-farkon saukarsa – a kan wadannan abubuwan guda biyu (akida da tarbiyya). Qur'ani ya yi bayanin a kan akida kuma ya ba ta kariya da dalilai daban-daban, ya magance ishkalolin da aka bijiro masa da su, kuma mafi yawanci ya bi da su ne ta hanyar fidira dinsu (yanayin zubin halittar mutum) domin shi dalili ne na lamiri wanda ya fi mayar da hankali ga can cikin kowane mutum ta yadda ba wanda ya isa ya yi inkarinsa da saba masa. Sai Qur'ani ya muhimmantar da zuwa da yanayin da ranar kiyama zai kasance da sunnar Allah wacce ta gudana a kan magabatan al'ummu, kuma ya zo da manya-manyan abubuwan da suka faru  masu ba da darasi a rayuwa har ya samu ya farkar da hankulansu, ya tsarkake zukatansu daga wannan lokacin ne sai ya fara kallafa masu, sai suka zama suna masu biyayya, kuma mun sani cewa lokacin da aka dauka ana tarbiyya a Makka ya fi yawa a kan na Madina, wanda daga nan ne za a fahimci muhimmanci mai yawa na a fara sanin ainahin cuta kafin a tafi ga magani.

2- To daga nan ne kofa za ta bude ta maganar darasi na biyu game da irin hanyar da Qur'ani ya bi wajen gyaran zukata da al'umma, wacce ita ce wajabcin gina janibin tarbiyya da halaye na kwarai da akida ga mutum musulmi, kuma lallai Qur'ani wajen yin wannan ginin ya yi amfani da wasu hanyoyi sababbin salo da ya dogara da su, na ambace su a cikin littafina (Falanarji’u Ilallah) a can din na fadi cewa: Lallai Qur'ani ya bi wadansu hanyoyi guda uku wadanda rayuwar mutum take gudana a karkashinsu (hankali, zuciya da ruhi). A babin misali Qur'ani yakan alakanta rashin samun albarkoki daga sama, rashin samun alheirai daga kasa, salladuwar ashararai da iko a kan sauran mutane, rashin amsa addu’a, a kan nisantar da mutane suka yi ga shari'ar Allah da kuma barin yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Don haka duk wanda yake son ya tsira daga wadannan wahalhalun masu tsanani, to ya dawo ga Allah ya sauke nauyin da ke kansa na wajibai. Ya zo a hadisi cewa: “Idan kuka bar yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna to za a debe dukkan albarkoki daga gare ku kuma bala’oi za su sauka a kanku, kuma ashararanku za su salladu a kanku, sannan za ku yi ta yin addu’a amma ba za a masa maku ba”[1].

      Mafi girma daga cikin wadancan hanyoyin shi ne abin da muka yi nuni gare shi na batun bijirowar da Qur'ani ya dinga yi na halin lokacin mutuwa da abin da zai biyo baya na ranar kiyama da yadda zai kasance wato abubuwan da idanu za su shaida a ranar da hirar kafirai da fasikai a cikin wuta tare da shaidanunsu za su auku cikin ambatowar sunnonin Allah Tabaraka wa Ta'ala ga masu bijirewa ga da’arsa. Allah Ta'ala ya ce: “Allah ya darkake a kansu, kuma akwai misalan wannan akibar ga kafirai (na kowane zamani)” Muhammad: 10, “Sai Allah ya kama su saboda zunubansu, kuma Allah mai tsananin ukuba ne”, Aali Imran: 11. Akwai kuma ni’imomin Allah ga bayinsa wadanda ba su kidayuwa kuma su kansu bayin sun yi ikirari da samuwar hakikanin fidira; “Shin kyautatawa na da wani sakamako face kyautatawa” Rahman: 60. Sannan sai bayani na sa’adar da take zama dalili na bunkasar zuciyar dan adam da rayuwarsa da garuruwansa idan dai har zai bi shari'ar Allah sau da kafa, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma lallai da mutanen alkaryu sun yi imani kuma suka yi takawa da hakika mun bude albarkoki a kansu daga sama da kasa” A’araf: 96.

