Siffofi Da Alamomi Ko Halayyar Al'ummar Jahiliyya A Mahangar Qur'ani

| |times read : 1001
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Siffofi Da Alamomi Ko Halayyar Al'ummar Jahiliyya A Mahangar Qur'ani

Kuma sifa ta farko daga cikin siffofin jahiliyya ita ce bautar da mutane suke yi ga wanin Allah Tabaraka wa Ta'ala, bautar nan kuma tana nufin yin da’a da jibintar da lamari kamar yadda ya zo daga Ma’asumai (as) cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala: “Sun riki malamansu (yahudu) da ruhubanawansu (nasara) Ubanningiji sabanin Allah, haka kuma sun riki Masihu dan Maryam haka. Alhali ba a umarce su ba face su bauta wa Allah shi kadai, babu abin bautawa face shi, tsarki ya tabbata gare shi daga abin da suke yin shirka da shi” Tauba: 31.  Sai Imam (as) ya ce: Amma wallahi ku sani, ba su kira su a kan su zo su bauta masu ba, kuma da za su kira su din ba za su amsa masu ba, sai dai sun halatta haram a kansu, sun haramta halal a kansu, sai suka bauta masu a yayin da su ba su ma sani ba”[1]. Wannan ibada a waccan al'ummar jahiliyyar ta kasance ga wanin Allah Tabaraka wa Ta'ala, shi ya sa ya zo a farkon sura daga cikin surorin Qur'ani suna neman da kada a yi da’a ga wanin Allah “Aha! Kada ka bi shi” Alak: 19. A wancan lokacin da’a ga Ubanningiji ta kasance nau’oi daban-daban; “Ba mu bauta masu ba – ai su gumakan – face domin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja” Zumar: 3. “Kuma kada sashenmu ya riki sashe Ubangiji sabanin Allah” Aali Imran: 64. “Lallai ne mu, mun bi shugabanninmu da manyanmu, sai suka batar da mu daga hanya” Ahzab: 67. “Sai suka bi umarnin Fir’auna, kuma al’amarin Fir’auna kuwa bai zama shiryayye ba” Hud: 97. “Bayan wadannan sai (‘ya’yansu) suka gaje su a bayansu, suka tozarta sallah, kuma suka bi sha’awoyinsu, to da sannu za su ga (sakamakon) batarsu” Maryam: 59. “Kuma idan aka ce masu: Ku bi abin da Allah ya saukar, sai su ce: A’a muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa, shin kuma koda ubannin nasu ba su hankaltar komai, kuma ba su shiryuwa?” Bakara: 170. “Akwai daga cikin mutane wanda yake yin musu ga sha’anin Allah ba da wani ilimi ba, kuma yana bin kowane shaidani mai taurin kai. An rubuta masa cewa duk wanda ya jibince shi, to lallai ne sai ya batar da shi, kuma zai ja shi zuwa ga azabar sa’ir (jahannama)” Hajj: 3-4. “A lokacin da wadanda suka kafirta suka sanya ta’assubancin kabilanci a cikin zukatansu, ta’assubancin kabilanci irin na jahiliyya” Fath: 26.

       Wadannan wasu ne daga Ubanningiji na jahiliyyar farko wacce ta kasance tana bautawa wanin Allah Tabaraka wa Ta'ala wadanda su ne: (gumaka, malaman da ba muklisai ba, Fir’aunoni, bin son rai mai umarni da aikata mummuna da sha’awoyinsa, ibilis, ta’assubanci, al’adu da akidun da aka gada daga wajen magabata), kuma dukkansu asalinsu shi ne bin son rai; “To idan ba su karba maka ba, to ka sani suna bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wane ne mafi bata daga wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya daga Allah ba? Lallai ne Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai” Kasas: 50.

Shin ko halayen mutanen yau sun saba da na wadancan? Ba kuma idan nace mutane ina nufin wadannan al'ummun wadanda suka kira kawukansu da wayayyu ba, domin su sun riga sun nutse cikin duhun jahiliyya tun daga kahonta zuwa kasan tafukanta. Sai dai ku barni in yi magana game da mafi muni daga wannan wadannan da suka kira kawukansu musulmai, alhali suna tafiya kafada da kafada cikin ayarin wadannan kafiran sun nutse cikin biyayya ga sha’awa da son rai da abubuwan da suke gangarowa daga gare su na sababbin Ubanningiji kamar wasanni da fasaha da wasu nazariyoyi da fandararrun dokoki; kuma har yanzu yin da’a ga shugabanni da manya kamar misalin shugaban kabila da masu matsayi ana yi masu biyayya ba tare da an kiyaye shari'a mai tsarki ba, don haka sai suke halatta abin da Allah ya haramta, kuma suna haramta abin da Allah Tabaraka wa Ta'ala ya halatta, kuma har yanzu wadannan sanannu dabi’un nan da akidu da sunnonin iyaye da kakanni ana yi masu da’a fiye da yadda ake yiwa shari'ar Allah subhanahu wa Ta’ala biyayya, ta yadda za ka ga al'umma za su iya kauda kai idan aka sabi Allah, amma da zarar an nemi a sabawa sanannun al’adu da akidunsu ba za su taba lamincewa ba. To sai ya zama kamar harshensu yana fadin cewa: (Gara azabar wuta da a kunyata). Sabanin musulunci wanda Imam Husain (as) ya misalta shi a Karbala a cikin fadinsa:

Mutuwa ita ce mafi cancanta daga jin kunya (tozarta)  

                                     Kuma ka kunyata (a kan gaskiyarka) shi ya fi daga azabar wuta

Kuma wannan abu a fili yake a cikin dokoki da kabilu suke kafa wa da sauransu, kuma wannan matar tana yin biyayya ga kauna da son kwalliya da duk abin da al’ada ta doru a kai, sannan kuma da duk wani abu da ya fito daga yammacin turai tun daga tufafi, kayayyakin caba ado da sauransu, kuma koda sun kasance sun saba da shari'a. To shin akwai wani abu daga ibada, da’a da jibinta lamari da ya yi saura? Wannan a matakin shirka ta da’a da biyayya kenan. Kuma Qur'ani yana ba mu labari game da cewa su wadannan Ubanningijin gabaki dayansu za su barranta daga bauta masu da aka yi a ranar kiyama sai dai nadamar mai nadama a lokaci ba za ta yi amfani ba; “Kuma daga mutane akwai wanda yake rikon tamka sabanin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma wadanda suka yi imani ne mafiya so ga Allah, kuma da wadanda suka yi zalunci suna ganin lokacin da za su ga azaba da cewa lallai ne dukkan karfi ga Allah yake, kuma lallai ne Allah mai tsananin azaba ne.

