Jahiliyyar Yau
Jahiliyyar Yau
Lallai tabbas mutane a yau suna rayuwa ne a wani sabon yanayi na jahiliyya – koda kuwa wasu sun kira abin da musulunci – a gwargwadon irin ma’anar da Qur'ani ya baiwa kalmar ta jahiliyya, domin shi bai ba ta ma’anar cewa wani yanki ne na lokaci wanda ya riga ya kare bayan bullowar hasken musulunci ba, a’a wata dabi’a ce ta zamantakewar al'umma wacce al'ummar da kanta ta yadda ta rayu a wannan yanayin, mai jawo zubewar darajar ita wannan al'ummar a sakamakon bijirewa shari'ar Allah Ta'ala da ta yi; “Shin hukuncin jahiliyya suke nema, shin wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah ga mutane wadanda suke yin yakini (masu tabbataccen imani)” Ma’ida: 50. Kuma Qur'ani ya ja kunne ga masu nemanta yayin da ya ce: “Kuma kada ku yi fitar tabarruji irin tabarrujin jahiliyyar farko” Ahzab: 33. Amma yanzu kamar wani take ne na samuwar jahiliyya ta biyu wacce a yau ga jama’a nan suna fama da rayuwa cikin tsananinta, wahalhalunta da cutarwarta.
Kai ba ma haka ba! Jahiliyyar yau ta hade da jahiliyyar zamanin baya sun hade sun zama abu guda, inda za ka samu mai karfi yana murkushe mai rauni, luwadi kuwa ya zama cikin dokoki na kundin tsarin mulki a wasu wuraren yadda har aure yakan gudana a tsakanin namiji da namiji, zina kuwa kazantar nan mai wari wacce take ta yaduwa tana kara game ko’ina a duniya an mayar da ita wata aba kamar barbarar dabbobi, tana ta kara yada ciwurwuka masu kashe garkuwar jiki kamar irinsu aids (sida) da makamantansa. Sannan in kai maganar tauye mudu da sikeli da dukkan dangoginsa sun mamaye sun zama ruwan dare ba yaro ba babba, abin bai tsaya a nan ba har da gwamnatoci, babu adalci a tsakanin alakoki tsakanin al'umma abin da ake kira da (kilo daya a madadin kiloli guda biyu), da kuma rikon ahbar da ruhbanawa da sauran sarakunan bata na daga shaidanun aljanu da mutane sashensu yana yin ishara ga sashe da kawataccen zance bisa ga rudu, a matsayin iyayengiji koma bayan Allah, suna kuma haramta abin da Allah ya halatta, suna halatta abin da Allah ya haramta, da abubuwan bautawa da ake bauta masu koma bayan Allah subhanahu wa Ta’ala wadanda ba su kidayuwa kuma ba wai sun takaita ga sake-sakin duwatsu ne ba kawai, a’a har yanzu shaidanu suna nan suna ta kara fantsama abin. Shaidanun aljanu da mutane sashensu yana yin ishara ga sashe da kawataccen zance bisa ga rudu kuma suna yin saddu ga hanyar Allah madaidaiciya; “Lallai ne, zan zauna in katange masu tafarkinka madaidaici (wato zan batar da su). Sannan kuma hakika, zan je masu daga gaba gare su, kuma daga baya gare su, kuma daga bangarorin damarsu da bangarorin hagunsu, kuma ba za ka sami mafi yawansu masu godiya ba” A’araf: 16-17. “Kuma kada ka zauna a kowane tafarki kuna (masu yiwa mutane) kule, kuma kuna kangewa daga hanyar Allah ga wanda ya yi imani da shi, kuma kuna nemanta ta zama karkatacciya” A’araf: 86. Waye ya fi wadannan masu katangewa daga tafarkin Allah ga wanda ya yi imani kuma suna neman sai sun karkatar da ita daga kan lafiyayyar fidira, fasikanci tare da kafa tarkuna na fitina da haifar da adawa a tsakaninsu, da tarwatsa harkokin tattalin arziki, da samar da kwararru wadanda ba su da aiki sai bata tarbiyya da kyawawan dabi’u na al'umma da sauransu.
Duk wadannan suna daga cikin siffofin da ke alamta jahiliyya a zamanin yau haka nan ma a kowane sauran zamani da kowane guri. Wannan ma’ana ita ce ainahin ma’anar da Qur'ani ya bayyana a kan jahiliyya kuma ya zama dole mu karbe ta, mu kuma fahimce ta.
Domin karin bayani, za mu kawo misalai na akida da ayyukan jahiliyyar farko mu kamanta su da jahiliyyar yau wacce muke rayuwa a cikinta, a wannan bayanin ina son in fitar da hadafofi kamar haka:
1- Daidaita ka’idoji da isdilahohin Qur'ani da cirato ma’anoninsu wadanda Qur'anin yake nufi, sannan sai gusar da kurar da ta lullubbe su a sakamakon gafala daga shi Qur'anin, da yadda ake horar da hankulla a cikinsa amma ba tare da an koma gare shi ba.
2- Tattaro tare da game dukkan bukatu zuwa ga Qur'ani, idan muka fahimci cewa lallai mutane sun koma ga jahiliyyar farko, to ya zama dole tana da bukatar komawa ga Qur'ani domin ya sake ceto al'ummar, ta hanyar yin riko da hannunta da mika ta ga tsarin musulunci na hakika.
3- Girmama fikirar Imam Mahdi (rayukanmu fansa gare shi), tare da tsayar da dalili na ilimi a kanta, domin su mutane lokacin da suka koma ga jahiliyyarsu ta farko, to Qur'ani shi kadai dinsa ba zai iya motsin da zai tseratar da su ba, a’a dole yana bukatar wani mai motsi wanda zai baje shi a faifai, kamar dai yadda Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana yi, koda yake shi wannan bai kasance Annabi ba, saboda yankewar Annabta daga kan Annabi Muhammad (s.a.w.a), to sai dai wadannan siffofin ba su haduwa ga wani in ba Hujjatar Allah ibn Hasan (rayukanmu fansa gare shi) ba. Ga ma alamomin bayyanarsa nan suna ta bayyana, yinin da aka yi alkawarinsa yana ta kara kusantowa[1]. Magana dalla-dalla game da wannan za ta zo a bahasi mai zaman kansa dangane da shi Imam (as).
[1] Shi ya sa aka rawaito a hadisi cewa shi Imam (as) zai zo da musulunci sabo, Qur'ani sabo, amma a nan dalalarsa wacce ta dace da abin nufi a nan ba tana nuna cewa shi Imam (as) ba zai fito daga cikin kewayen musulunci ba da Qur'anin kakansa (s.a.w.a) ba, a’a abin nufi shi ne zai goge kurar da ta lullube Qur'ani ya kuma gusar masa da daudar aka dora masa shekara da shekaru, ya kuma dawo masa da rayuwarsa sabuwa fil.