Rayuwa A Kusa Da Qur'ani
Rayuwa A Kusa Da Qur'ani
Na yi rayuwa irin ta almajirci wato rayuwa a kusa da Qur'ani, na rayu shekara da shekaru cikin kulawarsa a lokacin samartaka, na sauke tun ina dan shekara 20 zuwa 25, har ya cakudu da jini da tsokata, tunanina, harshena da zuciyata, kuma na kasance a tilawar da nake yi masa tare da zurfafa nazari a cikin tafsirinsa guda biyu masu muhimmanci, da fatan Allah ya kara masu daukaka, don ina mai tabbatar da cewa sun taka rawa a cikin rayuwata ta ilimi da fikira wadannan tafsiran guda biyu kuwa su ne (Al-Mizan da Fi Zilalil Qur'ani) har sai da na kammala su, na yi kulasar muhimman abubuwan da suke kunshe a cikinsu, saboda in samu damar sake bibiyarsu a kai a kai, har wadancan fikirorin suka zauna a cikin raina, ruhina da zuciyata a wancan lokaci mai faranta rai.
To mai na samu a farfajiyar Qur'ani? Mene ne wanda yake rayuwa a karkashin kulawar Qur'ani zai samu? Zai ga girman Allah Ta'ala yana tajalli a cikin ayoyinsa, dokokinsa, sunnoninsa da kudirarsa a cikin dukkan komai, kasa dukkanta damkarsa ce, a ranar kiyama kuma sammai ababen nadewa ne da damarsa, kuma izza gaba dayanta ta Allah ce, karfi da mulki duk nasa ne shi kadai, kuma shi ne wanda yake gadon kasa da abin da yake a kanta, kuma makomar bayi a wajensa take, kuma shi ne mafi kusanta zuwa gare su daga jijiyar wuyansu, kuma yana shamakancewa a tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma babu wani abu da zai iya mallakar wani abu na amfani ko cutarwa sai da izininsa, a saboda haka duk wani abu sabanin Allah Tabaraka wa Ta'ala yana kaskanta a gaban wanda yake dauke da Qur'ani, komin girmansa a zahiri, koda masoyansa da mabiyansa za su himmantu wajen ganin sun girmama shi da kambama shi, amma a nan ma din kudurar Allah za ta lakume abin da suke karya da shi, yanzu ka duba ina Iramawa suke masu zubin kirar jiki (jibga-jibgan mutane) babu su, ina Fir’auna ma’abocin turaku (da rundunar mayaka wadanda suka kafe masa mulkinsa) babu shi, babu ma’abocin taskokin nan da mabudansu suke nauyaya ga jama’a mazowa karfi. Amma wanda yake dauke da Qur'ani to shi karfinsa manne yake da karfin Allah, don haka ba ya tsoron waninsa (Allah); “Misalin wadanda suka riki wadansu masoya wadanda ba Allah ba, kamar misalin gizo-gizo ne wanda ya riki wani dan gida, alhali kuwa mafi raunin gidaje shi ne gidan gizo-gizo, da sun kasance suna sani” Ankabut: 41. Sannan ya zo a hadisi cewa; “Wanda duk ya ji tsoron Allah, to Allah zai tsoratar da dukkan komai daga shi”[1].
To daga nan ne za ka ga cewa lallai wannan babban karfin wanda kamar yadda ya zo a Qur'ani “(Sai ga igiyoyinsu da sandunansu) ana suranta su a gare shi, daga sihirinsu cewa lallai suna tafiya da sauri” Da Ha: 66. Wai shi mai iko ne yana iya isa ga dukkan abin da yake so, ashe fankam fayau ne domin sai aka wayi gari yana zagwanyewa kamar yadda gishiri yake zagwanyewa a cikin ruwa ba tare da an yi wani yaki ko kawo masa hari daga bangaren makiya na zahiri ba. Shi ya sa Allah yake ba ka labari game da wanda yake bayan halakarsu: “Sai Allah ya je wa gininsu daga harsashensa (tushensa), sai rufin ya fada a kansu daga samansu, kuma azaba ta je masu daga inda ba su sani ba (ba su yi shu’uri ba). Sannan a ranar kiyama, (Allah) yana kunyata su, kuma yana cewa: Ina abokan tarayyar tawa wadanda kuka kasance kuna gaba da jayayya (da annabawa) a wajen daukaka sha’aninsu? Wadanda aka baiwa ilimi suka ce: Lallai ne kaskanci da cuta a yau sun tabbata ga kafirai” Nahl: 26-27.