A lokacin da wadanda aka bi suka barranta daga wadanda suka bi su, kuma suka ga azaba, kuma sabubba suka yanke da su. Kuma wadanda suka bi, suka ce: Lallai da muna da wata damar komawa (duniya) sai mu barranta daga gare su, kamar yadda suka barranta daga gare mu (da ba su riki kinayen ba) kamar haka ne Allah ke nuna masu ayyukansu, suna da nadamomi a kansu kuma ba su zama masu fita daga wutar ba” (165-167).

      Yana kuma siffanta wadannan Ubanningiji wadanda dan adam yake bautawa ta hanyar mika wuya kacokaf gare su da yin da’a gare su sabanin Allah Tabaraka wa Ta'ala, Allah yana cewa: “Misalin wadanda suka riki wadansu masoya wadanda ba Allah ba, kamar misalin gizo-gizo ne wanda ya riki wani dan gida, alhali kuwa mafi raunin gidaje shi ne gidan gizo-gizo, da sun kasance suna sani” Ankabut: 41.

Kuma Allah ya ce: “Kuma wadanda suka kafirta ayyukansu kwatankwacin kawalwalniya ga fako suke, ta yadda mai jin kishirwa yana zatonsa ruwa ne, har sai idan ya je masa bai iske shi komai ba, sai ya samu Allah a wurinsa, sai ya cika masa hisabinsa, kuma Allah mai gaggawar sakamako ne” Nur: 39.

Wannan kam wani bahasi ne mai matukar mahimmanci domin zai jawo hankalin mutane su fahimci cewa suna fa karkacewa daga kan akidunsu, suna fa nisa daga tsantsar bautar Allah da kuma cewa lallai da’arsu ga Allah Tabaraka wa Ta'ala ta yi karanci sosai musamman idan aka kiyasta da da’ar da suke yi wa wadannan gumakan daban-daban. Saboda haka kamata ya yi bahasin a ba shi wannan taken (Gumakan Jahiliyyar Zamani) wanda yake bahasi ne mai hadari musamman kasantuwar buyarsa ga jama’a da dabi’ar nan ta ko-in-kula gare shi hatta ga wadanda suke muminai to ballantana kuma wasunsu.

  Amma game da boyayyiyar shirka, to mafi girman musibar a nan take, a nan ne zai yi wuya ka samu wani aiki da aka yi shi da ikilasi (domin Allah shi kadai) koda ma’abocin aiki ya zaci hakan, to in ba haka ba mene ne ya sa yake rubuta sunansa a kan katon allon kan hanya a yayin da ya gina ko kawata masallaci, idan dai aikinsa don Allah ne, to mai ya sa yake gorantawa da wannan kyautar har kuma ya yi ta ba da labari a kai idan dai shi muklisi ne?

           Sifa ta biyu daga cikin siffofin jahiliyya ita ce cewa ainahin shari'ar da take tsara masu yadda za su tafiyar da rayuwarsu kuma take kula da yadda suke husumominsu ta yi nisa daga shari'ar Allah Ta'ala; “Shin hukuncin jahiliyya suke nema”? Ma’ida: 50. To kuma duk wani hukunci sabanin wanda Allah ya saukar hukunci ne na jahiliyya kamar yadda Qur'ani ya bayyana, mu kuma yanzu muna ganin mafiya yawa daga cikin mutanenmu suna rayuwa ne a karkashin kabilanci, hukunce-hukuncen kabila su ne suke hukunta su, Allah bai saukar da wani suldani game da su ba, kawai jahilan mutane ne suka sanya su wadanda suka yi nisa ga barin Allah Tabaraka wa Ta'ala, wannan kuma a babin misali ne, kai ma za ka iya dubawa a nan kusa da kai ka ga yadda sauran al'ummu wanda kusan duk tafiya guda ce. Yanzu duba ka ga kasashen duniya daban-daban dokoki da shari'oin da suke tafiyar da su duk tsare-tsare ne da mutum ya kirkira, gajiyayyen da ba ya iya mallakawa kansa wata cuta ko kuma wani amfani, kuma ba ya iya ganin fiye da karan hancinsa, amma za ka same shi a kowace rana yana canja sakin layi na kaza, yana kara sakin layi na kaza wani lokaci kuma ya cire wani, a wani yanayin kuma sai ya gano can an tafka kuskure sai ya toshe abin da zai kawo sabani, haka dai, alhali madaukakin hadisi ya siffanta duk wata sabawa shari'a da gazawa wajen aiwatar da ita da jahiliyya a cikin fadinsa (as): “Wanda ya mutu, alhali bai yi wasiyya ba, ya mutu mutuwar jahiliyya”[2].

Fir’auna wannan da yake cewa: “Ba ni nuna maku komai face abin da na gani” Gafir: 29. Ba wai wata dabi’a ce kebantacciya da ta shafi mutum daya ba, a’a wata dabi’a ce da take maimaituwa a koda yaushe a wurin da yawa daga cikin wadanda suka jinginawa kawukansu cewa su masu yin shari’a ne sabanin Allah Tabaraka wa Ta'ala.

