Wajabcin Komawa Ga Qur'ani
Wajabcin Komawa Ga Qur'ani
Shin yanzu bayan duk wadannan bayanan muna kuma bukatar wasu karin bayanan masu kwadaitarwa domin komawa ga Qur'ani da rayuwa a karkashin inuwarsa, kuma shin akwai wanda ya yi saura a cikinmu wanda ba ya jin cewa lallai mun tafka asara saboda nisantarmu ga Qur'anin?
To yanzu mu zo gabaki dayanmu mu koma ga Qur'ani muna masu tuba gare shi da nadama kuma muna masu rokonsa a kan ya dawo ya jagorance mu da shiryar da mu zuwa ga Allah Tabaraka wa Ta'ala, kuma dole ne gare mu, mu yi tunanin wace hanya ce za a bi domin ganin an fidda wannan Littafi mai girma daga halin da mu da kanmu muka jefa shi a ciki da hana shi taka rawarsa a cikin rayuwar al'umma.
Watakila ka ce: Ai duk irin wadannan muna ganinsu ta hanyar makarantun koyon Qur'ani, haddarsa, tajwidinsa, da koyon ka’idodin karanta shi da rubuta shi.
Amma ni sai na ce: Tare da girmamawa ta ga dukkan wadannan, sai dai wannan bai wuce a kira shi bayar da muhimmanci ga bawo ba, alhali mafi muhimmanci shi ne abin ko tsokar da ke cikin dan itacen (lub)[1], domin shi lafazi ko magana kamar matsayin mazubi ne na isar da ma’ana kuma kamar bawo yake mai ba da kariya ga maganar wacce take a matsayin tsoka, kuma tsani ne na isar da ma’ana zuwa kwakwalwa, to shin zai wadatar a muhimmantar da bawo a manta da tsokar? Domin abin da ake nema shi ne dawowa da ruhin Qur'ani tare da abubuwan da ya kunsa, ma’anoninsa, fikirorinsa da fahimtarsa, kuma ko shakka babu cewa abu na farko da ake muhimmantarwa tilawarsa ce kawai sai sanin ma’anonin kalmominsa da kiyaye ka’idodin larabci na yadda za a iya furta haruffa daidai (makharijul huruf).
[1] Wato mu dauki misalin kayan marmari, kamar misali a ce ayaba ko mangwaro, ai tsokar da ke can cikin bawon ita ce muhimmiya ba bawon da yake daga waje ba wanda shi aikinsa shi ne yana lullube mafi yawa daga cikin kayan marmari. Kodayake a nan a kan samu bambanci daga wannan abin marmarin zuwa wancan.