     Lallai akida da tarbiyya su biyun nan su ne wadanda suke tsara yadda mutum zai isa ga hadafin da rayuwa ta doru a kai, don haka ne ma za ka ga su ne suke iyakance masa hanyoyin da zai dosa, alal misali; idan aka bukaci ba da gudunmawa ga wani aikin alheri ko taimakon wani mabukaci; wane ne zai yi hanzari wajen bayarwa: shin mumini ne wanda yake neman yardar Allah Ta'ala kuma yana kwadayin sakamako daga gare shi ko kuwa wanda ya watsar da addini wanda iyakar makurar himmarsa ita ce ya yi ta tara abin duniya irin wadanda suke: “Sun yanke tsammani daga (rahamar) lahira kamar yadda kafirai suka yanke tsammani daga mazowa kaburbura” Al-Mumtahana: 13. To na farkon shi ne farkon wanda zai hanzarta ya bayar. Wannan misali ne na tasirin akida da tarbiyya wajen tunkuda mutum ya aikata aikin kwarai, domin hadafin mumini (samun yardar) Allah Tabaraka wa Ta'ala, saboda haka ku kasance daga cikin ‘ya’yan lahira, kada ku kasance daga cikin ‘ya’yan duniya. Ba wani abu ne ya rugurguza al'umma har ta bace ta saki hanya ba sai saboda ta rasa hadafin da take rayuwa dominsa sai suka tarwatse ga barin hanya. Allah Ta'ala ya ce: “Kuma lallai wannan ne tafarkina madaidaici, sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarraba ku daga barin hanyata, wannan ne Allah ya yi maku wasiyya da shi watakila ku zama masu takawa” An’am: 153.

         Yanzu abin da ya rage mana shi ne cike wannan gurbin a cikin hankula da zuciyoyin al'umma har su gyara hanyar da suke a kai wanda hakan zai kai su ga gyaran rayuwarsu daidai da yadda Allah Tabaraka wa Ta'ala yake so, don haka sai mu yi riko da hanyar Qur'ani ta raya zukata, da daukaka su da tsarkake rayuka da ciyar da su abincinsu na akidar gaskiya wacce take ita ce tushen madaukakan halaye na kwarai, Allah Ta’ala ya ce: “Shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani, zukatansu su yi tawali’u ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar wadanda aka baiwa littafi gabanin haka, sai zamani ya yi tsawo a kansu, saboda haka zukatansu suka kekashe, kuma da yawa daga cikinsu fasikai ne” Hadid: 16.

       Wannan wata kofa ce wacce ya kamata mufakkirai da masu ba da horo su shiga ta cikinta domin salo ne na Qur'ani wajen wa’azi da raya zukata, kuma dukkan ayoyinsa da mai hankali zai yi zurfin tunani a kansu da ya sabunta tunaninsa a cikin manhajin rayuwarsa, kamar dai fadinsa Ta’ala a cikin suratul Dukhan: “Da yawa gonaki da idanun ruwa (koramu) sun barsu. Da shuke-shuke da kyawawan kerarrun gidaje. Da wata ni’ima da suka kasance a cikinta suna masu hutawa. Kamar haka kuma muka gadar da su ga wadansu mutanen daban. Sannan sama da kasa ba su yi kuka a kansu ba, kuma ba su kasance wadanda ake yi wa jinkiri ba” Dukhan: 25-29.

       Kuma ni ina maku nasiha da karanta littafin (Al-Qalbul Salim) littafi ne juzi’i biyu, na dayan yana magana ne a kan akida na biyun kuma a kan tarbiyya da kyawawan halaye, kuma lallai wannan littafin mujalladi biyu abin nema ne ga zuciyar da take mai ikilasi mai tsarki.