      Daga alamomin jahiliyya akwai karkatar akidunsu, game da wannan zan yi ishara da fadinsa Ta’ala: “Suna zaton abin da ba shi ne gaskiya ba game da Allah, irin zaton jahiliyya” Aali Imran: 154. Domin sun kasance suna da imanin cewa alal misali duk irin yadda mutum ya aikata wani mummunan aiki, to da zarar ya je ya yi yanka ya shekar da jini ga Ubanningiji to shi kenan ya tsira daga azaba. To kuma al'ummarmu ta hanyar yin aiki da wasu masu hawa kan mimbari da suka dorasu a kai a cikin zukatansu shi ne cewa wata akida da ke nuna cewa duk abin da mutum ya aikata na sabo komin girmansa da sauran abubuwan ki, to zubar hawaye daya a kan tuna zaluncin da aka yi wa Imam Husain (as) ya isheshi ya shiga aljanna, suna masu jingina abin ga wannan hadisin: “Wanda ya yi kuka a kan Husain koda gwargwadon fiffiken sauro ne aljanna ta wajaba a gare shi”[3]. Sannan su kafa dalili da fadin mawaki:

Lallai wuta ba za ta taba jiki ba       

                                                      Wanda yake dauke da kurar masu ziyarar Husain

To mu ba mu inkarin karamar Imam Husain (as) daga wajen Allah Tabaraka wa Ta'ala domin ya cancanci wannan karamcin da fiye da haka ma; sai dai, wannan yana nuni ne kan misali ne na abin da zai hukunta shigar, kuma wani yanki ne na dalili na shiga aljanna amma dole ne a samu kammaluwar dalilin wato daya yankin na dalili da zai cika sharudda da rashin samuwar abin da zai hana, sharadi na farko kuma shi ne yin da’a ga Allah Ta'ala a cikin umarnoninsa da hane-hanensa, kuma a nan Qur'ani a fili ya bayyana: “Kuma ba za su yi ceto ba face ga wanda (Allah) ya yarje masu” Anbiya’i: 28. A cikin hadisi kuma daga Imam Sadik (as): “Cetonmu ba zai taba shafar mai tozarta sallah ba”[4]. Haka nan ma ya sabawa wannan ayar: “To wanda ya aikata (wani aiki), gwargwadon nauyin zarra zai ganshi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai ganshi” Zalzalah: 7-8. Amma da mutum zai gyara aikinsa kuma ya tuba, tuba ta gaskiya to wannan kam.

Wannan karkacewar ta akidu tana da matukar hadari domin za ta iya janyo mutane su nisanci addininsu, kuma za su fuskaci karancin farkawa bayan sun durmiye cikin tabon wannan akidar wacce ta yi nisa daga tsarin Qur'ani da karkatarsu zuwa gare ta don haka sai su bar aiki da Qur'anin.

          Daga cikin alamomi na jahiliyya akwai fitar mata ba lullubi, fitar tabarruji, mace ta bayyanar da wasu gabobin jikinta masu nuna kyawunta, yin shigar ko-in-kula da kuma yada alfasha; Allah Ta'ala ya ce: “Kuma kada ku yi fitar tabarruji irin tabarrujin jahiliyyar farko” Ahzab: 33. Su kuma al'ummun yau na wannan zamanin sun wuce da iyawar wadancan al’ummun cikin fasikanci, fajirci da gwanancewa a cikin tabewa, bata, jefa dan adam cikin ayyukan alfasha da hore masu dukkan wata dama ta zamani ta ci gaban mai hakar rijiya domin a yada alfashar, kamar yadda jahiliyya take alfahari da salo-salonta da kirkiraro dokoki domin su kosar da sha’awoyinsu na dabi’a ta hanyar shaidana da shakiyanci, alal misali Kuraishawa sun sunnanta wata doka wacce take haramtawa kabilu yin dawafi a Ka’aba da tufafi, wai da sunan kila sun saba wa Allah da wadannan kayan, kuma sun aika munanan ayyuka alhali kayan suna sanye a jikinsu, don haka dole sai dai su zabi yin dawafi da wasu kayan, kaya ne na musamman na mutanen Makka, ko su nemo sababbin kaya ko kuma su yi dawafin nasu tsirara.

Su kuma masoyan shaidan a yau sun sunnanta sababbin salo-salo na yada alfasha ba irin wacce aka sani ba ta hanyar kayan wasanni da wargi wadanda suke bayyana fasikanci da fajirci a fili ba, a’a. Sun kirkiro wasanni ne na motsa jiki wadanda ba su gaza wadancan wasannin muni ba, wata kila ma wadancan din su fi rangwame, domin ana gudanar da su ne a boye, kuma kowa da kowa yana boyewa, ma’abocinsu ma yana jin kunya kar asirinsa ya bayyana a sarari. Amma wadannan ana gudanar da su a sarari tare da tinkaho, kuma kowa yana yaba masu. Shin ba ka ganin wannan wasannin masu yinsu sun wayi gari a hannun shaidanu sai yadda suka yi da su?!  Haka nan dai ake ta ba su sunaye, kamar sarauniyar kyau ko wani sunan daban ko su kira shi da zaben gwana ko tantance wacce tafi kowa, alhali dukkkan wadannan ba komai ba ne face nutsewa cikin wargi, fasikanci da fajirci. Mafi munin kuma shi ne ana yin abin ne a bainar jama’a, babu mai tsaira sai wanda Allah ya tsare. Hadafin kuma abu guda ne, ana son al'umma ta rayu kamar rayuwar dabbobi cikin barbara da haikewa mata ba lissafi tare da yada fasikanci lungu da sako na garuruwan al'umma.

             Daga cikin alamomin jahiliyya akwai toshewar basira da bacewar tunani a rayuwa. Misali wasu daga cikin mutane na zamanin jahiliyya sun kasance suna hana aurar da ‘yan matansu ga wadanda ba su ba, domin suna ganin kawukansu a matsayin mafifita su ne wadanda ake kira da (Humus), to a jahiliyyar yau ta zamani za ka samu irin wadannan da yawa. Mafiya bayyana a fili su ne wani sashe na sharifai masu dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a) domin su wadannan ba su aurar da ‘yan matansu sai ga sharifi kadai irinsu, kuma ‘yan matan nasu sun gajiya, lokacin aurar da su har yakan wuce, sukan haramta masu yin rayuwa ta hakkinsu na shari’a domin su yi rayuwa cikin ni’ima, su gina iyalai, su rayu cikin sa’ada ta gamagari. Duk wannan yana faruwa ne saboda wannan murgudadden tunanin na jahiliyya. Shin ina gamin wannan murdadden tunanin da tsarin Qur'ani! “Ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi matarsa, kuma ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata” Nisa: 1. Kuma daga cikin koyarwar Manzon Allah (s.a.w.a) akwai: “Idan wani wanda kuka yarda da halayensa da addininsa ya zo maku, ku aurar masa”[5]. To idan su madaukaka ne domin dangantakarsu da Manzon Allah (s.a.w.a), to shi kuma Manzon Allah (s.a.w.a) daukakarsa tana da danagantaka ne da musulunci da biyayyarsa ga Allah Ta’ala, ba wai don sunansa Muhammad dan Abdullahi ba ne. Allah ya ce: “Lallai idan ka yi shirka, hakika aikinka zai baci, kuma lallai za ka kasance daga masu asara” Zumar: 65. A wata ayar kuma: “Kuma da ya fadi wata magana daga cikin maganganu, ya jingina ta gare mu. Da mun kama damarsa daga gare shi. Sannan lallai ne da mun katse masa lakarsa. Kuma babu wasu a cikinku da za su iya kare shi daga (azabarmu) gare shi” Al-Haka: 44-47. Kuma shi Manzon Allah (s.a.w.a) da kansa ya fada cewa: “Ni kaina da zan sabawa (Allah) da na rushe”[6]. To mene ne kimar wadanda suke kasuwanci da sunansa (s.a.w.a) amma suna sabawa shari’arsa?

