Qur'ani Shi Ne Maganin Cututtukanmu Na Rayuwarmu Ta Zamantakewa

| |times read : 1226
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Qur'ani Shi Ne Maganin Cututtukanmu Na Rayuwarmu Ta Zamantakewa

Qur'ani yana da iko da karfin magance cututtukan da ke damun dan adam da kuma ingata lafiyarsa domin isa ga kamala, mu yanzu za mu baje kwazonmu wajen zakulo wasu daga cikinsu, kuma shi Qur'ani mai dawwama ne, rayayye kuma mai bayarwa har zuwa ranar kiyama, kuma daga cikin alamomin dawwamarsa karfin da yake da shi na tantance cuta da kuma gabatar da magani ga dukkan al'umma a kowane zamani da kowane wuri. Yanzu abin da ya kamace mu shi ne mu nemi taimakon Qur'ani mu kuma yi masa magiya a kan ya taimaka mana da maganin cututtukanmu na rayuwar jama’a a dunkule da a daidaiku.

       Idan aka jarabci al'umma da cutar rarrabuwa da tarwatsewa, to maganinsu shi ne fadin Allah Ta'ala: “Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba”, Aali Imran: 103. Bayan fahimtar cewa lallai igiyar Allah tana nufin: Qur'ani da Ahlul Baiti (as) kamar yadda hadisi ya nunar.

       Idan aka jarabci al'umma da cutar tsoro, raggwanci da rauni to maganinsu shi ne fadin Allah Ta'ala: “Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske ku, kuma koda kun kasance a cikin ganuwoyi ingantattu”, Nisa’i: 78. “Ka ce: Lallai mutuwar nan da kuke gudu daga gare ta, to lallai ita mai haduwa da ku ce” Juma’a: 8.

       Idan zukatanku suka cika da takaici da fidda tsammani to maganin wannan fadin Allah Ta'ala: “Kuma kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, lallai ne babu mai yanke tsammani daga rahamar Allah face mutane kafirai” Yusuf: 87. “Kuma wane ne yake yanke tsammani daga rahamar Ubangijinsa, face mutane batattu” Hijr: 56. “Lallai mu, hakika muna taimakon Manzanninmu da wadanda suka yi imani a cikin rayuwar duniya da ranar da shaidu ke tsayawa” Gafir: 51.

     Idan muka hadu da wani nau’i na shugabancin da ya kauce hanya tare da zalunci ga waninmu ko a kan zamani, to mu karanta fadinsa Ta'ala: “Kuma abin da ya same ka daga sharri, to daga kanka yake” Nisa’i: 79. “Lallai ne Allah ba ya canza abin da yake ga mutane, sai sun canza abin da yake ga zukatansu” Ra’ad: 11. “Allah bai zalunce su ba, amma kansu suka kasance suna zalunta” Aali Imran: 117.

     Kuma idan mutane suka biyewa bin inna rududu, suka wayi gari a matsayin (duk wanda inna ta aura baba ne) ba tare da sun yi zurfin tunani da hangen nesa tare da sanya basira ba; to Qur'ani ya ba su amsa da cewa: “Kuma mafi yawan mutane ba su zama masu imani ba, koda ka yi kwadayin hakan” Yusuf: 103. “Kuma idan kabi mafiya yawan wadanda suke a cikin kasa da da’a suna batar da kai daga hanyar Allah, ba su bin komai sai shaci-fadi, kuma ba su fadar komai face karya” An’am: 116, “Kuma mafi yawansu ba su yin imani da Allah face suna masu shirka” Yusuf: 106.

       Daga cikin cututtukan al'umma wadanda Qur'ani ya magance su akwai (jita-jita)[1] yada jita-jita wani ciwo ne mai tarwatsa, mai kawo rarrabuwa a cikin al'umma, mai girgiza dunkulewarsu wuri guda, mai ruda tunaninsu, amma Qur'ani game da wannan matsalar da maganinta ga abin da ya ce: “Kuma idan wani al’amari daga aminci ko tsoro ya je masu, sai su yada shi, amma da a ce sun mayar da shi zuwa ga Manzo da zuwa ga ma’abota al’amari daga gare su, lallai ne wadanda suke yin bincikensa daga gare su za su sanshi, kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamarsa, hakika da kun bi shaidan face ‘yan kadan” Nisa’i: 83. Da wasunsu masu yawa wadanda suke magance ciwurwukanmu masu tsanani.[1] Nan gaba kadan rubutun da na yi a kan wannan maudu’in a cikin silsilar (Nahwa Mujtama’in nazif) zai fito.