Hakkin Da Yake Kan Hauza Na Ta Dawo Da Tsarin Qur'ani

| |times read : 433
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Hakkin Da Yake Kan Hauza Na Ta Dawo Da Tsarin Qur'ani

Na yi imanin cewa wuri na farko a cikin wuraren zamantakewar al'umma wanda nauyi na jagoranci ya hau kansa shi ne Hauzar ililmi da dalibanta, madaukakanta, masu hudubarta da malamanta, domin gyaruwar al'umma yana nan a karkashin gyaruwar hauzar ilimi, haka ma lalacersu tana nan karkashin lalacewar Hauzar ta ilimi, muna neman tsari daga Allah. Ya zo a hadisi madaukaki daga Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Abubuwa guda biyu daga al'ummata, idan suka gyaru to al'ummar gaba dayanta ta gyaru, idan kuma suka baci, to dukkan al'ummar sun baci, aka ce ya Manzon Allah (s.a.w.a) su waye su? Ya ce: Malamai da sarakuna”[1].  

 Kuma lallai na fada a cikin wasu littafaina[2], cewa wani abu na kaico hakikanin kaico, shi ne bacewar Qur'ani daga cikin manhajoji na koyarwa a Hauzozin ilimi, domin sun samar da wani tsari wanda dalibi ba ya bukatar ya yi zurfi cikin ilimummukan Qur'ani mai girma, tun daga marhalar farko ta fara karatunsa har zuwa marhalar karshe, ba ya bi ta kansa sai a lokacin da yake bukatar kafa hujja da shi a kan wata ka’ida ta nahawu ko wani bahasi na usul da wata mas’ala ta fikihu, sai ya wayi gari gurin gwaji na karfafa tunanin hankali amma ba wai abincin ruhi da zuciya ba ko kuma waraka ga rayuka ba. Watakila ma dalibin Hauza zai iya kai wani matsayi a fikihu da usul amma ba ya rayuwa irin rayuwar Qur'ani kuma bai yi nutso cikin ma’amala da Qur'anin ba da kwankwadar iliminsa a matsayin sakon da zai tallafa masa ya gyara kansa ba, kai kwanaki ma da satuttuka za su iya wucewa ba tare da ka ga dalibin ilimi ya dauki Qur'ani domin ya karanta wasu daga cikin ayoyinsa, da yin tadabburi a cikinsu, saboda rashin samun dangantaka mai zurfi tsakanin dalibin da Qur'anin, amma da a ce ya samu guzurinsa da abincinsa a cikinsa wanda zai wadatar da shi daga waninsa da bai iya barinsa ba. Wannan kuma musifa ce mai girma a Hauzar ilimi da wuraren zamantakewar al'umma, watakila ma ka iya samun wadanda ba su iya karanta shi yadda ya dace ba.

       To amma tunda yake sakon Hauzar ilimi wacce take dauke da nauyinsa shi ne gyara al'umma da kusantar da su ga Allah Tabaraka wa Ta'ala, to lallai tun a farko, abu mai muhimmanci gare su shi ne su a kashin kansu su fahimci Qur'anin da himmantuwa wajen ganin sun aikata shi a aikace, domin ita al'umma ba za ta zama cikin alheri ba sai idan ta yi riko da Qur'aninta, ta shiryu da shiryuwarsa, ta haskaka da haskensa, kamar yadda mashhurin hadisin sakalain ya nunar: “Ni mai bar maku nauyaya guda biyu ne Littafin Allah da alayena iyalan gidana, madamar ku ka yi riko da su a bayana, ba za ku taba bata ba har abada”[3].



[1] Al-Khisal: Abwabul Isnain, hadisi na 12.

[2] Wasaya wa Nasa’ih Ilal Khudaba’i wa Dalabatil Hauzatil Sharifati (maganar ta gabata a cikin wannan mujalladin).

[3] A can baya an ambace shi.