Kuma da sannu za a ga alkawarin Allah da samun natsuwa ga muminai ta samu domin akiba tasu ce, amma sai idan bayan sun fuskanci: “Wahalhalu da cuta sun shafe su, kuma aka tsoratar da su har manzonsu da wadanda suka yi imani tare da shi suce: Yaushe ne taimakon Allah zai zo. To lallai ne, taimakon Allah yana kusa” Bakara: 214. Kuma lallai ba makawa ga fitina da jarabawa domin Allah ya tace masu imani; “Alif, Lam, Mim. Ashe mutane suna zaton a barsu su ce: Mun yi imani, alhali kuwa ba za a fitine su ba? Kuma lallai hakika, mun fitini wadanda suke a gabaninsu, domin lallai ne Allah ya san wadanda suka yi gaskiya, kuma lallai ya san makaryata” Ankabut: 1-3. To daga nan ne mumini zai samu tabbatuwa a kan kafafunsa duk irin wuya da tsananin da zai fuskanta domin ya san wannan Sunnah ce daga cikin sunnonin Allah ga bayinsa, don haka wajibi ne a gare shi ya gaskata a duk yadda matsaya ta kama, kuma da sannu Allah zai sakantawa masu gaskiya, kuma lamurra za su saukaka a gare shi cewa dukkan abin da yake wakana a kan kulawar Allah Subhanahu wa Ta’ala ne, Allah Ta'ala ya ce: “Lallai fa kai (ya kai Manzo) kana a kan kulawarmu” Dur: 48, “Wancan, saboda cewa lallai kishirwa ba ta samunsu, haka nan wata wahala, haka kuma wata yunwa a cikin hanyar Allah, kuma ba su daukar wani mataki wanda yake fusata kafirai, kuma ba su dandana wa kafirai wata damuwa ba face an rubuta masu da shi ladar aiki na kwarai, lallai ne Allah ba ya tozarta ladar masu kyautatawa” Tauba: 120.
Kuma da sannu zai gani albarkacin daukaka ta imani wanda duk ya umarci zuciyarsa da ma’arifa madaukakiya wannan al'ummar wacce take ta faman lallage a kan fako tana rayuwar karya da yaudarar kai tana yi wa kanta fatan aminci amma batacce, waliyyan shaidanu suna kawata masu daga dukiyoyi, makamai da sha’awace-sha’awacen da suke ta gogoriyo a kansu suna yakar juna a kan abin da ba zai ci gaba da wanzuwa gare su ba a’a sai dai ma ya zama azaba gare su. Suna kirkirawa kawukansu iyayengiji sai su dinga da’a gare su da bauta masu tare da mika masu wuya, suna shirya taruka da bukukuwa da shagulgula suna yin yanka domin kawai don neman samun kusanci da su ba kuma dabbobi kawai suke yankawa ba, a’a, hadda ‘yan adam, kuma suna barnatar da biliyoyin dukiyoyi a banza.
Kuma da sannu zai gani da kansa cewa ba shi kadai ba ne ballantana ya samu rauni ko kaskanci ko kankan da kai ko sallamawa, kuma abin da yake fuskanta da wanda yake gani da wanda yake rayuwa a cikinsa ba kansa farau ba, ba kuma shi ne farkon wanda ya fara cin karo da shi ba; “Kace: Ban kasance farau ba daga Manzanni, kuma ban san wace irin ma’amala za a yi game da ni ko game da ku ba, ni abin da nake bi kadai shi ne abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban kasance ba face mai gargadadi mai bayyanawa” Ahkaf: 9. A nan zai ga Annabawa masu girma sun gabace shi da waliyai masu karamci a kan wannan hanyar, da wadanda ke dauke da sako da masu gyara da bayin Allah salihai, kuma sun fuskanci matsaloli fiye da yadda shi yake fuskanta, kuma suka yi hakuri a kan mafi tsananin abin da yake hakuri da shi, haka nan ma sun fuskanci matsala daga al'ummar da suka yi rayuwa da ita fiye da yadda shi yake fuskanta, kuma yanayin shi din dai ne babu bambanci, Allah Ta'ala yana cewa: “Daga cikinsu akwai mai neman shiryuwa, amma masu yawa daga cikinsu fasikai ne” Hadid: 26. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku lizimci kawukanku, wanda ya bace ba zai cuce ku ba idan dai ku kun shiryu” Ma’ida: 105.
Kuma da sannu zai ga girmamawar Allah ga bayinsa yayin da zai yi magana da su shi da kansa, ya fuskantar da zancensa gare su kai tsaye, Allah mai girma mabuwayi mahaliccin sammai da kasa, ma’abocin sunaye kyawawa, da kansa ya aiko masu da sakonsa, ya kuma yi masu alkawari da kansa; to wace irin karramawa ce mafi girma daga wannan, wace irin fifitawa ce sama da wannan? “Hakika, tabbas mun girmama ‘yan adam, muka dauke su a cikin kasa da teku, muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda muka halitta, fifitawa” Isra’i: 70. To yaya kake ganin dabi’ar mutum, alhali yana karanta sakon masoyinsa kai masoyinma ba karami ba babban! (Qur'ani alkawarin Allah ne ga halittunsa saboda haka ya kamata ga dukkan mumini ya dinga yin duba zuwa gare shi)[2].