        Daga cikin alamominsu akwai sassabawar dabi’u da ma’aunai wadanda da su mutum yake zama mafifici kodai ya zama mabiyin Allah na hakika ko kuma ya zama mabiyin shaidani mai cike da rudu. Qur'ani yana bayyana wadannan da cewa: “Lallai mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa” Hujurat: 13. “Ka ce: Da falalar Allah da rahamarsa, to da wannan sai su yi farin ciki, shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa” Yunus: 58 A yayin da jahiliyya suke fifita da dukiya, matsayi da yawan ‘ya’ya; “Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku). Har kuka ziyarci kaburbura” Takasur: 1-2. “Kuma suka ce: Mu ne mafiya yawa ga dukiya da ‘ya’ya, kuma mu ba mu zama wadanda ake yi wa azaba ba” Saba’i: 35. Wadannan wasu al’amura ne da suke a bayyane ta yadda ban bukatar sai na kawo misalai, to sai dai wadannan ayoyin guda biyu suna bayyanar da kwatancen nan wanda ya tallafa ya fito da bambancin a fili; “An kawata wa mutane son sha’awoyi na mata da ‘ya’ya da dukiyoyi abubuwan tarawa daga zinariya da azurfa, da dawaki kiwatattu da dabbobin gida da hatsi, wannan shi ne dadin rayuwar duniya, amma a wurin Allah kyakkyawar makoma take. Ka ce: Shin in ba ku labarin mafi alheri daga wannan? Akwai gidajen aljanna a wurin Ubangiji ga wadanda suka bi shi da takawa, koguna suna gudana daga karkashinsu, suna madauwama a cikinsu, da matan aure tsarkakakku da yarda daga Allah, kuma Allah mai gani ne ga bayinsa” Aali Imran: 14-15. Kuma a wani wajen Allah yana cewa: “Kuma dukiyarku ba ta zamo ba, haka nan ma ‘ya’yanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinmu (kusantarwa ta matsayi), face wanda ya yi imani kuma ya aikata aikin kwarai, to wadannan suna da sakamako ninkin baninki na aikin da suka aikata, kuma su amintattu ne a cikin gidaje masu benaye” Saba’i: 37.

       Daga cikin halayen da a jahiliyyar farko da ta yanzu suka yi tarayya a cikinsu akwai yada munanan dabi’u, mafi bayyanarsu daga cikinsu akwai giya, tauye mudu, algushu, karya da luwadi; Allah Ta'ala ya ce: “Kuma ku je a cikin majalisoshinku da abin da ba shi da kyau” Ankabut: 29. “Kuma kada ku nakasawa mutane kayansu” A’araf: 85. “Narkon azaba ya tabbata ga masu nakkasawa. Su ne wadanda idan suka auna daga gurin mutane suke cika mudu. Amma idan sun auna masu a kwanon awo da mizani sai suna ragewa” Mudaffifin: 1-3. Har ma izgili suke yi wa mutane masu tsafta; “Kuma babu abin da ya kasance jawabin mutanensa, face dai suka ce: Ku fitar da su daga alkaryarku, lallai ne su wasu mutane ne masu neman tsarkaka” A’araf: 82. Ta yadda ya tabbata cewa Ja’afar dan Abu Dalib sunansa ya shiga cikin tarihi a kan cewa yana cikin wadanda suka haramtawa kawukansu shan giya da yin zina a jahiliyya. Kuma daga cikin munanan dabi’un nasu akwai cewa mai karfi yana taushe rarrauna, rushe halaye na kwarai, akidun mutumtaka ballantana kuma wadanda suka shafi na Allah, muhimmi a wajensu kawai wadanne amfanoni mutum a kashin kansa zai samu. Wannan dai ita ce wayewar zamani wacce take rugurguza ‘yan kasa gabaki dayansu, tana halakar da shuka da ‘ya’yan dabbobi a saboda abin da suke kira da (maslaha) wacce take sama da komai a wajensu. Amma hadafi na hakika wanda shi ne neman yardar Allah Tabaraka wa Ta'ala da kuma tsira a gobe kiyama to wannan kauce hanya kenan, Allah Ta'ala ya ce: “Da wata kungiya, lallai ne rayukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da ba shi ne gaskiya ba a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cewa:  Ko akwai wani abu a gare mu dai daga al’amarin? Kace: Lallai ne al’amari dukkansa na Allah ne. Suna boyewa a cikin zukatansu abin da ba su bayyana shi ba a gare ka, suna cewa: Da muna da wani abu daga al’amarin” Aali Imaran: 154. Wannan ita ce iya makurarsu kuma shi ne iya hadafinsu wanda suke rayuwa a dalilinsa cewa ko akwai wani abu a gare mu dai daga al’amarin.