3- Bi daki-daki a cikin shiryarwa, gyarawa da rika hannun mutane cikin tausasawa, kuma babban misali a nan shi ne: Bi daki-daki a cikin haramta shan giya – bisa la'akari da cewa wata al’ada ce da ta samu gindin zama a cikin al'umma wacce ta riga ta ratsa hankulansu da zukatansu – don haka sai aka fara hanawa ta hanyar bin matakai; mataki na farko: “Suna tambayarka game da giya da caca, kace: A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfanoni ga mutane” Bakara: 219. Sai wasu suka fara cewa to kar mu sha ta, tunda shan zunubi ne, ga shi kuma Allah ya haramta abubuwan alfasha da abin da ya bayyana daga gare su da wanda ya boyu da kuma zunubi. Wasu kuma sai suka ce daidai gwargwadon amfanin da take da shi. To sai fadin Allah Ta'ala ya sauka: “Kada ku kusanci sallah alhali kuwa kuna masu maye, har sai kun san abin da kuke fada” Nisa’i: 43. To sai wasunsu suka hanu, suka ce ba za mu sha wani abu wanda zai hana sallah ba, sannan sai ayar surar Ma’ida ta sauka wacce ta zo da tabbataccen hani mai gaba daya: “Ya ku wadanda suka yi imani, abin sani kawai giya da caca da refu da (wani nau’in kayan kuri’a), (su dukansu) kazanta ce daga aikin shaidan, sai ku nisance su, wala’alla ku yi nasara” Ma’ida 90.

     Kuma ita kanta saukar Qur'anin daya-bayan-daya, yanki-yanki sannu a hankali har aka dauki tsawon shekara 23 lallai hakan ya faru ne bisa hadafi – na daga abubuwan da ya yi hadafi gare su – magance wani yanayi bisa la'akari da wuri da zamani da zuruf din da ake ciki tare da la'akari da bambancin matakan da mutane suke a kai da isti’idadinsu na karbar saqon da aiwatar da shi.

Kuma zai iya yiwuwa saukarsa daki-daki ko daya-bayan-daya din na da wasu fuskokin daban-daban, domin a lokacin da yake son ya magance wata matsala mai tushe (tun kaka da kakanni) ta al'umma – kamar wata al’adar kabila wacce alal misali – da farko sai mu fara da kawo ishkaloli game da ingancin wannan al’adar da sanya shakku a cikinta, sannan sai a kawo makwafin wannan din da mafi alhairanta wadanda suke kishiyantarta, to idan tsira wannan shakkun a zukata kuma hankulla suka koma kan makwafi mafi cancanta sai natsuwa da wannan din ya samu kafuwa a rayuka, daga daidai wannan lokacin za a iya fara nakadinta, amma kokarin fara nakadi kai tsaye wato ba tare da waccan shimfidar ba, to lallai wannan yana nufin rushewar ginin musamman ma idan ya zamana al’adar ta samu kafuwa mai asali ce domin an halicci mutum a kan dabi’ar girmama abin da ya gada da kuma bautawa abin, a saboda haka sai wadannan mutanen su zama masu gaba da dukkan wani yunkuri na kawo canji game da wannan al’adar da suka ginu a kanta.

        A lokacin da aka aiko Manzo (s.a.w.a) da Annabta, bai fara da tunkarar gumaka kai tsaye ba, a’a sai ya fara bauta wa Allah shi kadai tare da Ali (as) da Khadija (as), a gaban idon Kuraishawa suna gani suna ji, kuma ba tare da sun cutar da shi da komai ba, sai dai wannan aikin na Manzon Allah (s.a.w.a) ya bude kofa ta tambayoyi masu yawa; suka dingi cewa mai wadannan ukun mai suke yi, kuma don wa suke bautar. Kuma mai ya sa suka bar hanyar al'ummarsu, wace irin gwarzontaka ce wannan wane irin imani ne mai zurfi haka ya ratsa zukatansu har suke iya jurewa tsayuwa da dukkan natsuwa a gaban kowa da kowa haka!