Kuma da sannu zai gani cewa dukkan komai a wannan duniyar an halitta shi ne a kan wani awo da wani lissafi kiyayayye, Allah Ta'ala ya ce: “Lalle mu, kowane abu mun halitta shi ne a aune (a kan awo)” Kamar: 49. “Kuma ba mu saukar da shi ba face bisa gwargwado sananne” Hijr: 21. “Kuma muna dora ma’aunan adalci” Anbiya’i: 47. Kuma dukkan halittu a daidaiku da a jama’a jama’a suna tafiya ne bisa sunna tabbatacciya “Sunnonin (hanyoyin) wadanda suke a gabaninku” Nisa’i: 26. “Kuma babu wata dabba a cikin kasa, kuma babu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa face al'ummu ne misalanku. Ba abin da muka bari ba mu yi bayaninsa ba a Littafi, sannan kuma zuwa ga Ubangijinsu za a tattara su” An’am: 38. Babu wani wanda ya isa ya fita daga cikin wannan dokar mai girma ta Allah; “To ba za ka taba samun musanya ba ga hanyar Allah, kuma ba za ka taba samun juyarwa ba ga hanya Allah” Fadir: 43. To ta yaya mutum zai bautawa wanin Allah Tabaraka wa Ta'ala alhali shi din ba zai iya tsira daga kamun sunnoninsa da dokokinsa ba, kuma babu damar yin wasa, wargi da lahawu; “Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan a karon kawai ba, tsarki ya tabbata a gare ka” Aali Imran: 191. “Kuma ban halitta aljannu da mutane ba sai domin su bauta min” Zariyat: 56. “Da mun yi nufin mu riki wani abin wasa (bisa kaddarawa) da mun rike shi daga gurinmu, idan da mun kasance masu aikatawa” Anbiya’i: 17. Saboda haka babu wata hanya ta faruwar abubuwa haka siddan a makance abin da so da yawa mulhidai suke amfani da hakan wajen wawaitar da hankula da tunanin mutane shekara da shekaru suna batar da su. Tabewa ta tabbata ga masu binsu da su wadanda ake bin. Tabbas a bayan halittar mutum akwai wani hadafi wanda ya zama dole ya rayu a sabili da shi, ya baje dukkan karfinsa domin ganin ya same shi, wanda wannan abu shi ne neman yardar Allah Tabaraka wa Ta'ala.
Kuma a cikin Qur'ani za ka ci karo da alkawarin Allah na ba da taimako a sarari da a boye a kan kowace matsaya, tsanani, gumurzu da yakar zuciya mai umarni da aikata mummuna ko shaidan, kuma lallai Allah zai ci gaba da kasancewa tare da shi; madalla da samun mataimaki kamarsa, madamar dai shi din yana tare da Allah. Allah Ta'ala ya ce: “Lallai wadanda suka ce Ubangijinmu shi ne Allah, sannan suka daidaitu, mala’iku na sassauka a kansu, (suna ce masu) kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi bakin ciki, kuma ku yi bushara da aljanna wacce kuka kasance ana yi maku wa’adi da ita. Mu majibintanku (mataimakanku) ne a rayuwar duniya da kuma a cikin lahira, kuma a cikinta kuna da abin da rayukanku ke sha’awa, kuma kuna da abin da kuka nemi a kawo maku a cikinta. (Wadannan) Liyafa ce daga (Allah) mai gafara, mai jin kai. Kuma wane ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na kwarai kuma ya ce: Lallai ni ina daga masu sallamawar al’amari zuwa ga Allah” Fussilat: 30-33. Ayoyi masu yawa wadanda suke ba da labarin samun natsuwa a cikin zuciyar muminai, da kawo daukin mala’iku masu alama da sauransu.
Kuma a albarkacin inuwar Qur'ani zai samu natsuwa, Allah Ta'ala ya ce: “Ku saurara! Da ambaton Allah zukata suke samun natsuwa” Ra’ad: 28. Da samun sassauci da warakar kiraza da shiriya da albarka da dukkan alkairai wadanda Qur'ani ya siffanta kansa da su.
Idan wanda yake dauke da Qur'ani ya samu dukkan wadannan, to dakewarsa da tsayuwarsa da karfin zuciyarsa za su karu, zuciyarsa za ta gyaru ta hau saiti, himmarsa za ta dadu, hikimarsa za ta bayyana, to a lokacin zai zama mabubbuga ta kyauta da alkairai ga kansa da ga sauran al'ummu, kamar dai yadda yake wani sha’ani ne na masu kawo gyara masu girma wanda shugabansu shi ne Manzon Allah (s.a.w.a) da Amirul Muminina (as).
[1] Man-La Yahduruhul Faqih: 4/410.
[2] Al-Kafi: 2/609, babun fi kira’atihi (kira’atul Qur'an), hadisi na 1.