        Daga cikin mafi muhimmancin halayen jahiliyya, kai abin ya wuce nan ma, domin wannan shi ne dalili na samuwarta; barin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna, abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya tsawatar a kansa: “Yaya za ku kasance, idan matayenku suka lalace, matasanku suka fasikance, kuka dawo ba ku yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna? Aka ce ya Manzon Allah (s.a.w.a) shin haka zai yiwu? Ya ce: Eh, mafi sharri daga wannan ma. Yaya za ku kasance idan kuka samu kanku kuna masu umarni da aikata mummuna kuna hani da aikata kyakkyawa? Aka ce ya Manzon Allah (s.a.w.a) shin haka zai yiwu?  Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Eh, mafi sharri daga wannan ma. Yaya za ku kasance idan kuka dinga ganin kyakkyawan abu a matsayin mummuna, mummuna kuma a mtsayin kyakkyawa”?[7]

Wannan kuma shi ne inda al'umma ta isa gare shi a yau, amma gazawar tun daga farko tana a kan malaman addini ko mutanen Allah (rabbaniyyin) a irin ambatawar Qur'ani, rashin taimakawarsu da ja da bayansu cikin sauke nauyin da ya hau kansu na lamarin al'umma, kuma idan ana maganar rabbaniyyin na hakika, to fa ku ne ya ku daliban Hauza da madaukakan mutane a cikin Hauzar mai tsarki. Allah Ta'ala ya ce: “Kuma kana ganin masu yawa daga gare su suna rigegeniya da gaggawa a cikin aikata zunubi da zalunci da cinsu ga haram, tir da abin da suka kasance suna aikatawa. Don mai malamai rabbaniyyuna da manyan malamai (ahbar) ba za su hana su daga zancensu na zunubi da cinsu ga haram ba? Hakika tir daga abin da suka kasance suna sana’antawa” Ma’ida: 62-63. “Sun kasance ba su hana juna daga abin ki, wanda suka aikata, hakika abin da suka kasance suna aikatawa ya munana. Kana ganin masu yawa daga gare su, suna jibintar wadanda suka kafirta, hakika tir da abin da rayukansu suka gabatar saboda su, watau Allah ya yi fushi da su, kuma a cikin azaba su masu dawwama ne” Ma’ida: 79-80.

   Wannan kuma wani halin ne daban daga cikin halayen al'ummar da ta nisanta daga Musulunci watau soyayya ga kafirai, dangane da wannan gazawar; Amirul Muminina (as) yana cewa: “Bayan haka, lallai ne abin da kawai ya halaka wadanda suke gabaninku yayin da suka aikata sabo kuma rabbaniyyuna da ahbar ba su hane su ba daga wancan, kuma a yayin da suka nutse cikin sabo sai azaba ta sauka a kansu to sai suka fara yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna suka yi aiki, sai umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna bai hana kusantowar ajali ba kuma bai yanke arziki ba”[8].

           Kuma madamar ba a tsayu da wannan wajibin ba, to babu wata daraja da za ta yi saura ga muminai a wajen Allah da wajen Manzonsa (s.a.w.a), kai hatta ma a wajen makiyansu, shi ya sa ma akwai masu bautar Allah daya a tsakanin Kuraishawa  wadanda su ne Ahnaf, wadanda suka ki bautar gumaka, suka kebe kansu cikin bautar Allah Subhanahu, sai dai ba su kasance suna da wata daraja a wajen mushrikai ba kuma ba su ma kula da samuwarsu ba, domin cewa sun bar wajibi mai girma.

A yayin da aka sanya sauke wannan nauyin daga cikin siffofin al'ummar musulmai: “Kun kasance mafi alherin al'umma wacce aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawa kuma kuna hani ga mummuna, kuma kuna imani da Allah” Aali Imran: 110. “Kuma lallai hakika Allah yana taimakon wanda yake taimakonsa, lallai Allah hakika mai karfi ne mabuwayi. Wadanda suke idan muka ba su iko a cikin kasa sai su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka kuma su yi umarni da kyakkyawa da hani ga abin ki, kuma akibar al’amura ga Allah take” Hajj: 40-41. “Kuma wata jama’a daga cikinku su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da alheri, kuma suna hani daga abin ki, kuma wadannan su ne masu cin nasara” Aali Imran: 104. “Kuma muminai maza da muminai mata sashensu majibincin sashe ne, suna umarni da kyakkyawa suna hani ga mummuna kuma suna tsayar da sallah, suna bayar da zakka, suna da’a ga Allah da Manzonsa, wadannan Allah zai yi masu rahama, lallai Allah mabuyi ne, mai hikima” Tauba: 71.

            Da sauransu masu yawa, sai dai mu a nan ba muna halin kididdigewa ba ne, domin wannan bahasin an gina shi ne a kan yin ishara kawai, sai kuma ba da kofa ta yin tunani dangane da wannan lamarin, kuma a kowace kofa, wata kofar guda dubu za ta iya budewa a cikin ludufin Allah Tabaraka wa Ta'ala da kuma yalwar rahamarsa.

           Daga cikin alamomin jahiliyya akwai haimana a kan canfe-canfe da tatsuniyoyi, misali larabawa sun kasance suna canfa kukan hankaka da na mujiya, a yau kuma yammacin turai suna canfa lamba ta (13), a wancan lokacin masu duba da bokaye sun shahara sun ci kasuwarsu, a yau kuma muna ganin yadda mutane suka yi marhabin lale da mai karanta tafin hannu, masu ramli, masu bugun kasa, masu rufa ido da masu wankin ido wani abu da yake tafiya da hankalin jahilai da wawaye.

           Daga cikin halayen jahiliyya akwai yin saddu ga Qur'ani da kautar da mutane daga gare shi ta hanyoyin daban-daban, Nadir dan Haris ya kasance wanda yana daga cikin wadanda suka tafi kasar Farisa suka koya daga labaran sarakunansu, sai yana bin bayan Manzon Allah (s.a.w.a), idan Manzon Allah (s.a.w.a) ya tashi daga majalisa sai shi Nadir ya zauna a wannan majalisar ya kama ba su labari sannan sai ya ce: Ina gama ku da Allah wane ne mafi dadin labari ni da Muhammad? Domin sun kasance suna sifanta Qur'ani da tatsuniyoyin mutanen farko ko kuma labarai ne ake masa shibtar su safe da yamma ko kuma labari ne kirkirarre, ko kuma su dinga kururuwa da karfi a yayin da Manzon Allah (s.a.w.a) yake tilawarsa domin su shiga tsakaninsa da jinsa, Qur'ani yana siffanta wannan matsayar tasu da cewa: “Kuma wadanda suka kafirta suka ce: Kada ku saurara ga wannan Qur'ani, kuma ku yi ta yin kuwwa a ciki (lokacin karatun) sa, tsammaninku za ku yi rinjaye” Fussilat: 26. Allah Ta'ala ya ce: “Kuma idan sun ga wata aya, sai su juya baya su ce: Sihiri ne mai dorewa (marar tsayawa)” Kamar: 2.