     Wadannan tambayoyin sun zama sanadin shigar wasu jama’a cikin musulunci – ka duba kissar Abdullah dan Mas’ud a cikin littafan sira – kuma Kuraishawa ba su yi fito na fito da shi ba, saboda bai tsokane su ba kuma idan da ya yi fito na fito da gumakansu tun a tashin farko to da wadancan tambayoyin ba su yi masu tasiri ba.

4- Muhimmantarwa da jawo hankalin al'umma game da al’amura na asasi wadanda ba zai yiwu su samu ba sai da kulawar ita al'ummar, musamman abubuwan da ya san al'ummar tana da ja a kansu da juya masu baya a bayansa (s.a.w.a) sai ya tsananta yin magana a kansu, alal misali: yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, Imamanci da jibintar lamurran muminai, tsanantawa ga kafirai, nuna soyayya ga makusanta, riko tare da yin kankamo da Qur'ani da itra (Ahlul Baiti (as)), kulawa da masallatai da sallolin jam’i na kamsu salawat da ta Juma’a.

Amma Annabi (s.a.w.a) yana gabata sai al'umma ta yi watsi da wadancan al’amuran na asasi ga al'umma masu bayar da kariya ga samuwarta, nan da nan sai kaucewa daga hanya ya soma. Kuma duk wani neman kawo gyara da samuwar alfanu to dole ne ya biyo bayan bincike wanda zai bayyana rawar da wadannan al’amura za su taka a cikin rayuwar mutane. To kuma wannan bincike ne mai zaman kansa da izinin Allah Ta’ala.

5- Tausasawa da saukakawa ga musibu da wahalhalun da mutumin da ke neman kawo gyara cikin al'umma da shiryar da su zai fuskanta ko kuma abin da muka kira shi da sunan mai dauke da Qur'ani a matsayin sako mai kawo gyara, Allah Ta'ala ya ce: “Alif, Lam, Mim, Sad.  Littafi ne aka saukar zuwa gare ka, saboda haka kada wani kunci ya kasance a cikin kirjinka daga gare shi, domin ka yi gargadi da shi, kuma tunatarwa ce ga muminai” A’araf: 1-2. “Saboda haka tsammaninka kai mai barin sashen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai kuntata kirjinka da shi ne domin sun ce: Saboda mai ba a saukar masa da wata taska ba, ko kuma Mala’ika ya zo tare da shi” Hud: 12. “Kuma ka yi hakuri, kuma hakurinka ba zai zama ba face domin Allah, kuma kada ka yi bakin ciki saboda su, kuma kada ka kasance a cikin kuncin rai daga abin da suke yi na makirci. Lallai ne Allah yana tare da wadanda suka yi takawa da wadanda suke su masu kyautatawa ne” Nahl: 127-128. “Lallai ne za a jarraba ku a cikin dukiyarku da rayukanku, kuma lallai kuna jin cutarwa mai yawa daga wadanda aka baiwa littafi a gabaninku da kuma wadanda suka yi shirka, kuma idan kun yi hakuri kuka yi takawa, to lallai ne wannan yana daga manyan al’amura” Aali Imran: 186 Amma akwai zance mai dadi mai kwantar da rai cikin fadinsa Ta’ala: “Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lallai kai fa kana a kan idanunmu (kana a kan kiyayewarmu)” Dur: 48. Hakikanin kulawa, ba da kariya, kiyayewa, yin rahama, tallafawa da tafiya a kan basira da sauransu.