To ga kuma jahiliyyar yau tana siffanta Qur'ani da irin wadancan siffofin cewa zancen Muhammad ne, kawai dai wani mutum ne ya yi amfani da kaifin kwakwalwar da yake da ita ta dan adam ba wai wahayi ne na Allah ba. Kuma sun yi kokarin wallafe-wallafe a kan abubuwa masu karo da juna a cikin Qur'ani (a tunaninsu fa) da suka gaza a kan niyyarsu ta rusa Qur'ani suka gagara yin hakan, kuma samuwarsa da kafuwarsa ta tabbata a gare su, sai suka juya – saboda tsabagen makirci da yaudara da tabewa – suna sace shi daga abubuwan da ya kunsa da sauke shi a aikace daga rayuwa ta yau da gobe, suka juyar da shi zuwa ga abin da ya yi kama da kasidu da wakoki wacce mawaka suke rerawa sai mazauna wannan majalisar masu sauraro su dinga bude muryoyinsu suna fadin (Allah, Allah, ya shaikh) suka juyar da shi ya zama hirzi (mai ba da kariya) ana daura shi a wuya ko a rataya a gidaje, iyakar kenan kar ka kara kar ka rage. Wannan salon kamar yadda kake gani ya fi hadari a kan salon Nadir dan Haris da ire-irensa, kuma shi ne mafi munin makirci da tasiri.

       Daga cikin fitattun tasarrufofinsu wadanda suke siffantuwa da su: Akwai kafewa a kan al’adu da akidun da suka gada daga magabata, tsananin riko da su, rashin bambaruwa daga gare su koda dalili da hujja sun kafu a kan bacinsu. Wannan tasarrufin sakamakon bijircewa da rashin sallamawa lafiyayyan tunani da kuma riko da ta’assubanci bisa la’akari da cewa wannan abin da suka jingina gare shi abu ne da yake da asali tun daga iyaye har zuwa kakanni don haka kimarsa ta sanya yana da tsananin wuya su watsar da shi. Kuma lallai Qur'ani ya yi ta maimaita wannan ma’anar a wurare da yawa ta yadda za mu iya fahimtar cewa lallai wannan na daga cikin bala’in da gabaki dayan Annabawa suka fuskanta. Allah Ta'ala ya ce: “Kuma idan aka ce masu: Ku bi abin da Allah ya saukar, sai su ce: A’a muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa, shin kuma koda ubannin nasu ba su hankaltar komai, kuma ba su shiryuwa?” Bakara: 170. “Lallai su, sun iske ubanninsu batattu. Saboda haka su, a kan gurabunsu suke gaggawa” Safat: 69-70. “Suka ce: Shin, ka zo mana ne domin mu bauta wa Allah shi kadai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance suna bautawa? To ka zo mana da abin da kake yi mana wa’adi da shi idan ka kasance daga masu gaskiya” A’araf: 70. “A’a, suka ce; lallai mu, mun samu ubanninmu a kan wani addini (na al’ada) kuma lallai mu, a kan gurabunsu muke masu neman shiryuwa. Kuma kamar haka, ba mu aika wani mai gargadi ba a gabaninka a cikin wata alkarya, face mani’imtanta sun ce: Lallai mu, mun samu ubanninmu a kan wani addini kuma lallai mu, masu koyi ne a kan gurabunsu” Zukhruf: 22-24. To wadannan ayoyin guda biyu na karshe suna nuni a kan cewa lallai wannan bala’in mai girma yana fuskantar duk wani wanda yake son ya ‘yantar da al'ummarsa ya kuma yi sa’ayi domin gyaruwarsu, da fadinsa Ta’ala: “Kuma kamar haka, ba mu aika wani mai gargadi ba a gabaninka” Zukhruf: 24. Kuma wannan bai kebanta da Annabawa su kadai ba.

          Kuma jahiliyyar yau ba ta da bambanci da jahiliyyar farko a cikin wannan, shaidu a kan haka suna da yawa, kuma al'ummarmu sun yi fama da wannan da yawan gaske; daga cikinsu akwai ra’ayin (tsuke tunani da yin rayuwa kwabo da kwabo irin ta mutanen da, tare da fada da duk wani ci gaba na zamani) kamar yadda wani masani daga cikin ‘yan Hauza ya tafi a kai.

          Daga cikin alamomin jahiliyya akwai rashin sanin Imami (jagora) na hakika; “Wanda ya mutu, alhali bai san Imamin zamaninsa ba, ya mutu mutuwar jahiliyya”[9]. Kuma da aka ce sani, ba wai ana nufin sanin suna ne kawai ba, a’a ana nufin ka san nauyi da takalifofin da suke a kanka game da shi, ka tsayu da su tsayuwa ta hakika. Sannan wannan gazawar a fili take wacce ta shafe mu game da Sahibul Asr (Imam Mahdi; rayukanmu fansa gare shi) kuma lallai add’ua da aka ruwaito ta siffanta irin wannan jahiliyyar “Ya Allah ka sanar da ni kanka, domin cewa madamar ba ka sanar da ni kanka ba, ba zan san Annabinka ba. Ya Allah ka sanar da ni Manzonka, domin cewa madamar ba ka sanar da ni Manzonka ba, ba zan san Hujjarka (Imam) ba. Ya Allah ka sanar da ni Hujjarka, domin cewa madamar ba ka sanar da ni Hujjarka ba, na bata daga addinina”[10]. Bata daga addini kuwa shi ne ainahin jahiliyya.

         Wannan kuma shi ne abin da yake bukatar a yi masa bahasi kammalalle game da wajabcin samuwar Imami kuma Hujja a kowane zamani, wannan kuma shi ne nauyi da aikin da yake a kanmu a zamanin gaiba game da Imam (aj) da bayar da amsa a kan da dama daga cikin tambayoyi da mushkiloli na tunani wadanda suke cushe a cikin lamarin Imamancin Imam. Abubuwa da yawa sun bace wa muminai game da shi, to ballanta wasunsu wadanda ba muminai din ba. Alhali shi Imam (aj) yana daga cikin (kofar Allah wacce ba a je wa Allah sai ta ita wannan kofar)[11]. To yaya za a yi wanda bai san kofar Allah ba ya shiryar zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta'ala, to mene ne a bayan Allah face bata bayyananne.

        Daga cikin alamominta akwai rusunawa abin duniya da rashin yarda da abin da ke koma bayan wannan (abubuwa na lahira wadanda ba a ganinsu) da inkarin gaibi, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma suka ce: “Ba ta zama ba, face rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama wadanda ake tayarwa ba” An’am: 29, “Kuma suka ce: Babu komai face rayuwarmu ta duniya, muna mutuwa kuma muna rayuwa (ta hanyar haihuwa), kuma babu abin da ke halaka mu sai zamani, alhali kuwa (wannan maganar da suke fada) ba su da wani ilimi game da ita, ba su bin komai face zato” Jasiya: 24. Sai Qur'ani ya zo domin ya kafa masu rayuwa madaukakiya domin su rayu saboda ita “Kuma ban halicci aljannu da mutane ba sai domin su bauta min” Zariyat: 56. “Ya ce: Ya ku mutanena! Ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta face shi, shi ne ya kaga halittarku daga kasa, kuma sai ya bar gina ta a hannunku, sai ku neme shi gafara, sannan ku tuba zuwa gare shi, lallai Ubangijina makusanci ne mai karbawa” Hud: 61. “Sannan kuma muka sanya ku masu kalifanci a cikin kasa daga bayansu, domin mu ga yaya kuke aikatawa” Yunus: 14. Don haka shi mutum ba an halicce shi ba ne domin wannan duniyar har da zai karar da gabaki dayan himmarsa gare ta, a’a an sanya shi kalifa ne a doron kasa domin ya gina ta ya kuma sanya ta gonarsa wacce zai girbi lahira da ita, sannan mahaliccinsa sai yi masa hisabi na duk ayyukansa domin ya ga mene ne abin da ya aikata. To kuma tsawatarwar Allah za ta zo ga irin wannan mutumin da ya yi nutso cikin tarkacen duniya; “Shin mutum na zaton a bar shi sagaga (wato babu manufar komai game da shi)? Shin bai kasance digo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)?! Sannan ya zama gudan jini, sannan Allah ya halitta shi, sannan ya daidaita gabobinsa. Sannan ya sanya daga gare shi nau’oi guda biyu; namiji da mace? Ashe wannan bai zama mai iko ba bisa ga rayar da matattu?!” Kiyama: 36-40. Haka yake tsarki ya tabbata gare ka, ya Ubangiji kai ne mai iko a kan wannan da a kan dukkan komai ma. Na’am sai dai wannan ba zai hana mutum ya nemi rabonsa na wannan duniyar ba, amma da sharadin kada ya zama ya mayar da shi hadafinsa da magaryar tukewarsa, a’a sai dai kawai ya mayar da shi tsani na isa ga hadafinsa na hakika wanda shi ne samun yardar Allah Tabaraka wa Ta'ala; “Kuma ka bida a cikin abin da Allah ya ba ka, gidan lahira kuma kada ka manta da rabonka daga duniya, kuma ka kyautata, kamar yadda Allah ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nemi barna a cikin kasa, lallai ne Allah ba ya son masu barna” Kasas: 77. Don haka mallakar abin duniya ba wai zari ne ko nuna gazawa ba; ya zo a ruwaya cewa: “Duniya ita ce wajen noman lahira”[12]. A wani hadisin daban kuma: “Duniya gidan hada-hadar waliyyan Allah ce”[13]. Domin a cikinta suke hada-hadar kasuwancinsu tsakanininsu da Allah, fataucin da ba ya yin tasgaro.     

       Daga cikin alamomin jahiliyya akwai warwatsuwa, rarrabuwar kai da tarwatsawa kowa ma ya rasa, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma kada ku kasance daga mushrikai. Watau wadanda suke rarrabe addininsu kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai” Rum: 31-32. Kuma duk wadannan suna faruwa sakamakon tarwatsawarsu ga dunkullen abu guda wanda zai zama sanadin haduwarsu waje guda wanda shi ne tauhidi da dayanta Allah Tabaraka wa Ta'ala. Kuma ya sanya dakin Ka’aba mai tsarki a matsayin wani alaminsa. Sai dai al'ummomin da suka yi nisa ga barin Allah suna karkasa da tarwatsa duniyar kasashe-kasashe, gari-gari a matakin farko, har kasashen duniya suka tasamma fiye da kasa (180). Sannan suna raba kan kabila-kabila, suna rarraba gungun jama’a-jama’a har a cikin kasa guda sai su rarraba su a kan bambancin tunani da fikira, a ce wannan dan gurguzu ne, wannan kuma dan jari hujja ne tare da cewa duk fa ‘yan kasa guda suke, kuma kabila daya ma, addini daya, amma sai su rarraba su tunani daban-daban har a cikin addini dayanma ba su kyale ba, kai wuce nan ma har a cikin mazhaba guda, sai a wayi gari kowace al'umma an rarraba ta kungiya-kungiya haka dai; “Kowace kungiya suna masu farin ciki da abin da yake a gare su” Mu’uminun: 53. Kuma Qur'ani ya ja hankali a kan cewa wannan rabe-raben yana daya daga cikin alhakin nisanta daga tsarin Allah; Allah Ta'ala ya ce: “Ka ce: Shi ne mai iko a kan ya aika da wata azaba a kanku daga samanku, ko kuma daga karkashin kafafunku, ko kuma ya gauraya ku kungiyoyi, kuma ya dandana wa shashenku masifar sashe, ka duba yadda muke sarrafa ayoyi, tsammaninsu suna fahimta” An’am: 65. Amma musulunci ya zo domin ya dunkule su ta hanyar wannan Qur'anin Allah Ta'ala ya ce: “Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba, kuma ku tuna ni’imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance makiya sai ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku saboda haka kuka wayi gari da ni’imarsa yan uwa, kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta sai ya tsamar da ku daga gare ta, kamar wannan ne Allah yake bayyana maku ayoyinsa, tsammaninku za ku shiryu” Ali Imran: 103. “Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to lallai ma’ishinka Allah ne, shi ne wanda ya karfafa ka da taimakonsa, da kuma muminai. Kuma ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu, da ka ciyar da abin da ke cikin kasa gabaki daya, da ba ka sanya soyayya a tsakanin zukatansu ba, kuma amma Allah ya sanya soyayya a tsakaninsu, lallai shi mabuwayi ne mai hikima” Anfal: 63-63.