        Kuma za ka samu sura cikakkiya ta sauka tana magana a kan wannan kamar suratu Yusuf wacce ta sauka a irin yanayi na damuwa wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu a ciki a Makka kafin hijira zuwa Madina, a yayin da ya rasa mataimaki bayan rashin Abu Dalib da Khadija (as), ga shi kuma ya riga ya fidda tsammani daga musuluntar Kuraishawa, don haka ya yi fatan samun wani wurin mafaka daban wanda ba Makka ba, kamar Da’if sai dai duk da haka ba a samu rangwame ba, sai ya zama tsanani ya yi wa musulmi yawa a daidai lokacin. Amma a daidai wannan yanayin sai suratu Yusuf ta sauka a gare shi tana ba shi labarin yadda ‘yan uwa suka rayu da dan uwansu karami har suka jefa shi cikin duhun rijiya wanda wannan yana nufin mutuwa kenan a yanayi da dalilai na dabi’a, sai dai Allah Ta'ala ya aika masa ayari suka tsamo shi suka sayar da shi a gidan sarauta a Masar, sannan daga baya kuma ya fada cikin tarkon matar Aziz da sauran mata sannan ya zauna gidan yari tsawon shekaru, amma sai Allah Ta'ala ya kubutar da shi daga kurkuku ya kuma sanar da shi tawilin mafarkai, sai a albarkacin wannan ya zama ya samu matsayi amintacce a kan taskokin kasa, sannan ya zama sarki bayan ya gama mallakar zukatan mutane ta hanyar kyawawan dabi’unsa da iya tafiyar da jagorancinsa. To a nan ne wadancan ‘yan uwan suka zo gare shi suna masu kaskanta a gabansa, sai kuma ya yafe masu saboda karamcinsa da fadin kirjinsa har yana ce masu: “Babu zargi a kanku a yau, Allah yana gafarta maku, kuma shi ne mafi rahamar masu rahama” Yusuf: 92. Sannan kuma sai Allah ya sada shi da dan uwansa da mahaifinsa. Wannan shi ne kwatankwacin ainahin abin da Kuraishawa suka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) daidai wa daida da abin da ‘yan uwan Yusuf suka yi, amma shi ma sai Allah ya ba shi nasara ya dora shi a kansu har ya iya riskarsu har a cikin gidajensu a Makka, kuma shi ma sai ya maimaita kalmar dan uwansa Yusuf (as) gare su, ya ce: “Babu zargi a kanku a yau, ku je ku sakakku ne”. Bayan ya tambaye su cewa: “Mai kuke ganin zan aikata da ku? Suka ce: Kai dan uwa ne mai karamci kuma dan Baffa mai karamci”[2]. Wannan kuma ikirarinsu ne da shaidarsu gare shi suna tabbatar da daukakar Zatinsa (s.a.w.a).

6- Kwadaitarwa ga neman ilimi ko koyo da zurfafa a cikinsa ga dukkan abin da zai kusantar zuwa ga Allah Ta'ala kuma zai kara wa mutum ma’arifa. Kuma an ce a cikin Qur'ani akwai aya fiye da dari biyar masu kwadaitarwa ga neman ilimi da yin tafakkuri, yabon masu ilimi da aibata jahilci da jahilai tare kuma da siffata makomarsu, har ta kai ga an sanya Qur'ani a matsayin sifa ta ilimi, fikihu da ma’arifa ga Allah Tabaraka wa Ta'ala wani dalili ne kara karfi da kaimi ga muminai a kan makiyansu da gomomin ribanyawa. Za a iya amfana a kafa dalili a karkashin wannan ayar mai girma, Allah Ta'ala ya ce: “Ya kai Annabi! Ka kwadaitar da muminai a kan yaki, idan mutum ashirin masu hakuri sun kasance daga gare ku, za su rinjayi dari biyu, kuma idan dari suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dubu daga wadanda suka kafirta domin su mutane ne da ba su fahimta” Anfal: 65. Yayin da kuma ya sanya hakuri wanda yake daga cikin muhimman dalilai na nasara a matsayin abin da yake kawo karin karfi rubi daya kacal, Allah Ta'ala ya ce: “A yanzu Allah ya saukake daga gare ku, kuma ya san cewa lallai ne akwai masu rauni a cikinku, to idan mutum dari masu hakuri suka kasance daga gare ku, za su rinjayi dari biyu, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku za su rinyaji dubu biyu da izinin Allah, kuma Allah yana tare da masu hakuri” Anfal: 66.



[1] Tahzibul Ahkam: 6/176.

[2] Tafsiri Nuril Sakalain: 2/460.