       Daga cikin bayyanannun alamomin jahiliyya akwai tsoron mutuwa da dukkan abin da yake nuni ko ishara gare ta, wannan kuma saboda sun yi asarar lahira ne, suka sanya mafi makurar hankoronsu kosar da sha’awoyinsu da kwadayinsu; “Ka ce: Idan gidan lahira ya kasance saboda ku a wurin Allah kebe ba da sauran mutane ba, to kuyi gurin mutuwa, idan kun kasance masu gaskiya. Kuma ba za su yi gurinta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar, kuma Allah masani ne ga azzalumai. Kuma lallai ne za ka same su mafiya kwadayin mutane a kan rayuwa, kuma su ne mafiya kwadayin rayuwa daga wadanda suka yi shirka, dayansu yana son da za a rayar da shi shekara dubu, kuma hakan ba ya zama mai nisantar da shi daga azaba domin an rayar da shi, kuma Allah mai gani ne ga abin da suke aikatawa” Bakara: 94-96. “Kace: Ya ku wadanda suka tuba (yahudu)! Idan kun riya cewa ku ne zababbun Allah ba sauran mutane ba, sai ku yi gurin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya. Kuma ba za su yi gurinta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar, kuma Allah ne masani ga azzalumai” Juma’a: 6-7. “Sannan idan tsoro ya zo, sai ka gansu suna kallo zuwa gare ka, idanunsu suna kewayawa, kamar wanda aka dauke hankalinsa saboda (magagin) mutuwa” Ahzab: 19. Sai dai Qur'ani yana tabbatar masa game da hakikar wannan tsoron wanda babu matserata daga gare shi: “Ka ce: Lallai mutuwar nan da kuke gudu daga gare ta, to lallai ita mai haduwa da ku ce sannan kuma ana mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane domin ya ba ku labari game da abin da kuka kasance kuna aikatawa” Juma’a: 8. “Kace: Gudun nan ba zai amfane ku daga mutuwa ko kisa ba, kuma har in kun gudu, ba za a jiyar da ku dadi ba face kadan” Ahzab: 16. “Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske ku, kuma koda kun kasance a cikin ganuwoyi ingantattu”, Nisa’i: 78. “Kace: Koda kun kasance a cikin gidajenku da wadanda aka rubuta masu mutuwa sun fita zuwa ga wuraren kwanciyarsu” Aali Imran 154. Don haka rashin tsoron mutawa ba ya samuwa sai idan an yi imani da Allah an kuma aikata ayyukan kwarai da gina lahira da yardar da Allah Tabaraka wa Ta'ala da kuma kusanta zuwa gare shi.

      Zuwa yanzu ina ji a jikina cewa lallai ni, na gabatar da wasu isharori wadatattu kuma na bude maku kofofin yin tunani daidai gwargwaado a wannan bangaren. Domin mataki mai muhimmanci na magance cututtukanmu da ke damun rayuwar zamantakewar al'umma shi ne gano ciwo sannan a tafi ga binciko yadda za a magance shi.

        Yanzu ya bayyana a wurinmu ta hanyar wadannan nukododin ma’anar jahiliyya a rayuwar mutane a yau, kuma mun san cewa ludufin Allah ga bayinsa madawwami ne, kuma ba ya kebanta da wasu jama’a banda wasu, don haka jahiliyyar jiya, ba wai ta fi jahiliyya yau ba ce, ba kuma wasu halaye na daban take da su ba, wacce a sakamakon haka Allah ya saukar masu da Qur'ani ya kuma turo masu da Manzo, amma kuma sai ya bar jahiliyyar yau sagaga, ba ta da bukatar muslihi wanda yake shi ne Al-Hujja dan Hasan (rayukanmu su zama fansa gare shi), kuma ba mu da bukata zuwa ga Qur'ani domin ya tsamar da mu daga zurfin rijiyar jahiliyya zuwa ga kololuwar musulunci.



[1] Al-Kafi: 1/53, Babin Takalid, hadisi na 1.

      Kuma wannan isdilahin mai muhimmanci na Qur'ani wato (Ibada), yana bukatar a bayyana shi saboda rashin fitowarsa a fili a cikin kwakwalen mutane, sai suke tsammanin cewa ibada tana nufin sallah ko kuma sujjada amma ba tana nufin da’a ba, shi ya sa ba su samun wannan tsarkin a cikin addininsu, cewa bayan sun yi sallah da azumi amma sauran mu’amalolinsu da dabi’unsu na rayuwa sai ka ga suna yinsu ta hanyar da Allah bai saukar ba, wanda wannan abu ne mai hadari, dole ne a gusar da wannan shubuhar daga gare su, shi ya sa aka ruwaito daga Imam Jawad (as) a cikin fadinsa: “Wanda ya saurari mai magana to hakika ya bauta masa, to idan wannan mai maganar ya kasance dan aiken Allah ne, to hakika ya bauta wa Allah, amma idan mai maganar yana yi ne da harshen ibilis to….” Tuhaful Ukul: shafi na 336.    

[2] Al-Rasa’ilul Ashara: shaikh Dusi, shafi na 317.

[3] Kamilul Ziyarat: shafi na 201.

[4] Biharul Anwar: 76/136.

[5] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Nikah; Abwabu muqaddimatil Nikah wa adabih, babi na 28, hadisi na 1.

[6]  Biharul Anwar: 22/467.

[7] Al-Kafi: 5/59, Babin: Umarni da kyakyawa da hani ga mummuna.

[8] Nahajul Balaga: Huduba ta 27.

[9] Kamaluddin Wa Tamamul Ni’imat: shafi na 409.

[10] Al-Kafi: 1/337.

[11] Al-Kafi: 1/196.

[12] Awalil Li’ali: 1/267.

[13] Minhajul Bara’ati Fi Sharhi Nahjul Balaga: 15/203.